Mutumin mai shekara 40 bai taɓa tunanin zai zama mai dafa abinci ba.

Za a iya taƙaita labarin Régis Boulingi a matsayin wani haɗin yanayi mai daɗi.

Yanzu a matsayinsa na shugaban gidajen cin abinci guda uku da kuma kamfanin sarrafa abinci, mutumin mai shekara 40 bai taɓa tunanin zai zama mai dafa abinci, kuma mamallakin wani kasuwanci mai riba ba, bayan da a farkon lamarin ya kasance mai wahala.

"Na zama mai dafa abinci ne a bisa tsautsayi, na fada harkar dafa abinci don na bayyana abin da ke raina, in ji Régis Boulingi.

"A lokacin da nake ɗan shekara 14, na yi wani kuskure da ya bai wa mahaifina haushi sosai... (Boulingi ya fashe da dariya don tuna hakan) har sai da ya hukunta ni ta hanyar tura ni wurin wani aikin mai da ke gabar Tekun Port-Gentil, don na dinga musu wanke-wanke a wajen," Boulingi ya shaida wa TRT Afrika.

Amma abin da ya kamata ya zama hukunci gare ni, sai ya zame min mafarin koyon sana'ar dafa abinci na tsawon shekaru a wani kamfani mai zaman kansa na Faransa.

Boulingi shi ne ma'aikaci mafi ƙarancin shekaru a gidan abincin da ke cikin tashar jiragen ruwan wanda ke sayar wa ɗaruruwan ƴan ƙasashe daban-daban abinci. 

Abin da mutum ke so

Ko da yake ya zama ƙwararren mai dafa abinci ne a bisa ƙaddara, Boulingi ya yi imanin cewa ya gaji sha'awar dafa abinci daga iyayensa, musamman mahaifinsa wanda ya ce yana aiki a gidajen abinci.

"Tun ina ƙarami na gane ina yawan sha’awar ma’aikatan mahaifina da sukan zo gidanmu su shirya abinci, duk da ban san cewa wata rana zan yi koyi da su ba.

"Na kasance ina ganinsu suna yin hadaddun abinci da ket na murnar zagayowar ranar haihuwa da kuma na aure.

"A lokacin da na tsinci kaina a harkar dafa abinci, sai abin ya zame mini cikakkiyar damar yin abin da nake sha'awa, maimakon na kalle shi a amtsayin hukunci," in ji shi.

Boulingi shi ne ma'aikaci mafi ƙarancin shekaru a gidan abincin da ke cikin tashar jiragen ruwan wanda ke sayar wa ɗaruruwan ƴan ƙasashe daban-daban abinci.

"Sun kasance suna kirana ɗan yaro. Daga mai wanke-wanke sai na koma aiki a ɗakin sanyi inda ake ajiye kayan abincin da ba a so su lalace, bayan shekara biyu zuwa uku kuma na zama cikakken mai dafa abinci.

"Ni ne mai kula da shirya abinci na Afirka. Sannan bayan shekara biyu sai na zama babban mai dafa abinci," ya bayyana.

Chef Boulingu ya ƙare wajen dafa nau;ukan abinci da dama.

Daga nan sai Chef Boulingi kamar yadda aka san shi, ya ci gaba da samun horo a fannin gashin abincin da ya shafi fulawa da burodi da kek.

Bayan ya shafe tsawon shekaru yana dafa abinci a otel, musamman a babban birnin kasar Gabon, Libreville, sai ya ƙaddamar da gidan abincinsa na farko a shekarar 2013 ta hanyar amfani da kuɗaɗen ajiyarsa da kuma tallafin abokai da dangi.

Hakan ya biyo bayan samun ƙarin horo kan kula da gidajen abinci a birnin Paris.

A yanzu shi ne shugaban kantuna uku da suka ƙware a fannin ilimin dafa abinci a Afirka ta Yamma.

Nau'ukan abinci

A yanzu Boulingui shi ne shugaban kantuna uku da suka ƙware a fannin ilimin dafa abinci a Afirka ta Yamma.   

"Na gamsu da cewa an haife ni ne don zama mai dafa abinci. Sha'awa ce ta saka nii kuma za ta ci gaba da kasancewa da ni har karshen rayuwata," in ji Boulingi.

Ko da yake ya ƙware da girke-girken abincin Afirka da na kasashen Yamma, amma duk da haka ya yarda cewa yana da abincin da ya fi so.

"Gogewata a harkar dafa abinci da kuma tafiye-tafiyen da na yi a duniya, sun taimaka wajen ƙara inganta salon girkina," in ji Boulingi.

Ya ƙara da cewa "Ko da yake har yanzu da sauran ƙuruciyata, na san yadda ake dafa nau'ukan abinci da yawai na Afirka, da na Gabon da sauran kasashen duniya."

"Duk da haka, ina da abinci guda daya da na fi so. Wannan abinci shi ne gasasshiyar kaza da dodo wato plantain," ya fada cikin cikin farin ciki.

Ba tare da la'akari da hanyar da ta shigo da shi cikin harkar ba, Boulingi ya saka wa kansa ƙalubalen horar da matasa don ba su damar cimma burinsu, kamar yadda ya yi sama da shekara 20 da suka gabata.

TRT Afrika