Masana sun bayyana cewa shan zobo yana da matukar alfanu ga lafiyar jikin dan adam. / HotoL Reuters

Daga Abdulwasiu Hassan

Karyewar darajar naira a Nijeriya ta yi babbar illa ga jama'ar kasar wadanda tuni suka dade suna fama da hauhawar farashi.

Masu aikin albashi ne lamarin ya fi shafa sakamakon abin da suke samu ba ya biya musu bukatunsu.

A cikin wadannan lokuta marasa tabbas, an samu mafita daga inda ba a yi zato ba a wani bangare na 'yan Nijeriya wadanda suke noma zobo da kuma sayar da shi kasashen waje.

Bashir Tukur Abubakar na daga cikin ma'aikatan gwamnatin da suka yi sa'a inda yake gauraya aikinsa na albashi da kuma sana'ar da yake yi a karshen mako ta saya da sayar da zobo.

Bashir yana tafiya zuwa kauyuka ya sawo zobo domin ya sayarwa wa masu sari da ke fitarwa kasashen waje.

Akasarin zobon da ake nomawa ana sarrafa shi, daga ciki har da wani lemo da ake yi mai suna Zobo.

A kasar Mexico, wadda tana daga cikin wadanda suka fi sayen zobo, ana amfani da shi wurin yin wani nau'in shayi mai sanyi wanda ake kira Agua de Jamaica.

Mexico ce kasar da ta fi sayen Zobo daga Nijeriya. / Hoto: AFP

Ba Bashir ne kadai ke cin gajiyar zobo ba a kasuwar wadda ke da tarin albarka. Auwalu Ahmed wani dan Najeriya ne wanda zuwa yanzu kasuwancinsa na tafiya daidai.

"Akwai kasuwanni da yawa da ake sayar da zobo a arewacin Najeriya, duk da cewa ba za ku iya siyan haja ba kawai kuna fatan samun riba mai kyau a sayar da ita," in ji Auwalu.

"Akwai mutane masu gaskiya wadanda za ka iya ba su kudinka, za su iya shiga lungu da sako a cikin kauyuka domin su sayo maka zobo daga manoma."

Ana sayar da kilo daya na zobo kusan 1,120. Bayan samunsa da yawa daga kauyuka, 'yan kasuwa irin su Auwalu na gyara shi sannan su sayar da shi ga masu fitarwa kasashen waje.

Tafiya zuwa Mexico

Ana fitar da zobon Nijeriya mai yawa zuwa Mexico inda kusan kaso 85 cikin 100 na zobon na tafiya can.

A shekarar 2017, yawan fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje bai yi tasiri ba, lamarin da ya haifar da cikas a kasuwar bayan Mexico ta hana shigar da zobon Nijeriya. Lamarin da ba zato ba tsammani ya sa mutane da yawa sun yi asarar kudade masu yawa.

Sai dai abin godiya a nan shi ne lamarin ya canza sosai, tun bayan da kasar da ke yankin Latin Amurka ta ci gaba da sayen zobon na Nijeriya.

Tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne kan kudaden shiga daga man fetur amma hukumomin kasar na kokarin neman mafiya ta hanyar habaka noma.

A karshen 2022, jakadan Nijeriya zuwa Mexico ya bayyana cewa kasarsa na sa ran samun dala biliyan uku a duk shekara tasayar da zobo zuwa kasar ta Mexico.

Nijeriya ta yi hasashen samun dala biliyan uku a duk shekara daga cinikin zobo. / Hoto: Reuters

Karyewar darajar naira da aka aka samu a baya-bayan nan ya sa kasuwancin ya kara samun riba ga wadanda abin ya shafa.

"Ta yadda farashin dala ya kara tashi, haka shi ma farashin zobo ya kara sama," kamar yadda Hashim Bello Dabai, wani mai sayar da zobo ya shaida wa TRT Afrika.

Hashim ya jima yana wannan kasuwancin a Kano tun daga 2015 bayan ya kammala karatunsa na sakandire a 2015.

"Babban kalubalen da muke fuskanta shi ne wasu daga cikin masu sayar da shi kan gauraya zobon da kasa ko kuma furanni domin ya kara nauyi a cikin buhu," in ji shi.

Sakamakon lalataccen zobo abu ne da masu fitarwa kasashen waje ba su siya, da zarar an yi watsi da shi, hakan zai iya zama asara ga 'yan kasuwa irin su Hashim.

Faduwar darajar naira idan aka kwatanta da dala yana sa manoma da yawa bayar da fifiko wajen noman amfanin gona da za a yi amfani da su wajen fitar da su zuwa kasashen waje kamar irin su ridi da citta, baya ga zobo.

Usman Muhammed wanda manomi ne a jihar Jigawa, ba wai kawai noman zobo yake yi ba, har ma yana siyan zobon daga wasu don biyan bukatun masu sayan sa a kai a kai.

"Ina gyara zobon kafin na sayar da shi ga masu fitarwa, wadanda ke son mafi inganci. Zobo ba abu ne da ake nema a Nijeriya kawai ba. Ya mamaye duniya," in ji shi.

Ana hada zobo da kayan hadi daban-daban inda ake dafa shi ya zama lemo. / Hoto: Others

Kasuwar zobo ta kara fadada ta yadda masu sayensa a cikin gida domin yin lemonsa suna fafatawa da wadanda ke kasar waje.

Matsalar tsaro

Duk da cewa Zobo ya kasance wani abu da manoma da 'yan kasuwa ke alfahari da shi, amma duk da haka ana fuskantar kalubale.

"Duk da fa'idar da kasuwancin ke da shi, gwamnati ko masu saka hannun jari ba su da sha'awar taimaka wa manoma su haɓaka," in ji Usman.

Wata matsala kuma ita ce ta tsaro wadda ke damun akasarin yankunan da ake noma zobon.

Wuraren sun hada da Jigawa da Borno da Yobe da Bauchi da Katsina wadanda akasarinsu sun bayyana cewa 'yan bindiga sun yi masu barna a 'yan shekarun nan.

Gwamnatin Nijeriya ta samu ci gaba wurin dakile wasu daga cikin 'yan bindigar ta hanyar tura dubban jami'an tsaro yankunan.

TRT Afrika