Hagia Sophia: Shahararren wurin ibadar Musulmi da Kirista a Turkiye

Daya daga cikin muhimman wuraren tarihi a Turkiya shi ne Hagia Sophia, wani gini da ya kasance majami’a kana masallaci – wato wuri ne na ibadar Musulmi da ta Kirista a tsawon tarihi.

A halin yanzu masallacin Juma’a ne, kuma wurin tarihi mai matukar muhimmanci ga Kirista da kuma masu yawon bude ido.

Yana cikin wuraren tarihi da al’adu da ke samun kariya a karkashin dokoki na Majalisar Dinkin Duniya.

A shekarar 1985 Hukumar Bunkasa Ilimi, Kimiyya da Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniyar (UNESCO) ta saka Hagia Sophia a jerin wuraren tarihi na addini da al’adu na duniya.

Wannan mataki ya sake daukaka martabar Hagia Sophia a duniya.

Hagia Sophia na daya daga cikin masallatan Juma’a mafi girma a Turkiya.

Duk da an mayar da Hagia Sophia Masallacin Juma’a, ba a hana masu yawon bude shiga su kashe kwarkwatar idanuwansu tare da daukar hotuna don nishadi da ilmantarwa ba.

Abubuwan ban sha’awa da ke masallacin Hagia Sophia.

Waje na farko na Hagia Sophia da ke fara jan hankali shi ne harabar Masallacin Juma’ar. Daga bangaren yamma Masallacin na da kofofo da suke da turaku masu ado da kayatarwa. Sannan daga tsakiya kuma ga wajen alwala da aka bawa sunan ‘Phiale’ wanda ke kara kawata harabar. Ana shiga harabar ta kofofi tara wadanda sai a tsaffin Majami’un Kisitoci ake samun irin su. Bayan an shiga daga ciki ana cin karo da irin wannan kofa da ake kira Narthex a harshen Turanci. Ita wannan kofa da ke bangaren kudu ana kiran ta da sunan Horologian. A karni na 9 Theophilos ya kafa siffar kuros da fika-fikan kofar azurfa.

Masallacin Juma'a na Hagia Sophia/ AA

Ana shiga wajen Ibada na daban ta kowacce kofar Narthex. Daga cikin kofofin akwai guda uku na tsakiya da ke da sunan kofofin Sarakuna. Sarki ne kadai ke bi ta wadannan kofofi guda uku. Wadannan kofofi guda uku sun fi sauran tsayi, ado da kayatarwa. Ana tunanin a zamanin Sarkin Daular Byzantine Iustinianos aka gina wadannan kofofi da suke da ado na azurfa.

A kowacce rana dubban masu yawon bude ido daga sassa daban-daban na duniya na ziyartar Hagia Sophia yayin da a shekara guda akan samu masu ziyara daga 3000000 zuwa 3,500 000. Sun kuma hada da Musulmi da wadanda ba Musulmi ba.

A lokacin da ginin ke matsayin gidan adana kayan tarihi ana biyan kudin shiga, amma tun daga shekarar 2020, lokacin da ake sake mayar da wurin ya zama masallaci, kyauta ake shiga.

Hagia Sophia/ AA

Hagia Sophia dai wuri ne da ke tsakiyar birnin Santanbul, kuma daga wajen, mutum zai iya ganin wasu muhimman gine-ginen na tarihi, don haka mai ziyara zai iya jifar tsuntsu biyu da dutse daya. Cibiya ce mai matukar muhimmanci ga musulmi da kirista kuma na daya daga cikin wuraren da ke tabbatar da hadin kan mabiya addinan biyu.

Ya kasance coci na tsawon kimanin shekara dubu, kuma ya kasance masallaci na kimanin shekara 500, daga bisani ya zama gidan adana kayan tarihi na tsawon kimanin shekara 70 har zuwa shekarar 2020 lokacin da ya sake komawa matsayin babban masallaci.

Hagia Sophia a matsayin wurin ibadar Kirista

Hagia Sophia wuri ne mai dimbin tarihi na shekaru fiye da 1600. Sunan ya samo asali ne daga Girkanci wanda ke nufin ‘’Hikimar Ubangiji’’ ko ‘’Hikima Mai Tsaki.’’ An fara gina wurin a zamanin mulkin sarkin Daular Romawa, Constantine I, a lokacin da daular ta amince da Kiristanci a matsayin addininta a hukumance.

A shekarar 360 Miladiyya a zamanin Sarki Constantin na II, aka bude Hagia Sophia da aka yi wa rufin katako a kan daya daga tuddan Santanbul bakwai, kuma a wannan zamani ana kiran ta da sunan ‘Babban Coci’.

To amma tun kafin Kirista su karbe iko da wurin, Hagia Sophia ya kasance wurin bauta ta masu addinin gargajiya.

An yi ta yi wa ginin kwaskwarima da sauye-sauye. Sau biyu ma aka sake ginin kusan baki dayansa.

Hagia Sophia/ AA

Sarkin Daular Romawa Theodosius na II ne ya sake gina Hagia Sophia a kan ta farko, lokacin da aka yi mata kokuwa da kusurwowin ado, kuma aka fara ibadar kirista a wajen a shekarar 415 Miladiyya.

A shekarar 532 kuma, lokacin ‘tawayen Nika’ wato wani mummunan bore na kin jinin shuwagabanni, a zamanin Sarki Justinyen, sai aka rusa wannan gini.

Bayan lafawar boren, sai Sarki Justinyen ya dauki matakin sake gina wannan wuri na Hagia Sophia, aka kasaita shi, ya fi dukkan biyu na baya da aka rushe.

Ginin Hagia Sophia da aka fara amfani da shi a matsayin Majami’ar Daular Byzantine, ya dinga samun matsala a tsawon tarihin sakamakon bore, tawaye, yake-yake - galibi tsakanin mabiya addinai ko dariku, ko dauloli daban-daban. To amma, har zuwa shekarar 1261, Hagia Sophia ya kasance wajen bauta da ke karkashin Majami’ar Darikar Katolika ta Romawa.

Matsayin Hagia Sophia a daular Usmaniyya ta Musulunci

Lokacin da Daular Usmaniyya ta Musulunci ta ci galaba kan daular Romawa, sannan suka kwace iko da Santanbul, a 1453, sai aka mayar da cibiyar ta Hagia Sophia ta kasance babban masallacin Juma’a.

A lokacin, Sarkin Daular Usmaniyya Sultan Mehmet Han da al’umar Musulmi sun dauki Masallacin Juma’a na Hagia Sophia a matsayin babbar alamar nasara ta kwace Santanbul.

Sallar Juma'a a Hagia Sophia/ AA

Tun daga Sarki Mehmet Han, Musulmi suka dinga gyara shi da kula da shi, kuma ya zama mafi kyau da kwari sama da yadda ya ke a baya. Daya daga cikin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen dorewar ginin Hagia Sophia, shi ne shahararren magini, Mimar Sinan, wanda ya yi kare-kare a ginin abin da ya taimaka sosai wajen tabbatuwar ginin a tsaye a yanzu haka.

Shi dai Mimar Sinan, ya yi aiki ne a zamanin Sarki Sultan Salim Han na II, wanda ya kasance daya daga

A tsawon lokacin da Sarakunan Daular Usmaniyya suka shimfida Mulki, an samar da hasumiyoyi, da karin kubbobi da babbar haraba da minbari da mabubbugan ruwa da makrantar Islamiyya da kuma dakin karatu a Hagia Sophia.

Matakin da gwamnatin Erdogan ta dauka a baya-bayan nan.

A zamanin Daular Usmaniyya an bayar da muhimmanci ga ado a cikin masallacin. Hagia Sophia ya kasance a matsayin Masallacin Juma’a tsawon shekaru 481 kafin a watan Nuwamban 1934 Majalisar Ministocin Turkiya ta dauki matakin mayar da masallacin zuwa gidan adana kayan tarihi. Bayan shekaru 86 a matsayin gidan adana kayan tarihi, a ranar 10 ga Yulin 2020, Kotun Kolin Turkiya ta soke hukuncin da ya mayar da Hagia Sophia gidan adana kayan tarihi, inda ta sake mayar da wurin ya kasance masallacin Juma’a. Bayan wannan mataki da Kotun ta dauka, sai shugaban kasar Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya sanya hannu kan doka mai lamba 2729 wadda ta bayar da dama aka fara gudanar da ibada a masallacin. Matakin ya janyo ka-ce-na-ce inda mabiya addinin kirista suka nuna rashin gamsuwarsu. A halin yanzu, ana ci gaba da amfani da cibiyar a matsayin masallaci kuma wurin tarihi da yawon bude ido wanda Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana. Ba a hana mabiya addinin kirista da sauran wadanda ba musulmi ba shiga wurin.

Hagia Sophia bayan faduwar rana/ AA