Laylatul Qadr: ‘Yan Nijeriya sun tattauna kan zakuwarsu ta son ganin dare mafi daraja na Ramadan

Laylatul Qadr: ‘Yan Nijeriya sun tattauna kan zakuwarsu ta son ganin dare mafi daraja na Ramadan

An shafe ranar Litinin da Talata ana tattauna batun Laylatul Qadri a shafukan sada zumunta na Nijeriya.
Masallatai a fadin duniya sun fara cikar kwari don gabatar da Sallar Tahajjid a goman karshe na Ramadan / Hoto: AA

Daga Ebubekir Yahya

Tun ranar Litinin da aka kammala azumi na 19 Musulmai a fadin duniya suka shirya shiga goman karshe na watan Ramadan da shirin riskar dare mafi daraja na Lailatul Qadr.

Jama’a a sassan duniya ciki har da Nijeriya, sun yi ta tofa albarkacin bakunansu da irin addu’oi’in da suke fatan Ubangiji ya amsa musu a wannan dare.

An shafe ranar Litinin da Talata ana tattauna batun Laylatul Qadri a shafukan sada zumunta na Nijeriya.

Maudu'in #Laylatul Qadr ya yi ta tashe har ta kai an yi amfani da shi sau fiye da 20,000 a Twitter, inda mutane suka dinga bayyana zumudi da zakuwarsu ta zuwan wannan dare mai albarka.

Can a Facebook ma an yi ta ambatar Laylatul Qadr sau fiye da 6,000 har ya zama cikin mafiya tashe a shafin.

Ranar Talata 4 ga Afrilu ce ta yi daidai da ranar 20 ga watan Ramadan, kuma ranar da daddare ne za a fara laluben daren da ake tsinkaya a dararen kwanakin mara na goman karshen.

Shafin da ke Kula da Masallatai Biyu Masu Daraja na Makkah da Madina Haramain Sharifain a Twitter ma ya wallafa sanarwar tunin daren.

Me mutane ke cewa game da Laylatul Qadr?

Yawanci mutane sun nuna zakwadin son riskar daren ne don su samu su tsaya a cikinsa su kuma roki Allah ya amsa musu addu'o'i da bukatunsu.

Malamai ma sun yi ta yi wa al'umma tuni a kan muhimmancin daren da yin kira da ka da a yi wasa da wannan dama ta ribatar Ramadan.

Ga dai yadda mutane suka dinga tattaunawa da tofa albarkacin bakunansu game da wannan dare mai albarka na Laylatul Qadri:

"Allah Ka sa mu riski Lailatil Qadri," in ji @sons_weeder.

May Allah count us among those who will witness the night of Laylatul Qadr and accept our supplication as an act of ibadah. RAMADAN DAY 20...2023

Posted by Idris Muhammed Amaga on Tuesday, April 11, 2023

Idris Muhammad Amaga ma ya ce "Allah Ya sa muna daga cikin wadanda za su riski daren Laylatul Qadr tare da amsar addu'o;inmu a matsayin ibada."

Allah ya sa mu dace da lailatul qadri. Amin.

Posted by Ibrahim Musa on Tuesday, April 11, 2023

Shi kuwa @Jwadzz cewa ya yi "A wannan karon a daren Laylatul Qadr, ina so na roki Allah Ya sanyaya min zuciyata. Ba na son soyayya. So nake kawai na kasance cikin farin ciki ba tare da wani abu da zai gurbata min nishadi ba."

Wasu Musulman kuma sun yi ta tunasar da jama'a kan irin addu'o'in da Musulunci ya koyar da ya kamata a dinga yi a wannan dare na Laylaul Qadri.

@hauwamg_ ta ce "Na ga bidiyon Omar Sulaiman (wani malamin Musulunci), ya ce ka da mu manta cewa daren yana farawa ne tun daga Magariba! Ku guji yin duk wani abu marar kyau ko wanda aka haramta. Ina ga tunatarwa ce mai muhimmanci. Allah Ya sa muna daga cikin wadanda za su riski daren laylatul Qadt, Ameen."

Yaushe ake riskar Daren Laylatul Qadr?

Babu wanda ya san yaushe ne takamaiman daren Laylatul Qadr, amma an bayyana cewar ana riskar daren a dararen mara na goman karshe na watan Ramadan. (Misali daren 21 ko 23 ko 25 ko 27 ko kumaa 29).

Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya bayyana cewa "Ku neme shi a goman karshe, a dararen mara," (Hadisin Bukhari da Muslim).

Sai dai malamai sun ce kasamncewar daren na fadawa a dararern mara, hakan ba ya nufin a ki yin ibada a cikin sauraren dararen goman karshen.

Abun da ake so Musulmi ya shagalta da shi a tsawon watan Ramadan shi ne Ibadu don neman kusanci da dacewa a nan duniya da gobe kiyama.

The Prophet (ﷺ) said, "Search for the Night of Qadr in the odd nights of the last ten days of Ramadan." [Bukhari]

Posted by Haramain Sharifain on Tuesday, April 11, 2023

Ta yaya ake bambance daren Laylatul Qadri daga sauran darere?

Wasu malaman na ganin babu wasu alamomi na musamman da ake gani, kawai abun da ake so shi ne a yi ibada a ko wane dare na goman karshe don neman dacewa.

Yayin da wasu malaman kuma sukan ce daren na da alamomi kamar daren a kan yin ruwan sama, sannan washe-garin daren rana na fitowa amma ba ta da zafi.

Me aka hori Musulmai su yi a wannan dare?

Kamar yadda ake son raya dukkan dararen Ramadan musamman ma dararen goman karshe da Lailatul Qadr ke fadawa a cikin su, ana bukatar Musulmai da su shagaltu da Ibadu; kamar nafilfili da karatun Alkur'ani Mai Tsarki da zikiri da addu'o'i da sadaka da sada zumunci da sauran ayyukan lada.

An ruwaito wani Hadisi da Nana Aisha, daya daga cikin matan Annabi Muhammad SAW ta tambaye shi cewa “Ya Ma’aikin Allah idan mun dace da daren Laylatul Qadr wacce addu’a ya kamata mu yi?

Sai ya ba ta amsa da cewa ta ce “Allahumma Innaka Afuwwun Tuhibbul Afwa Fa’afu Anna”.

Falalar daren Laylatul Qadr

A wannan dare na Laylatul Qadri aka saukar da Alkur'ani Mai Tsarki.

Ibada a wannan dare na Laylatul Qadr daidai take da ibadar shekara 83.

Daren Laylatul Qadri dare ne da ya fi darare dubu alheri da falala.

Ramadan wata ne da ake gafarta dukkan zunubai don haka malamai ke jaddada muhimmanci yin ibada ka'in da na'in don neman dacewa.

Dare ne da Mala'iku suke sauko wa duniya, ciki har da Mala'ika Jibrilu Alaihissalam.

Daren Laylatul Qadri na da Salama da Albarka.

A wannan dare ne Allah Madaukakin Saki yake kasafin komai.

TRT Afrika