Mai zanen yana fitar da zane ya fita fes tamkar hoto da aka dauka da na'ura babba. Hoto: Hopex John       

Daga

Pauline Odhiambo

Kowane mai fasaha yana da wata baiwar da ta bambanta da shi sauran masu fasaha.

Wannan baiwar, wadda ke bambanta aikinsa da na abokan sana'arsa ce take kara fito da shi a idon duniya.

Wasu masu fasahar sukan yi amfani da salo daban-daban a rayuwarsa. Amma shi John Adenuga Opeyemi, yana hada salon daban-daban ne a lokaci guda domin kara fito da baiwarsa.

Yana kere sa'anni ne ta yadda yake iya fitar da zane fes tamkar hoto da aka dauka da kyamara babba.

Zane-zane masu ban sha'awa

Opeyemi, wanda yake gudanar da ayyukansa kamfaninsa mai suna 'Hopex John," ya bayyana cewa burinsa na nuna al'adun Afirka ne ya karfafa masa gwiwar kokarin kawo sauyi a tsarin na zane.

"Duk wani abu da ya shafi zane-zane da na yi, tun daga wadanda na zana, ko abin da nake zanawa da tsarin tufafinsu duk suna nuni ne da tsari da al'adun Afirka," inji John a tattaunawarsa da TRT Afrika, sannan ya kara da cewa, "Wannan shi ne tsarina, kuma da shi aka san ni."

Wasu zane-zanen John ba a kammala su ba, wanda hakan ke kara jan hankalin mai kallo a kan bukatar karasa bangaren da ya rage din.

Hopex 2: Hopex John

"Idan mutum yana fafutikar samun karbuwa, ba dole ba ne a fahimci baiwarsa. Wannan ya sa nake rage wasu gurabai a zane-zanen, inda guraban da na bari suke nuna akwai abubuwan da za a iya ganowa nan gaba, sannan wuraren da na rufe da zanen suke bayyana yanzu," in ji shi.

"Wani bangare da nake bari a dudashe kuwa yana nufin abin da ya gabata gare ni da sauran 'yan Afirka da suke fafutikar samun nasara a rayuwarsu."

Abin da ya taso yana sha'awa

John tun yana karami yake sha'awar zane-zane. A makarantar sakandare, shi yake taimakon abokan karatunsa da suke bangaren kimiyya wajen zane-zane, inda saboda kwarewarsa har malamansu ma sukan kira shi ya yi zane a jikin allo idan suna karantarwa.

"Nakan kalla wasu faye-fayen bidiyo a YouTube domin kara kwarewa," in ji John.

Domin sha'awar da yake yi wa harkar ce ta sa John ya karanci bangaren fasahar zane-zane wato Fine Arts a Jami'ar Benin, inda ya fara gwaji da kaloli daban-daban har ya fara amfani da salon da yake yi yanzu.

Launi mai haske yana taimakawa wajen kara fito da zanen ya yi fes. Hoto: Hopex John

Kafin ya fara zane, John yakan fara ne da rubuta abubuwan da yake son sakawa a cikin zanen a kwamfutar hannunsa. Daga nan sai ya fara tunanin wane fitaccen mutum zai sa a cikin zanen tare kuma da tunanin kalar da zai amfani da ita.

Fasaha babban

Ya yi wa fitattun mutane da dama zane, amma yawancin wadanda suke tallata shi abokansa me da makwabta da ma wasu bakin wadanda suke amincewa su shiga wajen aikinsa da ke Birnin Benin ya dauke su hoto.

Daga cikin hotunan ne yake zabar wadanda suka fi kyau, ya fara fitar da tasiwirarsu, sannan ya bi tasiwirar da kala. Daga cikin ayyukansa na baya-bayan nan akwai kundi mai suna "Love, Peace and Deceit," wanda a ciki akwai fitattun mutane da dama da ya zana.

"Ina so sakonnin da nake aikawa da zane-zanen da nake yi su yi tasiri sosai. Ina so bayan na kammala zane, da an gani a gane sakon da nake aikawa," in ji matashin mai shekara 31, inda ya kara da cewa, "wannan kundin da na yi, makasudinsa shi ne in isar da sakon kauna da zaman lafiya da rayuwa mai kyau da mutanen Afirka da dama suke fata."

A zane-zanen John da dama akwai wasu wurare da yake bari domin wata manufar. Hoto: Hopex John

Kowane aiki a cikin kundin sai da ya yi kusan mako uku kafin ya kammala.

Kyauta mai muhimmanci

John ya yi kiyasin cewa ya yi zane akalla guda 700 tun daga shekarar 2017 da ya fara sana'ar.

Yakan fara ne da gwaji ta hanyar zana kansa- tsarin da yawancin masu zane ba su cika so ba. Mutum ya duba tare da auna aikinsa yana yi wa masu zane da dama wahala.

Amma shi John yana yawan zana kansa. Kokarin zana kansa da yake yi, wanda tun shekarun baya ya fara, ya zama masa jiki yanzum

"Na fara zana kaina ne tun a shekarun baya, inda duk shekara nake zanen domin murnar zagayowar ranar haihuwata. Ina jin dadin zana kaina domin kowane tabo da zane da yake jikina yana da tarihi tare da nuna wani sashe a rayuwata. A tsawon lokacin da suka gabata, wannan shi ne kyauta mai muhimmanci da nake yi wa kaina."

John yana gwaji ta hanyar zana kansa. Hoto: Hopex John

Kyawun Afirka

An baje-kolin ayyukan John a wuraren nuna hotuna a Nijeriya da Faransa da Amurka.

Sai dai ya sha fama da kalubale kafin ya Kai ga samu wannan nasarar.

"Abin takaicin shi ne yadda ba a cika damuwa da ayyukan fasaha ba a Afirka. Haka kuma akwai ban haushi yadda ake biyan 'yan kudade kadan a kan ayyukan fasaha da ake daukar lokaci mai tsawo kafin a kammala," in ji shi.

Amma duk da haka, John yana da yakinin yadda ake nuna ayyukan fasahar mutanen Afirka a duniya zai taimaka wajen karfafa gwiwarsu.

"Burina in nuna ayyukana a duniya domin su san cewa al'adun Afirka suna da kyau da kayatarwa."

An baje-kolin ayyukan John a wuraren nuna hotuna a Amurka da Faransa. Hoto: Hopex John

TRT Afrika