Daga Pauline Odhiambo
Idan ka ziyarci babban birnin Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, wato Kinshasa, ko Brazzaville, babban birnin Jumhuriyar Congo da ke maƙwabtaka, za ka haɗu da mutane maza da mata da ke shiga ta musamman.
Abin da shiga ta musamman ke nufi a nan, shi ne tufafi masu kaloli daga sama har ƙasa, ko shiga ta a zo a gani da tufafin manyan kamfanonin kwalliya na duniya. Kuma ko ina ka je hakan yake, kan layuka, ko cikin unguwanni, za ka ga masu shiga mai ɗaukar hankali.
Bari mu fayyace abin, Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo da Jumhuriyar Congo ƙasashe ne biyu daban daban. Belgium ce ta mulki Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo, yayin da Faransa da mulki Jumhuriyar Congo.
Babban birnin Jumhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo shi ne Kinshasa, yayin da babban birnin Jumhuriyar Congo shi ne Brazzaville.
Wani bayani shi ne manyan biranen biyu Kogin Congo ne ya raba su, mai tsawon kilomita 7.
Masana tarihi sun gano asalin salon shigar 'yan Congo ya faro ne daga shekarun 1920s, lokacin da ƙasashen biyu suna ƙarƙashin mulkin mallakar ƙasa ɗaya.
Yayin da wani ɓangare na al'ummar suke haɗa gamayyar yaƙi da 'yan mulkin mallaka, wani rukunin al'umma a Kinshasa da Brazzaville sun zaɓi su ringa shiga irin ta masu mulkar su.
Wannan rukunin ba wai na gamagarin mutane ba ne, hadiman turawan Faransa ne da na Belgium.
Wata ta'ada ce ta cewa, "E, kai ne ubangidana, amma zan iya irin shigarka da yin irin rayuwarka."
Hadiman suna tara 'yan kuɗaɗensu na albashi su sayi tufafin al'ummar Yamma, yayin da wasunsu da aka tura aiki a Belgium ko Faransa suke dawowa Congo da tufafin da iyayen gidansu suka ba su.
"Sape yana nufin al'ummar "ambianceurs", kuma mutane ne 'yan kwalliya," in ji wani ɗan TikTok St Germain de Londres.
A harshen Faransanci, ambianceurs su ne mutane da ke nishaɗantar da mutane a wajen biki ko taro.
"Wasu sukan saka tafafi masu kauri da takalman hunturu, duk da cewa suna ƙasa da ke nahiyar da ba a buƙatar kayan sanyi," cewar wani ɗan Tiktok.
Masana tarihi sun rubuta cewa yin shigar wani nau'i ne na gwagwarmaya irin na al'ummar Congo. Cikin shekaru, salon shigar ya samu farin jini tsakanin rukunan mutanen al'ummar ƙasashen Congo.
Salon ya cigaba da haɓaka sosai, inda wasu 'yan Congo suke haɗa nau'o'in al'adunsu na tufafi tare da salon shigar Turawa, wanda ya fito da salon da ake kira a yau da al'adar 'Sapeur'.
Al'ummar Congo suna kiran shigar da La Sape, wanda ke nufin "yin shiga ta bajinta."
A fahimtar mutane, salon shigar yana nufin bayyana ra'ayi, tarihi, da nuna salon ƙashin-kai. Kuma wannan salo na musamman ya ƙunshi sanya hular malafa, da sandar dogarawa, da askin 'yan gayu, da jaket mai jan hankali, da takalmin fatar kada, da tufafin ƙarya.
Masu nazari sun rubuta cewa salon sapeur salo ne na rayuwa a gidan da kuɗin hayar wata guda ya kai dala 50, amma mutum zai adana kuɗi don sayan tufafin ƙawa da takalmin da farashinsu ya kai dala 300.
"Ya kamata Masu sanya tufafin su adana kuɗinsu, su yi jari maimakon ɓarnatar da kuɗi kan tufafi masu tsada," cewar M. G Evie a shafin Tiktok.
Sai dai da yawa daga masu sanya sapeur suna cewa manufarsu ɗaya ce: suna nuna cewa suna iya rayuwa mai kyau duk da matsin arziƙi.
Wasu kuwa sukan ce sabo ne kawai, kuma barin al'adar ba zai yiwu ba. Duk da maƙudan kuɗin da suke kashewa kan tufafin ƙawa, hakan abin alfahari ne kuma babu asara.
Ana alaƙanta mawaƙin Rhumba ɗan Congo, Papa Wemba da yaɗa al'adar La Sape. A zahiri ma, ya taɓa cewa La Sape tamkar addini yake.
Sakamakon haka an saka wa Papa Wemba laƙabin "le Pape de La Sape", ma'ana "baban 'yan sapeurs".