Ƙarin mahaifa kan fito ne lokacin da mace ke iya ɗaukar ciki da haihuwar ɗa. / Hoto: Others

Daga Pauline Odhiambo

Mai wallafe-wallafe a internet 'yar Afirka ta Kudu, Owamie Netshivhazwaulu ta yi fama da ciwon ala'ada tsawon shekaru, kafin daga bisani ta samu sauki ta hanyar tiyata.

Ta yi fama da raɗaɗin ciwo saboda ƙarin mahaifa da ya tsiro a mahaifarta wanda ya girma bayan lokaci, inda ya haifar mata da tsananin ciwo.

Ta faɗa wa TRT Afrika cewa, “Na sha wahala idan ina al'ada tun daga 2015, wanda ya tilasta min shan magungunan rage zugi. A 2020 na gano ina da ƙarin mahaifa a lokacin da ni da tsohon mijina muna neman samun ɗa”.

Ƙarin mahaifa yakan fito ne a mahaifa da yake bayyana a shekarun da mace take iya ɗaukar ciki ta haihu.

Zubar da jini

A cewar masana, ƙarin mahaifa yakan bambanta a girma. Wanda aka fi gani shi ne mai haifar da zubar jinin al'ada mai daɗewa, da saka zugi, da ciwon bakin mahaifa, da yawan ko shan wahalar fitsari da kumburin ciki.

A wasu lokuta, ƙarin mahaifa yakan hana mace ɗaukar ciki.

Owamie ta ce, “Likita na farko da na gani da nake neman ɗaukar ciki ya gaya min cewa ba zan samu ɗa ba. Ya yi min sikanin da ya bayyana yadda mahaifata ta samu ‘nakasu’ kuma mafita ɗaya ita ce a yi tiyata don cire ta".

“Na ji matuƙar baƙin ciki kuma na kira goggota ina kuka saboda takaicin a ce ba zan haihu ba.”

Ƙanwar mahaifiyar Owamie ta ba ta ƙarfin gwiwa cewa ta tuntuɓi wani likitan mata na daban – wani mataki da ya ba ta kyakkyawan fatan samun haihuwa.

Owamie da ke birnin Johannesburg ta ce, “Likita na biyu da na gani ya ƙarfafa min rai cewa mahaifata ba ta da naƙasu kwata-kwata. Wato dai, sikanin ɗin da aka yi a baya sun tsufa saboda hotunan ba su fita da kyau ba. Abin da ya yi kama da naƙasu ashe ƙari ne da ya fi mahaifata girma”.

“Na ɗauki makonni biyu kafin na samu shawara ta biyu, kuma a lokacin ina ta yin fatan samun ciki.”

Abin kunya

Yayin da take yin bincike kan ƙarin mahaifa da tiyatar cire ta, an gargaɗi Owamie cewa ka da ta ambata halin da take ciki a danginta.

Owamie ta ambaci, “Cewa ina da mahaifata da ake cewa tana da ‘naƙasu’ da ba zan iya ɗaukar ciki ba ya sa abin ya zama abin kunya a yawancin yankunan Afirka. Hakan ya sa ni tsoro har na ƙi faɗa wa mahaifina”.

Abin ya yi muni lokacin da wasu maƙwabtanta suka samu ɗa, abin da ya sa Owamie ta ji ƙarin burin samun nata ɗan.

“A lokacin na yi jimamin uwata marigayiya saboda na yi ta tunanin da tana raye, da ta yi iya ƙoƙarinta wajen kyautata lamarina. Na yi sa'a, ina da ƙanwar mahaifiyata da ta shige gaba kuma take tsaya mini yayin da nake fama.”

Yin magani

Magance ƙarin mahaifa ya haɗa da yin maganin da ba tiyata ba da kuma ta hanyar tiyata. Samun magani ya danganta kan girman ƙarin da kuma inda ƙarin yake, ko kuma alamun cutar.

Dr Eunice Wangeci, wata likitan mata a Nairobi ta ce, “Ba ko yaushe ƙarin mahaifa ke buƙatari magani ba, musamman idan ba su nuna wata alamar ciwo. Wasunsu sukan motse su da kansu, amma idan suna da girma sosai kuma suna saka ciwo, ana ba da shawarar yin tiyata”.

“Kuma ana iya amfani da magunguna masu hana kumburi da masu daidaita sinadaran hormone don sauƙaƙa raɗaɗi da rage zubar da jinin al'ada.”

Idan lamari ya tsananta, ana yanke mahaifa don kawo waraka gabaɗaya.

Kawo ƙarshen tsangwama

Owamie ta faɗi cewa, “Kafin a min tiyata, na yi magana a tashata ta YouTube. A lokacin na yi tunanin ni kaɗai ke fama da ciwon ƙarin mahaifa, don haka na yi bidiyo lokacin da nake fama da tsoro saboda tunanin cewa mutane za su min dariya su raina na".

Ta ƙara da cewa, "Amma mabiyana sun nuna mini goyon baya inda wasunsu suka ba da labarin matsalarsu ta ƙarin mahaifa da kuma zaɓin magani da ya musu aiki. Maganganunsu sun taimake ni na gano cewa samun ƙarin mahaifa ba abin saka kunya ba ne."

"Har yanzu akwai masu nuna abin kunya ne idan kana da karin mahaifa amma na yi imani cewa ta hanyar ilmantar da kawunanmu kan alamun cutar da maganinta, da hakan zai fi kyau."

Me ce shawararta ga sauran mata da ke da ƙarin mahaifa?

Ta kammala da cewa, “Lokacin da nake tasowa, da yawanmu an gaya mana cewa samun ciwo yayin al'ada wani ɓangare ne na kasancewa mace, amma hakan ba gaskiya ba ne sam".

"Nakan samu matsanancin ciwo yayin al'ada amma tun bayan tiyatar da aka min ban sake samun ciwo ba. Na ma daina shan maganin rage zugi kuma yanzu ina fatan wata rana na samu haihuwa.”

TRT Afrika