Daga Sylvia Chebet
Matakin da shugaban Kenya William Ruto ya ɗauka na ƙin sanya hannu kan sabuwar dokar haraji mai shirin ɓullo da sabbin haraji, ya yi matuƙar rage tunzurin da ƙasar ta faɗa, sai dai hakan na iya rage kimar shugaban a cewar masharhanta.
A wajen gwamnatin Ruto, ƙara harajin ya wajaba don a haɓaka kuɗin-shiga da kusan dala biliyan $2.7, domin a biya kuɗn ruwa kan bashin ƙasa, da rage giɓin tattalin arziƙi da ba wa gwamnati damar cigaba da aiki.
Sai dai masu zanga-zanga sun kalli sabbin harajin a matsayin matakin azabtarwa, ganin cewa da ma tsadar rayuwa tana damunsu, kuma sun ji takaicin yadda majalisa ta yanke hukuncin amincewa da ƙudurin dokar.
Sun far wa Majalisar Dokoki, wadda ta ke da tsaro mai tsauri, inda suka cinna wa wani yankin gininta wuta yayin da 'yan majalisa ke tserewa, har wasu suka kuɓuta ta a cikin motar asibiti.
Sauyin matakin da shugaban ya yi ranar Laraba ya bayar da mamaki, ganin ce wa ya ci alwashin sanya hannu kan ƙudurin. Ba a yi zaton ganin matakin ba, amma masana tsarin mulki sun ce hakan ya wajaba bayan da zanga-zangar ta koma tashin hankali.
Hukumar Haƙƙin Binl-adama ta Kenya, KNHRC ta ce aƙalla mutane 22 ne suka rasu, yawancinsu waɗanda aka kashe lokacin da masu gangamin suka far wa majalisa ranar Talata.
"A siyasance, matakin na da mummunan tasiri kansa idan ya ci gaba a irin wannan tsari,” in ji wani lauya a Kenya Charles Kanjama da yake zantawa da TRT AFRIKA, inda ya ƙara da cewa: “Akwai wani karin magana mai cewa mai hikima ya san lokacin da da ya kamata ya sauya ra'ayinsa.”
Shugaban ya amsa cewa ƙudurin ya haifar da “yaɗuwar rashin jin-daɗ” kuma ya saurari koeken al'ummar Kenya.
“Na ba da kai”
"Na ba da kai don haka ba zan rattaba hannu kan dokar hada-hadar kuɗi ta 2024 ba, kuma za a janye ta daga baya," Ruto ya faɗa yayin wani jawabi ga kasa ranar Laraba.
“Ta yiwu wannan tayin sulhu ne,” in ji Bobby Mkangi, wani lauya masanin shari'a a Kenya, wanda ya yi nuni da cewa: “Da wuya ka ga ɗan siyasa ya, ballantana ma shugaban ƙasa, a ce ya ba da kai.”
A cewar masana tsarin mulki, yana da wuya ka ga matakan kafa doka sun yi nasara ba tare da ka ga an yi adawa da ita ba, amma duk da haka sai ka ga sun tsallake.
Kanjama ya yi nuni da cewa,“Suna yin tunani bisa lissafin siyasa, wato ko zan iya gamsar da mafi yawan 'yan majalisa su goyi bayan wannan ƙuduri? Kenan, batun shi ne shi (Ruto) bai yi lissafi mai kyau ba game da tsananin ƙyamar da mutane ke yi wa batun matakansa”.
Mkangi ya bayyana cewa, “Wataƙila akwai mutane a gwamnatinsa da suke ganin akwai buƙatar a matsa wajen tabbatar da ƙudurin ya zama doka, kuma an cimma batun domin gwamnati a nan gaba, ba a kalle ta a matsayin mai rauni ba”.
Ƙudurin ya wuce a majalisa ranar Talata, “amma ra'ayin mutane ya juya zuwa adawa da shi, kuma ba wanda ake alaƙantawa da shi kamar shi kansa shugaba Ruto,” cewar Kanjama.
A kamfe ɗinsa, Ruto ya nuna kansa a matsayin ɗan "buga-buga”, wanda ya sha alwashin ɗabbaƙa matakan da za su rage raɗaɗin tattalin arziƙi ta hanyar haɓaka samun kuɗin al'ummar Kenya. Amma sai gashi “'yan fafutuka” da suka mara masa baya, sun ga tsarin harajin gwamnatinsa ya ci amanarsu.
Fusatattun masu zanga-zanga sun fara kiran da ya yi murabus, baya ga neman ya janye ƙudurin dokar da ya gabatar.
Shugaba Ruto ya faɗa ranar Laraba lokacin da ya sanar da cewa ba zai sanya hannun kan ƙudurin dokar ba, inda ya ce, "Al'umma sun yi magana".
"Zan gabatar da tayin hulɗa da matasan ƙasarmu, 'ya'yayenmu maza da mata don mu saurare su," in ji Ruto, a wani yunƙuri da ya saɓa wa jawabin da ya yi na daren Talata lokacin da ya kwatanta wasu masu zanga-zangar da "masu aikata laifuka."
Wasu daga cikin matasan sun ɗauki jawabin shugaban a matsayin nasara ga adawarsu, amma wasu har yanzu ba su gamsu ba kuma suna shakkar alƙawuransa.
“An janye ƙudurin amma shin za ku dawo da waɗanda suak rasu duniya?” cewar Hanifa, ɗaya cikin 'yan zanga-zangar wadda aka tsare na ɗan lokaci yayin gangamin na ‘Mamaye Majalisa’, a wani rubuta a X.
Daughter of Isiolo, wata 'yar zanga-zanga ita ma ta wallafa a X cewa, “Janye ƙudurin da Shugaba Ruto ya yi, wani mataki ne ƙarami, amma bai wadatar ba wajen magance matsalolinmu. Muna buƙatar gagarumin garanbawul don warware manyan matsalolin Kenya.”
“Ina ganin akwai tunanin cewa zanga-zanga a tituna za ta iya zamowa babbar barazana wadda za ta ci gaba da cutar da ƙarin mutane,” in ji Kanjama, da yake kwatanta tunanin masu gangamin.
“Akwai mutane da suka gina fushinsu kan gwamnatinagainst… kuma ba za ta tafi haka nan kawai ba.”
Mkangi ya yi imanin cewa kafin dawo da amincinsu kan gwamnati, dole cikin 'yan watanni masu zuwa “su ƙarfafa mayar da hankali” kan tsumi da tanadi, da kaucewa ɓarnata dukiya a wajen gwamnati.
“Ya kamata a gaba mu daina ganin jami'an gwamnati suna tafiye-tafiye, musamman zuwa ƙasashen waje, da kuma jerin gwanon motoci, da ire-iren nuna kwalliya da muke gani a kafafen sada zumunta, da kuma 'yan siyasa su ringa nuna nasarorinsu.”
A yanzu gwamnatin Ruto tana fuskantar ƙalubalen inganta tattalin arziƙin ƙasa, da rage hauhawar farashi, da samar da ayyukan-yi da sauran damarmakin samun kuɗi ga dubban matasa marasa aikin-yi don a maido da amincin da ke tsakanin jama'a da jagororinsu.
Duk da ƙin amincewa da ƙarin harajin, masu shari suna ganin cewa har yanzu gwamnati tana da damar samo dabarun nemo kuɗn shiga sama da yadda take samu yanzu.
Mkangi ya yi amanna cewa “A gaskiya za mu iya ƙara yawan kuɗn harajin da ake tarawa idan muka toshe hanyoyin da kuɗaɗen haraji suke zirarewa daga kashi 14% zuwa har kashi 20% na ma'aunin GDP”.
“Idan Hukumar Haraji ta Kenya ta mayar da hankali kan tabbatar da karɓo harajin da ake da su yanzu, za su iya cike giɓin da fasa shigo da sabbain harajin zai haifar.
Matsalolin da aka gada
Masu sharhi suna ganin cewa wasu matsalolin da ake fama da su a kasar Kenya, kamar cin hanci da almubazzaranci da dukiyar al'umma, ba daga gwamnatin Ruto suka samo asali ba, sun faro daga gwamnatocin da suka ganace shi.
"Wannan kudurin na kara kudaden haraji shi ne ya tada kura, ko kuma a ce shi ne ya harkuza mutanen Kenya," in ji Mkangi.
"Shi ya sa ake tambayar me ya sa za ka kara mana kudaden da kake karba da wajenmu alhalin ba ma ganin komai a kasa.?"
A daidai lokacin da aka kasa magance matsalar amana a kasar, gwamnatin Ruto tana kuma fama da matsalar biyan bashin shillings triliyan 11 wato Dala biliyan 86, wanda ya kusa kai kashi 70 na kudin shigar kasar.
Sai dai kuma Kenya ta kasance tana fama da matsalar bashi tun kafin Ruto ya karbi mulki a Satumban 2022.
Kanjama ya yi amannar cewa Ruto ya assasa kudurin ne watakila ba wai don yana son ya kuntata wa mutanen Kenya da karin haraji ba, sai dai kawai don yana tunanin ta wannan hanyar ce kadai za a daidaita tattalin arzikin kasar.
Amfani da matasa
Ba kamar sauran zanga-zangar da aka yi a Kenya a baya ba, wannan zanga-zangar ta matasa ce wadda aka fara a ranar 18 ga Yunin bayan Ministan Kudin kasar ya gabatar da kudurin a majalisa, sai zanga-zangar ta fara kankama a kafofin sadarwa.
Lokacin da suka fara zanga-zangar, ba su da jagora, kawai sun samu hadin kai ne a kan abu daya ba tare da bambancin siyasa ko addini ko kabilanci.
Matsalar ita ce ta yaya Shugaban Kasa zai tattauna da matasan da ba su da jagora? Lamari ne mai cike da rudu, wanda hakan ya sa masu sharhi suke gargadin a bi a hankali. "Ba mu ba ne za mu yanke wa matasan abin da suke so," inji Mkangi.
Kanjama ya kara da cewa, wata hanya da za a iya bi wajen tattaunawa da matasan shi ne, "a bi su zuwa inda suke" - wato a kafofin sadarwa.
"Ta kafofin sadarwa ne suke fara kaddamar da zanga-zangar, ta twitter da TikTok. Don haka da shi ya kamata mu yi amfani wajen isa zuwa gare su."
"Matasa ne 'yan zamani. Da ka yi magana da wasu daga cikinsu, sakon zai isa zuwa ga sauran. Don haka ba sai an tattara matasan baki daya ba a filin wasa."
Amma abu mafi muhimmanci shi ne abin da Shugaban Kasa da gwamantinsa za su yi, matakan da zai dauka ne za su nuna inda ya dosa, da kuma ba matasan karfin gwiwar aminta da sulhun da ya yi alkawari a ranar Laraba.
"Ina tunanin idan ya dauki matakai masu kyau, al'ummar Kenya za su aminta da shi, sannan yunkurinsa na ja da baya, ba zai zama tsoro ba, sai dai wani yunkurin hana kasar fadawa cikin rikicin," in ji Mkangi.