Kimanin mutane miliyan goma irin wannan iyali sun rasa matsugunansu tun bayan barkewar yakin Sudan: Hoto/NRC

Daga Abdulwasiu Hassan

Rashin mayar da hankali da ake yi a kan rikicin da ake fama da shi a Sudan yana ƙara tsanani sosai yayin da sauran a'amuran siyasar duniya ke mamaye kanun labarai da kuma zuciyoyin jama'a, duk da irin yadda kungiyoyi kamar Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway (NRC) ta bayyana yaƙin da "mafi girman rikicin jinkai a duniya".

Rahotannin da ke fitowa na nuni da irin wahalhalun da miliyoyin 'yan kasar Sudan ke ciki a rikicin da ake yi tsakanin sojojin kasar da dakarun sa-kai na Rapid Support Force (RSF) tun bayan barkewar fada a ranar 15 ga Afrilu, 2023.

Fiye da mutum miliyan 10 ne suka rasa muhallansu a yankuna da birane da garuruwa, da kauyuka waɗanda ikonsu ke sassauyawa a tsakanin bangarorin da ke rikici da juna. Adadin wadanda suka mutu ya haura 20,000.

Bayan da ya ziyarci Port Sudan da ke gabar Tekun Red Sea da kuma Darfur, Sakatare Janar na NRC Jan Egeland ya yi gargadin cewa za a fuskanci yunwa idan ba a gaggauta kai dauki ga mutanen da suka makale a kasar ba.

"Abin bakin ciki ne a ce ba za mu iya taimaka wa miliyoyin mutanen da ke fama da yunwa da tashin hankali a wannan yaƙin da ke yaduwa a fadin Sudan ba," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

Ba ranar tsagaita wuta?

Har ya zuwa yanzu, hanyoyin warware rikice-rikice na kasashen duniya ba su ma iya zartar da kudurin tsagaita wuta a Sudan ba, balle a aiwatar da shi.

Hasina, wacce ’yar asalin Habasha ce, ta gudu daga Khartoum tare da ‘ya’yanta uku a farkon yakin: Hoto/NRC

A halin da ake ciki dai fada ya bazu zuwa akalla 13 daga cikin jahohi 18 na kasar ta arewacin Afirka, lamarin da ya kara tabarbare yanayin jinƙai.

"Sudan na fama da matsalar gudun hijira mafi girma a duniya, mutum miliyan 11 ne suka rasa matsugunansu a cikin kasarsu, kuma mutum miliyan uku ne ke zama a matsayin 'yan gudun hijira a kasashe makwabta.

"Wannan ya zama lamari mai ban mamaki da ya shafi mutum miliyan 14 wadanda dukkansu suka tsere daga gidajensu saboda tashin hankali," in ji Egeland

Yunwar da ke kunno kai a kan al’ummar ya sa miliyoyin mutane da ke tururuwar ƙaura duk da ba su da wata alaka da yakin.

"Yanzu dole ne mu magance matsalar yunwa mafi girma a ko ina cikin duniya. Wasu mutum miliyan 20 na bukatar agajin jinƙai. Akwai karancin agaji da kuma cikas da yawa na taimakon," Sakatare-Janar na NRC ya koka.

A kowane yanayi

Dimbin jama'a na barin Darfur a baya-bayan nan don guje wa tashin hankali da yunwa yayin da kayayyaki ke ƙarewa kuma da kyar kayan agaji ke shiga.

Jan yana zagayawa a wata unguwannin da aka lalata a Al Geneina: Hoto/NRC

"Abin da na gani a Darfur shi ne cewa a kowace rana mutane na gudun hijira, musamman a El Fasher da ke arewacin Darfur - a wani bangaren kuma sukan yi hakan saboda tashin hankali da kuma saboda rashin abinci da rashin samun taimako a Geneina, wanda shi ne babban birnin yammacin Darfur," kamar yadda "Egeland ta shaida wa TRT Afrika.

"Na ga yankuna da dama da aka lalata aka ƙone, da sace-sace, ciki har da ofishinmu da ke Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway."

Sai dai duk da tashe-tashen hankula da rashin tabbas da ake fama da shi a kasa, hukumomin agaji ba su yi kasa a gwiwa ba wajen ba da taimako ga fararen hular da ke da alhakin yakin.

A cewar Egeland, NRC tana ba da agaji a yankunan kudanci, gabashi, da arewacin Sudan. Hakan ya hada da samar da tallafin fulawa da ake samu daga Turkiyya zuwa gidajen burodi kusan 350 a yankunan da abin ya shafa domin amfanin jama'a.

"Muna yin hakan kai tsaye tare da ma'aikatan agaji 400 ko kuma ta wasu ƙungiyoyin haɗin gwiwa 50," in ji shi.

Kiran kai taimako

NRC na kokarin kara yawan gidajen burodin masu cin gajiyar da ke samun tallafin fulawa zuwa 900, wanda ya bazu a Darfur da sauran wurare a kasar.

Gidajen burodin Sudan za su iya aiki idan suka dan samu taimako. Hoto/NRC

"Wannan yana nufin mutane rabin miliyan za su iya samun tallafin burodi kowace rana ta wannan aikin," in ji Egeland.

Babban ƙalubalen yaƙi da yunwa na iya ƙara dagulewa sai dai in an sami ƙarin taimako, tare da wani shiri na duniya na matsa wa bangarorin da ke gaba da juna damar baiwa ma'aikatan agaji damar shiga cikin fararen hula.

TRT Afrika