Genge salon waƙa ce ta Afirka da ta samo asali daga Kenya, sai kuma kiɗan Bongo wanda salo ne na hip hop din Amurka cakuɗe da na Tanzaniya.

Daga Charles Mgbolu

Gabashin Afirka ya sake yunƙurowa a fagen waƙe-waƙe a shekarar 2023, inda babban kamfanin Spotify ya yaba wa mawaƙa massu fasaha na Gabashin Afirka a cikin rahotonsa na ban kwana da 2023 ‘2023 Wrapped Report’, saboda irin yadda suka sake fitowa idon duniya tare da jan hankalin masu sauraro na gida da na waje da irin waƙe-waƙensu masu ban mamaki da kuma irin haɗin gwiwar da suke yi.

Masana'antar waƙe-waƙe ta Gabashin Afirka ta shahara da salon kaɗe-ƙaɗen zamani, wanda asalinsa na kasashen yamma ne, musamman hip hop da funk.

Akwai kuma tasiri mai ƙarfi na waƙoƙin gargajiya na Afirka, wato kiɗan Boomba, wanda kuma ake kira Kapuka a Kenya.

Genge salon waƙa ce ta Afirka da ta samo asali daga Kenya, sai kuma kiɗan Bongo wanda salo ne na hip hop din Amurka cakuɗe da na Tanzaniya.

Bayanai daga shafukan waƙe-waƙe da kiɗe-kaɗe a cikin takaitaccen bayani da suka fitar na 2023 sun ba da lambar yabo ta shahara ga Afrobeats daga Yammacin Afirka, amma mawaƙan Gabashin Afirka su ma sun yi fice a cikin manyan sigogi daban-daban.

Diamond Platnumz

Naseeb Abdul Juma, wanda aka fi sani da suna Diamond Platenumz, wanda ke ɗaya daga cikin manyan mawaƙa a Tanzaniya, waƙoƙinsa sun samu adadin sauraro miliyan 65 a kan dandalin Spotify a 2023.

Waƙoƙin Diamond Platnumz sun samu adadin sauraro miliyan 65 a kan dandalin Spotify a 2023. Photo: Diamond Platnumz

Wannan ya ninka adadin da ya samu a shekarar 2022 (miliyan 30), tare da masu saurare miliyan 1.4 duk wata.

Waƙarsa ta Jugni kawai, an saurare ta fiye da sau miliyan 13, inda suk wata mutum 1.3 ke saurarnta. Mafi ƙarfi ya zuwa yanzu shi ne haɗin gwiwarsa a kan 'Yope Remix', wanda ya yi tare da mawaƙin Kongo Innoss'B, inda aka kalle tra sau sama da miliyan 220 a kan Youtube.

Souti Sol

Tawagar mawakan Kenya ta Sauti Sol sun ɗaga hankalin mutane a watan Mayun 2023 lokacin da suka ba da sanarwar cewa za su daina taka rawa a fagen waƙar Kenya bayan sun shafe shekaru 18 tare.

Sun ci gaba da cewa za su gudanar da rangadin bankwana da kade-kade a nahiyar da ma wasu kasashen yammacin duniya.

Sauti Sol suna da masu sauraron waƙoƙinsu sama da 400,000 a kowane wata. Photo: Souti Sol

Labarin ya ƙara ta'azzara shahararsu, inda waƙoƙinsu suka ɗare sama a mafi yawan manhajojin da ake saka waƙoƙi.

Spotify, a cikin rahoton nasa, ya ce kungiyar tana da masu saurare sama da 400,000 a kowane wata, kuma bakandamiyarsu Lil Mama, wacce aka saki a watan Nuwamba 2022, an saurare ta fiye da sau miliyan uku tun bayan sanarwar dakatarwar da suka yi, a cewar Spotify.

Waƙar wata 'yar tawagar Sauti Sol, Bien Aime-Baraza ta 'My baby' da ta yi da 'yar Nijeriyar nan Ayra Starr, ita ma tana samun masu sauraro da yawa, inda a 2023 aka saurare ta sau sama da miliyan bakwai a Spotify.

Harmonize

Rajab Abdul Kahali, wanda kuma aka fi sani da Harmonize, ɗan Tanzaniya ne mai rikodin din salon waka na Bongo Flava kuma ɗan kasuwa.

Fiye da mutum 760,000 ne ke sauraron wakokin mawakin mai shekara 33 duk wata a Spotify. Photo: Harmonize

Waƙarsa, mai suna 'Single Again', wanda aka saki a watan Agusta 2023, ta yi nasara inda aka saurare ta sau sama da miliyan takwas a kan Spotify. An kalli wakar da ya yi ta hadin gwiwa da mawakin Nijeriya Ruger, sau sama da miliyan hudu a Youtube.

Fiye da mutum 760,000 ne ke sauraron wakokin mawakin mai shekara 33 duk wata a Spotify, inda waƙarsa ta haɗin gwiwar tare da Blag Jerzee (Falling for You) wadda aka saki a cikin 2021 har yanzutake jan zarenta a 2023, inda aka saurare ta sama da sau miliyan 34.

Rayvanny

Raymond Mwakyusa, wanda magoya baya suka sani da Rayvanny, mawaƙi ne ɗan ƙasar Tanzaniya mai shekaru 30 aka saurari wakokinsa sau fiye da miliyan 100 a manhajar Boomplay, kuma ana sauraronta sau fiye da 500,000duk wata a Spotify.

Akwai wata waƙarsa 'Melody' da ya fito tare da mawaƙin Tanzania Jay, da ita kaɗai kawai an kalle ta sau fiye da miliyan 10.1 a Tiktok. Photo: Rayvanny

Akwai wata waƙarsa 'Melody' da ya fito tare da mawaƙin Tanzania Jay, da ita kaɗai kawai an kalle ta sau fiye da miliyan 10.1 a Tiktok.

Rayvanny ya fara fito fili da wakarsa ta farko mai suna "Kwetu" a shekarar 2019. Wakarsa ta "Tetema" da ya fito da Diamond Platnumz a ƙara daukaka shi a fagen wakokin gabashin Afirka.

Xenia Manasseh

Xenia Manasseh wata mawaƙiyar R&B ce ta Kenya mai samun daukaka da sauri, wacce ta shiga cikin jerinmu inda ta zama mawaƙiyar yarinya mai kwajini.

An san Manassa da sanya kida mai yawa a cikin waƙoƙinta. Photo: Xenia Manasseh

Xenia mai shekara 26 a kan saurari waƙoƙinta sau sama da 300,000 duk wata, kuma waƙarta ɗaya mai taken ‘When It’s Over’ wadda aka saki a cikin 2019 an saurare ta sama da sau miliyan ɗaya, bisa ga bayanan Spotify na 2023.

Haɗin gwiwarta da furodusa na Kenya Ukweli a cikin waƙar ‘Love or leave me’ ya sa an saurare ta sama da sau miliyan 1.2 a Spotify.

TRT Afrika