Daga Abdulwasiu Hassan
Wayar hannu da ke haɗa zumunci a tsakanin miliyoyin zukata a cikin ƙasa mafi yawan al'umma a Afirka, a yau kuma tana zama sanadin rusa zamantakewa.
Wasan kyanwa da ɓera ake yi a kowane yammaci tsakanin Isa (ba sunasa na gaskiya ba) da matarsa a kan batun waya. Rabi (ba sunanta na gaskiya ba) ta tsiri al'adar son duba wayar mijinta a duk lokacin da ya dawo daga aiki.
A koyaushe takan ƙagu ta ga ya ajiye wayarsa a kan tebur don shiga wanka, ita kuma sai ta lallaɓa ta ɗauki wayar.
Kamar yadda ta saba, Rabi cikin gaggawa takan fara binciken wayar don ganin waɗanda suka kira shi da kuma saƙonninsa. Sau da dama hakan kan saka ta a cikin damuwa maimakon kwanciyar hankali.
Duk lokacin da na duba wayarsa, nakan ga wani abu da kan fusata ni. Da alama yana yawan hira da wasu matan," ta faɗa cike da jin takaici.
Yadda waya ke jawo matsala
Ba Rabi ce kadai ke da irin wannan halayya ba. A Nijeriya, wayar tafi-da-gidanka tana haifar da rashin jituwa tsakanin ma'aurata da dama, tana haifar da rashin yarda da kuma sanya shakku a cikin aure da dama.
Masaniyar ilimin halayyar ɗan'adam Aisha Bubah ta shawarci irin wadannan ma'aurata da su riƙa tattaunawa ta gaskiya a kan abubuwan da suke so da waɗanda ba so abokan zamansu su rika yi kafin a yi aure.
"Idan ba haka ba, za mu samu kanmu a yanayin da miji ko mata suke jin cewa ɗayan yana ɓoye abubuwa a wayarsa, kuma hakan zai iya yin barazana ga dangantakarsu,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
"Sirrin kiyaye daidaito da tabbatuwar aurenku cikin zama lafiyashi ne a guji yin duk wani abu da ka iya zama barazana ga zamantakewarku.
Idan har kuna barin wasu shaidu ko alamu da abokin zamanka ba ya so a kan wayarka, to hakan zai iya haifar da matsala,” in ji masaniyar halayyar ɗan'adam din da ke Abuja.
Matsalar da ta zama ruwan dare
Ko da yake za a iya ganin kamar ƙaramin abu ne, wannan rashin yarda da junan ya jawo har sai da wani tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban kasa a Nijeriyar ya taɓa ba da misali da matsalar.
Ya shaida wa ma’aurata a wajen auren gata da gwamnatin jihar ta yi wa mutum 1,800 kwanan nan cewa, “Ina da shawara guda daya a gare ku: Ka da ku dinga binciken wayar abokan zamanku, saboda hakan na daga cikin manyan dalilin da ke jawo mutuwar aure a zamanin nan.
Mutane da yawa a Nijeriya sun yi imanin cewa yawan duba wayar abokin zama yana shafar zaman aure sosai. Amma akwai mutane irin su Rabi da suke ganin ya zama wajibi su dinga binciken wayar mijinsu don sanin me yake ciki.
Waya wata hanya ce ta bin diddigi. "Ya wajaba a kaina na gano dalilin da ya sa yake yawan shafe lokaci yana amfani da waya. Yana yawan sauya lambar sirri ta buuɗe wayar tasa, amma ko yaushe ya sauya sai na gano sabuwar," ta gaya wa TRT Afrika.
Fayyace komai
Don yin zama na ƙeƙe da ƙeƙe, Rabi ta mayar da shi ƙa'ida cewa ba za ta taɓa ɓoye wa mijinta wayarta ko hana shi dubawa ba. Takan tabbatar ma ta ajiye ta wasarere a gabansa. Amma bai taɓa nuna sha'awar ɗauka ba balle har ya yi mata bincike.
A maimakon haka, ya fi damuwa da bincike da bin diddigin da take yi masa, kuma ya sha kai ƙararta wajen yayyenta da mahaifiyarta.
"Muna yawan yin faɗa kaca-kaca. Har malaman addini sun sha yi mana sulhu, amma ina, na riga na yi nisa, ba zan taɓa daina duba wayarsa ba," Rabi ta faɗa.
To mece ce mafita ga wannan masifa da take lalata zamantakewar aure a Nijeriya? Masaniyar halayyar ɗan'adam Bubah tana ganin dole a dinga tattaunawa ta gaskiya tsakanin ma'auratan da kuma yin bayani a kan duk wata alama da za ta iya dasa zargi a zuƙatansu.
Ma'auratan da ke takun-saka kan wannan batu na bukatar su zauna su yi tattaunawa ta ƙeƙe da ƙeƙe. Ya kamata su fahimci dalilin da ya sa hakan ke faruwa tun da farko, me ya sa ba za su samu fahimta a kan wannan batu da bai wani taka kara ya karya ba," in ji Bubah.
Abin ban haushin shi ne ba fa asarar rai ce aka yi ba. Na'urar da aka ƙirƙira da nufin sauƙaƙe hanyoyin sadarwa da ƙulla zumunci a yau ta zama abar da ke rusa zamantakewa.