Daga Firmain Eric Mbadinga
A matsayinsa na dan kasuwa, Darhyl Nkogho yana ta fafutikar nemo hanyoyin kasuwanci ne a wuraren da wasu suke ganin kamar ba zai yiwu ba. Ya yi karatu ne a fannin kididdiga, wanda hakan ya taimaka masa wajen wuce sa’a, tare da hangen nesa da tsara yadda harkokin kasuwancinsa za su cigaba.
A kasarsa ta Gabon, Nkogho ya kawo sauyi a kan yadda mutane suke kallon harkokin kasuwanci.
“Muna so ne mu karfafa gwiwar ’yan kasuwarmu na Gabon domin su rika gogayya da takwarorinsu na duniya a fagen kanana da matsakaitan kasuwanci, wanda muke tunanin hakan zai rage yawan rashin aikin yi a kasarmu,” inji Nkogho, wanda yake tallafa shirin “Un Gabonais=Une Boutique".
Shirin ya zo ne a daidai lokacin da rashin aikin yi, ya yi katutu a tsakanin matasan kasar, ga kuma tsadar rayuwa a kasar ta Gabon wadda yawanci baki ne suke rike da manyan ayyukan albashi a cikinta.
Bambanci mai yawa
Ko a birnin Libreville ko Franceville ko Lambaréné, sai a kwanan ne bangarori kamar kamun kifi, da sufuri da sauransu suka fara samun shigowar ’yan kasuwa ’yan asalin kasar ana damawa da su. Amma duk da haka, har yanzu ba su da yawa a ciki, idan aka kwatanta da baki.
Rashin aikin yi, musamman a tsakanin matasa a kasar yanzu haka ya kai kashi 38 a kasar da mutanenta suka karuwa da tsakanin miliyan 1 zuwa 2 a shekara 20 da suka gabata.
La’akari da sakamakon wani bincike da aka yi a 2021, shirin na “Un Gabonais=Une Boutique” yana koyar da yadda za a samu yanayin kasuwanci mai kyau tsakanin manya da kananan ’yan kasuwa karkashin jagorancin shi Nkogho din.
Matashin mai shekara 30 ya ce akwai bukatar samar da fahimtar juna da hadaka a yanayin kasuwancin kasar.
Misali, idan karfe 2:30 na rana ya yi a ranar Juma’a, harkokin kasuwanci a Gabon suna tsayawa saboda Musulmi suna tafiya Masallacin Juma’a. kasancewar yawancin masu kananan kasuwancin Musulmi ne, sai ya kasance an kulle shaguna da dama a wannan lokacin.
“Wasu lokutan a kan shiga damuwa, musamman idan ana bukatar wasu abubuwan cikin gaggawa,” inji wata ’yar kasar mai suna Jessica Eyang a tattaunawarta da TRT Afrika.
“Akwai watarana da nake so zan tura wa wani dan uwa kudi a ranar Juma’a, sai da na sha wahala kafin na samu shagon tura kudin. Sai na da jira daga karfe 1 zuwa karfe 3 na rana kafin na tura kudin.”
Neman hadin kai
A shekarar 2019, a wani rahoto mai taken, “Kawo sauyi, samar da ayyukan yi da gyara al’umma,” Hukumar Tattalin Arzikin Afrika na Majalisar Dinkin Duniya ta yi binciken kwa-kwaf a game da yanayin rayuwa da tattalin arzikin kasar Gabon.
A bayanin kammalawar binciken, hukumar ta yi kira da a bunkasa harkokin kasuwanci da harkokin cibiyoyin hada-hadar kudi a kasar. Ta kuma yi kira da a tallafa wa kananan ’yan kasuwa, sannan kasar ta dage wajen samar da wasu hanyoyin samun kudin shiga da dama.
Nkogho ya fito da karfinsa yana ta kokarin ganin alaka mai kyau ta kulla tsakanin masu saya da masu sayarwa a kasar, inda yake da burin ganin ba a samu yankewar kayayyakin da mutane suke bukata ba a kowane lokaci, a kowace rana.
“Tattaunawa na da muhimmanci. Ita ce za ta samar da fahimta tsakanin masu saya da sayarwa da kuma rage yawan dillalai, wanda hakan zai rage farashin kayayyakin,” inji shi.
Zuwa yanzu, shirin na Un Gabonais=Une ya samu nasarar assasa shagunan abinci da dama a kasar. Kowane shago yana samar da ribar akalla CFA 300,000 wato Dalar Amurka 487 duk wata.
Masu kula da shagunan, ciki har da mata da masu sha’awar fara kasuwanci suna halartar tarukan karawa juna sani a zahiri da kuma ta intanet, inda suke tattaunawa a tsakaninsu a kan hanyoyin inganta kasuwancinsu.
A farkon watan Maris, shirin ya tara akalla matasa 400 a birnin Libreville domin horar da su hanyoyin kasuwancin kayayyakin abinci.
Masanin tattalin arziki dan asalin kasar Gabon, mazaunin Canada, Jean-Louis M'Badinga ya bayyana aikin Nkogho a matsayin, “aikin da ke karfafa matasa. Kokarin da yake yi zai taimaka wajen rage rashin aikin yi a tsakanin matasa, da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar matukar an ba shi goyon bayan da yake bukata,” inji shi a tattaunawarsa da TRT Afrika.
Matsaloli
M'Badinga ya ce babbar matsalar da ke gaban ’yan kasuwar kasar ita ce rashin jari.
“Mutanen Gabon suna fuskantar matsala wajen samun tallafin jarin da suke bukata domin bunkasa kasuwancinsu, wanda haken ke dakushe kasuwancin, wadanda su ne ya kamata su bunkasa tattalin arzikin kasar.”
“Abin da ake bukata yanzu shi ne canja tunanin mutanen kasar, ta yadda direban tasi da mai tsaron shago da mai sayar da kifi da mahauci za su daina daukarsu sana’arsu a matsayin mara daraja. Idan gwamnati ta taimaka musu wajen iganta harkokinsu, mutane za su fara daukar sana’o’insu da daraja.”
A bangaren tallafin da gwamnati za ta iya bayarwa, masanin tattalin arziki M'Badinga ya ce kananan ’yan kasuwa suna fama da matsaloil masu yawan gaske.
“Idan ana so su cigaba da gudanar da harkokinsu, dole gwamnati ta tallafa wa kananan ’yan kasuwar nan tare da bunkasa wasu hanyoyin samar da kudin ta hanyar bunkasa wasu bangarori irin su bangarorin harkokin kudi, da yawon bude ido,” inji shi.
Duk da cewa Nkogho yana da burin samun tallafin gwamnati a nan gaba, a yanzu dai ya shagalta ne da tallata aikinsa, wanda da yake da burin ganin ya yadu a fadin kasar baki daya ta hanyar amfani da kafofin sadarwa na zamani.