Daga Firmaın Eric Mbadinga
Cyril Biyoghe mai shekara 26 dan kasar Gabon, ya bayyana cewa yana samun gamsuwa mara misaltuwa daga aikin sassakar dutse da aka fi sani da Mbigou.
Ba shakka yana samun kudaden shiga daga aikin sassakar da yake yi, amma irin karfin gwiwa da ya ke samu daga abokan cinikinsa yana kara masa kaunar aikinsa.
A gundumar Alibandeng da ke babban birnin Gabon Libreville, Cyril ya yi fice sosai. Matashin wanda tsayinsa ya kai inci 5'6, kuma a koyaushe yana cike da murmushi a fuskarsa, yana da saukin kai kuma ana iya saurin gano shi cikin taro.
A aikinsa, ya siffata dutsen Mbigou zuwa kusan komai - kama daga sassaken jikin mutum da na dabbobi da sauran abubuwa marasa rai da dai sauransu.
Karfin gwiwa daga kuruciya
Cyril mamba ne na masu aikin sassakar fasaha na dutsen Mbigou, wata babbar kungiya a Libreville.
"Mahaifiyata ta yi aiki a wani shago da ke kusa da wurin aikin masu sassakar dutsen Mbigou. A lokacin kuruciyata, ina sha'awar ganin yadda masu aikin sassaka ke canza duwatsu zuwa kyawawan ayyukan fasaha," kamar yadda Cyril ya shaida wa TRT Afrika.
Rashin tilasta masa barin makaranta a lokacin da yake tasowa, bayan haka ne, ya yanke shawarar bin shiga aikin fasahar dutse.
Dutsen Mbigou shi ne babban kayan aikin da Cyril ke mayar da hankali akai wajen hada ayyukansa na fasaha. Ana samun dutsen a cikin launikan fari da ruwan toka da kore-kore da kuma ruwan kasa.
'Aikin fasaha da ke burge abokin ciniki'
A shekarun baya-baya nan, mutane kan yi tafiya mai nisa zuwa Alibandeng don siyan dutsen Mbigou, wanda ake iya kayyade darajarsa bisa ga nauyinsa.
Sauran abubuwan da ke kayyade farashin dutse sun hada da yanayin lokaci. A lokutan damina akan yi aiki mai yawa kafin a ciro dutsen.
Cyril ya ce a yayin aikin sassaƙar, babban burinsa da ke gabansa shi ne ya mayar da dutsen zuwa wani fasaha da za ta birge abokan cinikinsa.
Daya daga cikin manyan ayyukan da ya yi, shi ne na wani mutum da ke zaune a jan benci, yayin da yake wasa da kayan kidansa na katako.
Alkinta al'adun Gabon
''Aikin fasahar tsohon mutumin da aka kewaye da kawuna guda tara ya wakilci lardunan Gabon, ta hanyar buga kayan kidan na gargajiya, yana tunatar da matasan Gabon al'adunsu, da kuma dalilin da ya sa yake da muhimmanci a alkinta su," in ji Cyril.
A wani aikin da ya yi, Cyril ya sassaka hoton wani mutum da yake hanyar komawa gida da jaka a bayansa.
Cyril ya bayyana cewa mafi yawancin abokan cinikinsa masu zuwa yawon bude ido ne, daga ciki da kuma waje kasar.
Bulla cutar COVID-19, wacce ta dakatar da ayyukan jiragen sama da dama, ya yi sanadin haifar wa Cyril koma baya a kasuwancinsa, kamar yadda ya shaida wa TRTAfirka.
Ya ce, idan ya yi sa'a ya kan samu tsakanin dala 100 zuwa 200 a aikin fasaha guda daya da yi.