Daga Firmain Eric Mbadinga
Wasu hotunan na zama a zukata, suna sauya fahimtar mutum ga uniya ta hanyoyin da suke canja rayuwa.
Abu mai matukar muhimmanci a sana’ar Clarence Hascheley shi ne wasan kwaikwayon kungiyar da ke da zango tara, da ke nuna lauyoyi ‘yan gayu masu sanye da tufafi masu kyau, da ke da kwarjini kuma suna yin nasara kan shari’’in da suke kare wa a gaban kotuna.
Wannan tufafi ne ya kawo cikar burin Clarence.
“Tunanin na zama kamar sa a cikin tufafi ya zamar min abin da na ke matukar kauna,” ya fada wa TRT Afirka.
“Za ka iya ganin alamun hakan a ayyukan da na ke gudanarwa.”
Clarence kwararren mai sana’ar dinki ne da yake kokarin birgewa. Littafinsa na hotunan kaya na dauke da kayatattun wanduna da riguna – kuma abu ne da a Livrebille ake wuce wa ba tare da an lura da shi ba.
Kayansa masu sunan, ‘House of Clarence’ ya samar da nagarta tun bayan kaddamar da shi da riguna masu kyau shekaru biyu da suka gabata.
Kwastomomi na son tufafin da Clarence ke samarwa saboda yana yin abinda suka bukace shi – yana gwada mutane tare da ba su abinda suke so.
Yana amfani da yadika mafiya inganci, sannan kayansa na da sauki da ake iya saka su a kowanne yanayi.
“Manufar ita ce karfafa gwiwar mutane wajen saka sutura mai kwarjini,” in ji Clarence. “Mu ne tufafin gayu da ake iya saka wa a kowanne yanayi cikin rahusa.”
Shafin yanar gizon House of Clarence ya bayyana cewa “Dinka sutura don birgewa ne aikin da ke faranta masa rai
Talabijin a matsayin mai jan ra’ayi
Ba Clarence ne kadai mutumin da ya fara yin nasara da shuhura a sana’ar da ya gani a talabijin ko intanet ba.
A 2019, sashen nazarin halayyar dana dam na Jami’ar UCLouvain, jami’a mafi girma a Beljiyom da ke koyarwa da yaren Farasanci, ya buga wani bincike da ke nuna yadda jaruman talabijin ke yin tasiri mi kyau kan yara kanana, kamar yadda za su iya iya yi musu illa.
A cewar binciken, yawancin daliban sakandare na aji 5 da 6 sun fi son wani hali na musamman a cikin shirin talabijin, mafi girman yiwuwar su yi ƙoƙarin kama wannan mutumin har ma suna zaɓar sana'a iri ɗaya.
Bayan ya karanci harkar banki da hada-hadar kudi a Ghana, ya yanke shawarar jajircewa sosai wajen cika burinsa na kasuwancin kayan ado.
Iyalin Clarence da abokansa, waɗanda suka yi tunanin zai zama ma'aikacin banki, sun so su gamsar da shi cewa hakan ne ya fi dacewa da shi. Amma da ya dage kan burinsa sai suka goyi bayansa gaba daya.
A yau, House of Clarence yana da ƙwararrun ƙwararru waɗanda ke kula da abokan ciniki.
Ribar kasuwanci
Matakin da Clarence ya ɗauka na rungumar rashin tabbas da ke tattare da fara kasuwanci duk da shaidar karatun digiri da ya mallaka wanda zai iya sama mishi gurɓin aikin yi mai tsoka na daga cikin ƙalubalen rashin ayyukan yi da mafi yawan matasa suke fuskanta a ƙasarsa ta Gabon, inda ake yawan fama da rashin aiki yi.
A shekarar 2023, matsalar rashin aikin yi a tsakanin matasa ya zarce kusan da kashi 20 cikin 100 a Gabon.
Clarence dai ya yi imanin cewa sai matasa sun tashi tsaye kana sun ƙarfafa wa kansu gwiwa tare da yin dukkan abin da ya kamata su yi wajen cika burinsu. Yana mai farin ciki da godiya kan yadda abubuwa suka zo msihi cikin sauƙi.
''Ina ci gaba da yin aikina ne bisa ga sauraren ra'ayoyin jama'a, sannan ina iya koƙarina wajen riƙe abokan cinikayyata, ta hanyar gwada su da kuma kai musu kayan da na ɗinka musu kai tsaye zuwa gidajensu ko wuraren aiki don samar musu sauƙi,'' kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Mamidi na da burin faɗaɗa aikinsa zuwa ɗinkin kayan mata da yara.
''Na yi matukar mamaki kan yanda odar kaya suke yawan shigo wa, duk da farashi mai yawa da muke bayar wa kan dinƙi irin na 'yan Gabon.''
Inganci abu ne da matshin mai ɗinki ba zai taba yin wasa da shi ba. Yana shirin faɗaɗa kasuwancinsa ta hanyar ɗinka kaya mata da yara, yanayin da zai ba shi damar ɗaukar harin mutane aiki.
Clarence, wanda ke ƙaunar ɗan wasan ƙwallon ƙafa ta Gabon, Pierre- Emerick Aubameyang, ya shawarci matasa da su faɗaɗa tunaninsu.
''Kowane mutum a fagen nemansa zai iya kawo wani abu na musamman don ciyar da ƙasarmu gaba,'' in jishi. ''ku ɗauki ɗarasi a rayuwar Aubameyang da ni kaina!"