Daga Charles Mgbolu
A daidai lokacin da ake ban-kwana da shekarar 2023, tuni fitaccen mawakin Nijeriya Rema ya fara hutun karshen shekara domin ya samu ya sarara.
Ya bayyana a karshen watan jiya cewa ya tafi hutun ne ‘bisa shawarwarin’ likitocinsa, wanda hakan ya sa ya dakatar da duk wasu tarukan da ya shirya halarta na karshen shekara.
Sai dai duk da haka, akwai abubuwa da dama da suka faru a bana da suka zama tilas mawakin ya yi tunkaho da su.
An saurari wakokin albam dinsa mai suna Rave and Roses sama da biliyan 3 a manhajojin sauraron waka, sannan wakarsa ta ‘Calm Down’ wadda ke cikin albam din, ta kafa tarihi da damai ita ma.
Shin me ya sa mawakin dan shekara 23 ya samu nasarori haka? Me ya yi daban? Za mu yi kokarin amsa wadannan tambayoyin ta hanyar tariyar abubuwan da suka faru, da kuma nasarorin da matashin mawakin ya samu.
Hadakar waka da mawakan duniya biyar Kimanin wata daya bayan ya saki wakar ‘Calm Down’ a 11 ga watan Fabrairu, sai Rema ya fitar da albam dinsa mai suna Rave & Roses a 25 ga Maris na 2022.
A cikin kundin Rave & Roses akwai wakoki 16, inda a ciki ya yi hadaka da mawakan duniya irin su Chris Brown dan Amurka da 6Lack shi ma dan Amurka da AJ Tracy daga Birtaniya da Yseult dafa Faransa.
Hadakar sun yi kyau sosai, inda Rema ya yi amfani da damar wajen daga darajarsa da daga tauraronsa a duniyar mawaka.
Kafa tarihin da ya yi a duniyar wakar Amurka da Turai ce ta fara haska Rema a duniyar waka, sannan tun daga lokacin, gaba kawai yake yi.
Farko-farko
Rema ya fara zagayen tallata albam dinsa ne ta hanyar yada su a kafafen sadarwa da taruka da kalankuwa. Ya samu nasarar sayar da dukkan tikitin shiga taronsa a Arewacin Amurka da Turai, ciki har da dandalin 02 da ke Landan.
Wakokinsa duka na asali ne, kuma yana da tsari na daban. Kawai dama bukatarsa tauraronsa ya fara haskawa, wanda kuma ya samu.
Haka kuma ya kara samun nasara ta hanyar wasu abokan hulda fitattu irin su Selena Gomez, wadda ta wallafa hotonta da Reama a shafukanta na sada zumunta a ranar 17 ga Agustan 2022, sannan ta rubuta cewa, “Ku saurare mu.”
Wannan hoton ya kara daga mawakin a shafukanta masu jimillar mabiya sama da miliyan 400.
Manhajojin wakoki na zamani
Kididdiga daga fitacciyar manhajar sauraron waka ta Soptify ta bayyana cewa a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka wato MENA, mawaka irin su Rema da Ckay da BurnaBoy da sauransu a matsayin wadanda aka fi sauraron wakokinsu.
Wakokinsu idan aka hada jimillar sauraronsu da aka yi, su ne kan gaba a wakokin da aka fi saurara a kididdigar Indian International Music Chart da MENA, inda Rema ya shiga kundin bajinta na Guinness World Record.
Sakin wakokin Rema ya zo daidai da lokacin da salon wakokin Afrobeats suke samun karbuwa a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka da Asiya.
‘Baitoci cikin taushin murya’
A dukkan wakokin Rema, masu sauraro suna yaba masa bisa amfani da kalmomi masu saukin fahimta.
Da farko, wasu masu kushe sun fara bayyana wakokinsa da rashin armashi, amma lallai daga baya an gane cewa akwai wani boyayyen sirri a salonsa.
Wadannan boyayyun sirrukan sun taimaka wajen kai wakokin Rema kasashe da dama.
Wakokinsa da yake yi cikin tattausan murya a wani yanayi da ya kira da Afro-rave-salon wakokin da suke da alaka da wakokin hip-jop, da wakokin Afirka da tsarin daukar wakokin da ke bayyana yanayin saututtukan inda ake daukar wakar da sauransu.
Wakar 'Calm Down'
Watakila za a iya cewa ita ce babbar nasararsa. Wakar ‘Calm Down’ ita ce babba a wajen Rema-ya shiga kasuwa da ita, inda ya kafa tarihi da dama da ita.
Ba karamar nasara wakar ta samu ba bayan ya yi ta shi kadai, sannan sabunta ta da ya yi mawakiyar Amurka Selena Gomez sai ta kara daraja.
Yanzu haka wakar tana cikin wakokin da aka saurara sau sama da biliyan daya a Spotify, inda ta shiga wannan matakin tun a Satumba.
Wadannan nasarorin ne suka bude wa Rema wasu kofofin, inda masoyansa suke ta kiran neman kari.