Daga Jean-Rovys Dabany
Tsawon shekaru, dan kasar Gabon da ke rayuwa a babban birnin Libreville, Desirey Minkoh ya tafi zuwa yankuna da dama na Gabon da manufar dauko hotunan wurare masu kyau da kayatarwa na Gabon ta hanyar amfani da na'urar daukar hotonsa, wanda yake yada hotunan a shafukan yanar gizo da ma na sada zumunta.
"Ta hanyar rahotannina, Ina bayar d ahaske kan kyawun da Gabon ke da shi. Muna da fadin kasa mai albarka. A yayin da nake tafiya a dazuka, na gano cewa muna da muhallin da ake bukatar a adana shi tare da nuna wa duniya shi," in ji Desirey Minkoh, yayin tattaunawa da TRT Afirka.
A ra'ayin mai daukar hoton, kasar ba ta amfani da cikakkiyar damar da take da ita ta samun masu yawon bude ido.
Desirey ya bayyana cewa kafafan yada labarai na ta kokawa a fagen siyasa da sauran labarai marasa dadi tsawon shekaru.
Yana fata ayyukansa za su bude idanuwan 'yan kasar Gabon, su taimaka musu wajen barin rayuwar birane, su je su amfana da kyawun asali na yanayin kasar.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "madalla da hotunan da na dauka, masu sana'ar shirya yawon bude ido na gano wuraren da a baya ba su san da su ba, ba su san za su iya ziyartarsu ba."
Mai daukar hoton ya bayyana cewa ya gaji da irin hotuna d abidiyon da ak nuna wa na "Afirka mai fama da yunwa, mai yawan yara masu kwashako, nahiyar da yunwa ta yayyaga da ke fama da yake-yake".
Desirey ya ce "Manufar ita ce a nuna Afirka ta wata sabuwar hanya da sabon salo. Ana so a fadi cewa ba wa' ta'annatin kudade ko yara da ke fama da yunwa kawai muke da su a Afirka ba, akwai abubuwan nunawa da za a iya takama da su a duniya".
Amma dajin da ke wannan kasa t Tsakiyar Afirka, kamar a sauran yankunan duniya, na fuskantar barazanar masu shigar sa suna sare bishiyu.
Mutanen da ke rayuwa a kewayen dazukan na sare bishiyu don biyan bukatarsu ta makamashi, ko yin gini. Ana mafnai da wasu bishiyun don magunguna.
A ra'ayin masanin tsirrai Ghislain Moussavou, dazukan Gabon na cikin matsin lamba.
Kamar yadda yake ga sauran dazuka a duniya, mu ma muna rasa dazuka da dama. Dazukanmu na cikin hatsari da fuskantar barazana da za su iya kai su ga lalacewa.
Wannan asara da suke yi na zuwa ne sakamakon ayyukan masu sarar bishiyu, hakar ma'adanai, neman albarkatun mai da sauran ayyuka da suka hada da na noma," in ji masanin muhalli.
Wani bincike da aka gudanar da ke bayyana barazanar da Gabon ke fuskanta da aka buga a Mongabay, wata kungiyar kare muhalli ta kasa da kasa, an bayyana Gabon na asarar sama da hekta 10,000 kowacce shekara a dazukanta sakamakon kutse.
Domin magance sare dazuka da kuma ba su kariya, mahukunta na ta kokarin wayar da kan jama'a kan muhimmancin kula da bishiyun kasar.
"Sibang Arboretum" wani yanki da aka kebe a Libreville, babban birnin Gabon, na zama abin misali ga jama'a don su fahimci bishiyu da yadda ake rayuwa da su ba tare da cutar da su ba.
Wajen da ke da girma da fadin hekta 16, Sibang Arboretum gida ne na bishiyu da dama da a yanzu ake gudanar da nazari a kan su.
Duk da kokarin da ake yi na bayar da kariya ga Sibang, masu kutse ba bisa ka'ida ba na shiga su yi ta'annatinsu.
Masu sare bishiyu na cewa suna yin hakan ne ala tilas.
"Wadannan itatuwan da na saro ana amfani da su wajen maganin hakori.A yanzu 'yar uwata na fama da ciwon hakori mai tsanani," in ji Charlie Abessolo, mazaunin Sibang yayin tattaunawa da TRT Afirka.
Tun bayan samun 'yancin kan Gabon, Cibiyoyin Binciken Ayyukan Noma da Gandun Daji da Samar da Magundunan Zamani da na Gargajiya ke kula da Arboretum, wadanda dukkan su hukumomi ne da ke karkashun kulawar Ma'a'katar Binciken Kimiyya.
Henri Bourobou, Daraktan Cibiyar Hada Magungunan Zamani da na Gargajiya ya ce ba tare da samar da madadin itatuwa ba, to zai yi wahala a iya kawo karshen sare bishiyu a Sibang.
Ya shaida wa TRT Afirka cewa "Sibang na kewaye da kauyukan da ke takura usu. Wadannan jama'a na zuwa diban itatuwa, suna zuwa diban sassake."
Masu bincike na cewa kaso 20 na tsirran da ake da su a Gabon babu su a sauran sassan duniya.
Mai daukar hoton sa ran ayyukansa za su taimaka wajen kubutar da dazukan Gabon.
"Abun da kawai muke da shi na nunawa yaranmu da jikokinmu shi ne arzikin da Allah ya baiwa kasarmu. Ya rage na dukkan mu mu kare dazukanmu. Ba aiki ne da za ka yi yau ka daina yi gobe ba, dole ne a dukkan zamani a dinga yin wannan aiki," in ji Desirey Minkoh.
Mai daukar hoton ya lashe kambi da dama saboda ayyukansa. Kambi na baya-bayan nan da ya lashe shi ne a watan Nuwamban 2023, a lokacin da ya samu kambin daukar hoto na gasar daukar hotuna karo na 42 da 'Photo magazine' ke shirya wa duk shekara.