Aso ebi ya yi suna matuƙa inda har waɗanda ba ƴan Nijeriya ba da ke halartar bukukuwa suna sakawa. / Hoto: Getty Images

Daga Abdulwasiu Hassan

Aso ebi, wani nau'in tufafi ne a al'adar Yarabawa wanda ake amfani da shi a wuraren bukukuwa, inda a halin yanzu ya bazu matuƙa a Nijeriya.

Irin yadda baƙi ke saka tufafin idan suka je wurin bukukuwa ya zama wani abu da aka saba gani musamman a ƙasar wadda ke Yammacin Afirka, inda ƴan kallo ake ɗaukar hankalinsu sakamakon yadda launin tufafin ke haskawa.

Ya zama wani bangare na kyakyawan yanayin zamantakewa - yana wuya a yi taro a kasance a wurin taron ba tare da ganin jerin mutane sanye da tufafi na Afirka iri ɗaya ba.

Me ya sa yan Afirka ke saka Aso ebi?

"Yana da kyau mutum ya juya ya ga ko ina duka abokansa sun saka tufafi iri ɗaya kuma hakan wata alama ce da za ta nuna cewa akwai yiwuwar an gayyace ka bikin," kamar yadda Hauwa ta shaida wa TRT Afrika.

Ko da ƴan Nijeriya na zaune a ƙasar waje, za a iya ganin aso ebi a cikin wannan hoton wanda aka ɗauka a birnin Santambul na Turkiyya. / Hoto: Anadolu Agency

Ita ma Fauziyya Sa'ad tana da irin ra'ayin Hauwa inda ta ce saka Aso Ebi na sa ta ji ta zama cikakkiyar ƴar biki a duk lokacin da ta je wurin bikin.

"Ina jin daɗi da kuma jin cewa ina cikin bikin," in ji ta.

Sai dai baya ga jin cewa mutum yana tare da ƴan biki, su ma waɗanda aka je bikin domin su suna jin cewa ƴan uwansu da abokansu suna son su sakamakon yadda suka halarci bikin nasu.

Irin yadin da ake amfani da shi wurin yin tufafin a wani lokaci wadda ke bikin kan saye shi da yawa wanda daga baya ta ya sayar da shi ga masu son halartar bikin.

Waɗanda suke sayen tufafin na Aso ebi na kallon hakan a matsayin wata hanyar bayar da gudunmawar kuɗi domin toshe wasu kafofi na hidimomin biki.

Takura wa mahalarta biki

Duk da yadda irin wannan abu ya shahara, akwai damuwa kan cewa yana takura wa waɗanda ba su da halin sayen tufafin da aka zaɓa a matsayin Ao ebi.

Akan yi Aso ebi domin wani biki na musamman, kamar yadda ake gani a wannan hoton wanda aka ɗauka a birnin Benin City na Jihar Edo a Nijeriya. / Hoto: Anadolu Agency

"Yana da matukar bakin ciki wani lokaci saboda ina jin kishi wani lokaci. Kawai dai ji nake kamar ba ni cikin abokan bikin kuma ba za a ba ka irin wannan kulawa ta musamman ba a wani biki da sauransu," kamar yadda Hauwa ta shaida wa TRT Afrika.

"Ba Aso ebi, ba abinci, babu babban teburi a gare ka. Sai dai a ƙarshe za ka kasance ba za ka sake saka kayan Aso ebi ɗin ba bayan bikin," in ji ta.

Fauziyya ta yi bayani kan dalilin da ya sa mutane ba su son saka Aso ebi bayan biki.

"Ba na son Aso ebi sakamakon duk lokacin da ka saka shi mutane sun san daga wurin da ya zo, da nawa aka saye shi," kamar yadda Fauziya ta shaida wa TRT Afrika.

Haka kuma Hauwa tana da wani abu da ba ta so idan ana maganar Aso ebi - takura mata sayen tufafin duk da cewa ba za ta iya saye ba.

Wani abu kuma da ba ta so game da sayen Aso ebi shi ne soke bikin da aka saka.

"Na kashe N25,000 kan Aso ebi na ƙawata inda aka fasa bikin kwanaki biyu kafin ranar. Shin duka wannan wahalar ta cancanta?" kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

TRT Afrika