Daga Sylvia Chebet
Wani rikici na shari'a da ke ƙara ruruwa tsakanin Jamhuriyar Dimokuradiyar Kongo da kamfanin Apple game da rassan Silicon Valley behemoth a Faransa da Belgium da ake zargin suna amfani da "ma'adinan rigingimu" da aka samo daga ƙasar da ke Tsakiyar Afirka.
Ƙorafin da DRC ta shigar game da Apple a ranar 17 ga watan Disamba ya danganci batun da suke yi kan kayayyakin da kamfanin ke amfani da su ne ana samun su ne ta hanyar rashin zaman lafiya sakamakon akwai masaniya kan cewa ana amfani da kuɗin ma'adinai domin tallafa wa masu riƙe da makamai da ke aikata kisa da cin zarafi ta hanyar lalata.
DRC ta kasance wurin da ake samun ma'adinan Tin da Tantalum da Tungsten, waɗanda dukansu ana amfani da su wurin ƙera kwamfuta.
Wasu daga cikin wuraren haƙar ma'adinan da ke kai ma'adinai ga kamfanonin fasahar, ƙungiyoyin 'yan bindiga ne ke iko da wuraren ma'adinan, waɗanda Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙungiyoyin 'yan ta'adda suka bayyana a matsayin laifukan cin zarafin bil'adama.
Tun a shekarun 1990 ne ake gwabza fada tsakanin kungiyoyin masu dauke da makamai a yankunan gabashin Kongo.
Gasar neman ma'adinai na daya daga cikin abubuwan da ke haifar da rikici yayin da 'yan tawayen ke ci gaba da sayo makamai da kudaden da ake samu daga fitar da su ba bisa ka'ida ba, wadanda galibi ana safarar su ta wasu kasashe.
A cikin shekaru 25 da suka gabata, an kashe 'yan Kongo fiye da miliyan biyar, yayin da wasu miliyan 7.2 suka rasa muhallansu sakamakon rikicin.
Masudi Radjabo Papy, dan kasar Kongo daga yankin gabashi mai fama da rikici, ya koka kan yadda kasarsa ba ta taba samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ba, sakamakon fafutukar da kungiyoyin 'yan tawaye masu dauke da makamai ke yi na cin gajiyar arzikinta.
"Dalilin yakin gabashin DRC shi ne yadda ake hakar albarkatun kasa ba bisa ka'ida ba," kamar yadda Papy ya shaida wa TRT Afrika.
"Ana kashe mutane da dama ba tare da haƙƙinsu ba," in ji Papy
"Wannan shi ya sa nake ganin lokaci ya yi da shugabannin Afirka suka yanke shawarar kare muradun Afirka.
"Da mun kasance masu kula da juna da ba za mu samu wadannan yake-yake na cikin gida ba, musamman a DRC."
Abin da ya gani a cikin shekaru goma da suka gabata ya tabbatar masa da irin tabarbarewar harkar kasuwanci da cin zarafin al’ummarsa da kasarsa.
"Wannan shi ya sa nake ganin lokaci ya yi da shugabannin Afirka suka yanke shawarar kare muradun Afirka. Da mun kasance masu kula da juna da ba za mu samu wadannan yake-yake na cikin gida ba, musamman a DRC."
Abin da ya gani a cikin shekaru goma da suka gabata ya tabbatar masa da irin tabarbarewar harkar kasuwanci da cin zarafin al’ummarsa da kasarsa.
Abubuwa sun lalace
"Yadda lamarin yake shi ne (manyan kamfanonin ƙasashen Yamma) na zuwa DRC sanye da fuskar Afirka.
"Za su iya zuwa da fuskar Kenya ko Tanzania ko Rwanda. Idan suka zo DRC, mu 'yan ƙsar Kongo muna ganin kamar ɗan uwanmu ne ya zo, sai mu soma alaƙa da shi irin haka," kamar yadda Papy ya shaida wa TRT Afirka.
Ga talakawan Kongo, sha'awar ƙasashen waje ga ma'adinan ƙasarsu ya bar su da zalunci, fatara, har ma da mutuwa - mugun yanayin da ke tattare cikin mummunar kalmar "ma'adinan jini".
Bayan da ya je wuraren hakar ma'adanai da yawa, Papy ya ce 'yan uwansa da suke hako ma'adinan ba a ba su hakkin da ake bai wai bil'adama ba kuma ba sa samun wata fa'ida mai ma'ana daga aikinsu.
"Su ne waɗanda ke rayuwa a cikin yanayi na tsananin talauci, irin abin da ba za ku iya fara tunaninsa ba," in ji shi.
Ba mutanen ƙauye ba ne kawai ke karya bayansu a cikin ma’adinan ko kuma a fitar da su daga gidajensu don ba da hanya don hakar ma’adinai.
Papy ya ce "Idan aka yi komai daidai, Kongo za ta yi gogayya ne da tattalin arzikin China cikin sauri."
Albarkatu da ake sacewa
Masana tattalin arziƙi suna kallon Congo DR a matsayin mai matuƙar muhimanci a fagen haɓakar tattalin arziƙin fasaha, duk da ba ta kangaba a fagen fasahar duniya.
Ga misali, kashi 80% na ma'adanin cobalt na duniya, wanda babban sinadari ne wajen ƙera motocin lantarki, daga Congo Dr aka samo shi. Azurfa, zinare, lithium da ƙarin muhimman ƙarafa da ma'adanai suna cikin ragowar jerin.
"Idan da muna sarrafa duka waɗannan ma'adanai a nan Congo, za ka yi mamakin cigaban da za mu samu a yau. Me ya sa ƙasashen Afirka ba sa haɗa kai su zuba jari a harkar ma'adanai?" cewar Papy.
Maimakon haka, masu zuba jari daga kasashen waje da ke zuwa da kowace irin manufa wajen samun ma'adanan su ke cin karensu a wuraren haƙar ma'adanan Congo.
Ma'adinan da aka sace
Masana tattalin arziki sun yi la'akari da cewa DRC na da muhimmanci a tattalin arziƙin ƙasashen da suka mayar da hankali kan fasaha ba tare da cin gajiyar wannan hakan ba.
Misali, kashi 80% na cobalt na duniya, muhimmin bangaren kera motocin lantarki, daga DRC ne. Azurfa, zinare, lithium da sauran karafa masu daraja da ma'adanai sun ƙunshi ragowar jerin.
Papy ya yi imanin cewa nahiyar Afirka ta gaza wajen kafa matakan tattalin ma'adanai kamar yadda ƙasashen Yamma suka yi, "saboda an rarraba mu zuwa ƙananan ƙasashe".
Zama mai haƙar ma'adanai na mai ƙaramin ƙarfi, shi da ɗaruruwan wasu ƙananan kamfanoni an kawar da su daga kasuwar duniya, inda ake samu tarin riba.
Cibiyoyin ƙasashen waje masu biliyoyin daloli na zuba jari suna da arziƙin sayan ƙasa, kayan aiki, da ma'aikata da ke iya aiki ba dare ba rana.
Don fahimtar haka, mai haƙar ma'adanai na mai ƙaramin ƙarfi zai iya sayan kilo ɗaya na kuza daga "masu haƙa a daji" kan dalar Amurka $12. Kamfanonin ƙasashen waje ne za su saye shi daga wajensu a farashin da bai wuce dala $17 duk kilo ba, har da haraji.
Lokacin da kuzan ya isa kasuwar duniya, za a sayar a farashi ninkin wancanm.
Papy ya ce, "Lamarin tamkar na cocoa ne daga Cote d'Ivoire ko Ghana. 'Yan Afirka ba sa morar arziƙin ma'adanansu".
Guzuren tuffa
Idan an koma Turai, kamfanin Apple ya doge cewa ba ta samo ma'adanai asali kai-tsaye.
Kamfanin ya yi iƙirarin cewa yana budawa a-kai-a-kai kan masu kawo muss kaya, inda yakan wallafa rahoton bincike kan bayyana gaskiya, sanna yana ba da kuɗi ga cibiyoyin da ke aikin kyautata tsarin iya gano inda ma'adani ya fito.
Rahoton Apple na 2023 da ya gabatarwa hukumar kula da hannun jari ta Amurka, ya ambaci cewa babu ɗaya cikin masu kawo mata manyan sinadarai uku da aka tace, ko zinare, wanda yake ɗaukar nauyi ko amfanar da ƙungiyoyi masu makamai a Congo ko ƙasashe maƙwabta.
Bayan Congo DR ta shigar da ƙararraki a wannan watan, Apple ya saki wata sanarwar barranta.
Kamfanin ya ce, "Yayin da rikici a yankin ke ta'azzara a farkon shekarar nan, mun ankarar da masu kawo mana kaya da masu musu aikin sarrafawa da su dakatar da samo kuza, tantalum, tungsten, da zinare daga Congo DR da Rwanda".
"Mun ɗauki wannan matakin ne saboda mun damu da haɗarin cewa ba ya yiwuwa masu bincike na zaman kansu ko tsarin tantancewa na masana'antu ya aiwatar da binciken da ake buƙata don cim ma sharuɗanmu masu inganci."
Sanarwar ba ta fayyace lokacin da aka sanar da waɗannan masu samar da kaya ba.
Reuters ya ambato lauyoyin Congo na cewa, "Sanarwar Apple game da canje-canje kan tsarin sayan kayanta, sai an tabbatar da ita a ƙasa, an kuma auna ƙididdigar da za ta goyi bayan hakan".
Sun ƙara da cewa za su matsa lamba kan ƙarar da aka shigar a Paris da Belgium kan Apple France, Apple Retail France da Apple Retail Belgium.
Wannan ya haɗa da rufa-rufa kan laifukan yaƙi da safarar ma'adanai, da kayan sata, da aika ayyukan cinikayya na yaudara don tabatarwa masu sayan kaya cewa hanyar samo kayan tsarkakakkiya ce.
Cewar lauyan Congo a Belgium Christophe Marchand, ƙasarsa tana da alhakin ɗaukar mataki saboda wawashe arziƙin Congo da ya fara lokacin mulkin mallaka da sarki Leopold II na Belgium ya yi a karni na 19.
Ya ce "Yana da muhimmanci kan Belgium ta taimaki Congo a ƙoƙarinta na amfani da shari'a wajen kawo ƙarshen satar".
Robert Amsterdam, wani launan Congo DR mazaunin Amurka, ya ce ƙorafi kan Faransa da Belgium su ne na farko da ƙasar Congo ta yi kan wani babban kamfanin fasaha, inda ya ayyana su a matsayin "harin farko".