Petrouchka Thierry: Uwar masu fama da naƙasa ta Gabon

Tausayi yawanci yakan samo asali ne daga abubuwan da mutum ya taɓa fuskanta a rayuwa, kamar dai yadda ya faru da Petrouchka Thierry Moupaya Ossiga tun tana ƙuruciyarta.

A matsayinta na yayar wanda ke fama da cutar galahanga wato "autism" da Turanci, matashiyar 'yar ƙasar Gabon ta san irin matsaloli da faɗi tashin da masu lalurar da ta shafi ciwon taɓin hankali ke fama da su, da ma fafutukar da ake yi wajen ganin al'umma sun rungumi mutane masu fama da naƙasa.

"Yanzu ya cika shekara 20 da haihuwa," in ji Petrouchka da take magana a kan ƙaninta. "Ba ya iya yi wa kansa komai yadda ya dace. Don haka sai na fara tuntuɓarsa don jin halin da yake ciki a gida. Hakan ne kuma ya sa na fara fafutukata," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Petrouchka, wadda a yanzu mai fafutukar inganta rayuwar masu fama da nakasa ce da take zaune a birnin Libreville, ta ga abubuwa da yawa daga mutane daban-daban na wahalhalun da suke sha sakamakon naƙasa.

A matsayinta na 'yar shekara 24, "Uwar naƙasassun" tana sadaukar da lokacinta sosai wajen taimakon masu buƙata ta musamman.

Yayin da wadanda suka dangwali romon alherin Petrouchka za su yi la'akari da kansu a matsayin masu sa'a, yawancin mutum biliyan 1.3 masu fama da nakasa a duniya ba sa samun tallafin da suke bukata daga iyalansu ko al'ummarsu.

Yaƙi da ƙyama

Ana kallon ƙyama a matsayin babban shingen da dole ne mutanen da ke da nakasa su shawo kanta.

Haka nan suna fuskantar wasu nau'ukan wariya da suka hada da ƙin yarda da kuma yin watsi da su.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), rashin samun bayanai game da nakasa da kuma rashin tallafin zamantakewa ga wadanda ke kula da yara masu nakasa su ne sauran abubuwan da ke tattare da hadari.

Al'adar keɓe wa yara masu nakasa a matsugunai daban ma yana sa su kasance cikin haɗari da haɗarin fuskantar tashin hankali.

A Libreville, Petrouchka tana yaƙi a kullum don hana irin tsarin da al'umma ta mayar da shi al'ada wadanda hukumar WHO ta lissafa a matsayin abubuwa marasa kyau.

Petrouchka ta shafe shekaru tana tallafa wa mutane masu fama da cutar galahanga, tun daga taimakon yadda za su tafiyar da rayuwarsu har zuwa kan taimakon kudi.

Daga cikin kudaden da take samu daga kasuwancinta, matashiyar tana kashe kudade don biyan bukatu masu muhimmanci na mutanen da take taimako.

Wasu lokutan takan kaddamar da kamfe na tara kudi a kafafen sada zumunta don daukar nauyin muhimman ayyukan da take yi.

Yawanci yaran da take kula da su sun fito ne daga cikin iyalan da ba su da karfi, da ba za su iya daukar dawainiyar yara masu bukata ta musamman ba.

"A duk lokacin da na bukaci taimako, na kan yi fada da mutanen da ke gefena. Wasu suna ba da gudunmawar CFA 2,000 (US $ 0.32) ko ƙasa da haka, amma duk suna amfani. Duk abin da muka samu muna amfani da shi don masu buƙatar taimako," ta gaya wa TRT Afrika.

Taimokon ɗan'adam

Yawanci Petrouchka tana fara tuntubar wanda ke famada nakasa ne ta hanyar kafofin watsa labarai daban-daban. Wani lokaci kuma kai tsaye ake zuwa wajenta.

"Uwar Nakasassu" ta Libreville ko da yaushe tana nan don ba da taimako - inda za ka ganta ko ta yi rakiya ziyara zuwa asibiti ko yi wa yara masu nakasa wanka k, ciyar da su.

"Ina amfani da shafukan sada zumunta wajen wayar da kan wadanda ke kin yara masu nakasa da kuma watsi da su. Irin wannan yaro na farko da na yi kokarin kula da shi, ba ya ga dan'uwana, ya mutu ne sakamakon watsi da shi da mahaifiyarsa ta yi," in ji ta.

"Zan yi duk abin da zan iya don tabbatar da cewa irin wannan abu ba zai sake faruwa a kusa da ni ba."

Ko da yake yanayin ɗan'uwanta ɗan shekara 20 ya yi tasiri a kan manufofinta na zamantakewa, Petrouchka ta yi imanin cewa ba wannan kaɗai ba ne ya sa ta zama mai taimakon ɗan'adam da hidimar mutane babu gajiya.

"Ba kowane yaro da ke da ɗa galahanga ba ne ke iya aikin sa-kai kamar ni," ta gaya wa TRT Afrika.

Labari mai sa ƙarin gwiwa

Idan aka waiwayi baya, Petrouchka ta dauki sadaukarwar Édith Lucie Bongo, tsohuwar uwargidan shugaban Gabon, a matsayin abin kwaikwayonta.

Kafin ta mutu a shekara ta 2009, Édith ta ƙirƙiri Gidauniyar Horizons Nouveaux a 1996, wadda ta ƙware wajen taimaka wa yara masu nakasa da marasa galihu, da marayu.

Petrouchka ta taimaka kusan iyalai 50 zuwa yau, yawancinsu suna babban birnin Gabon.

Mutane da yawa suna mamakin yadda, a shekarunta, Petrouchka take da kulawa da mai haƙuri, da kuma sadaukarwa. Ta yaba wa danginta, musamman iyayenta, wadanda suke kara mata kwarin gwiwa akai-akai.

TRT Afrika