Daga Firmain Eric Mbadinga
Rodolphe Eva Ndong Ovono ya yi waiwaye zuwa shekarar 2018 a matsayin shekarar da ta sauya masa rayuwarsa.
Rodolphe ya rasa mahaifinsa, Simon, sai dai irin dawainiyar kula da shi da ya yi a lokacin da mahaifin nasa yake fama da rashin lafiya abu ne da ba zai taba mantawa da shi ba.
"Darasin da na dauka daga rashin lafiyar mahaifina, ban ma san yadda zan kwatanta muku ba," kamar yadda matashin 'dan asalin Gabon mai shekaru 45 ya shaida wa TRT Afrika.
"Mutane su kan zama masu rauni bayan shekarunsu ya ja. Kuma a wannan lokacin ne suka fi bukatar a nuna musu soyayya da kulawa.
"A gare ni, bayan na shafe shekara guda tare da mahaifina, hakan ya kara karfafa dangantakarmu saboda ya samu kulawa da soyayya."
Samar da shirin Akiky Care
Rodolphe ya samar da kamfanin Ayiky Care, shirin da ke tallafa wa tsofaffi a Libreville, bayan da ya fahimci cewa babu cibiyoyin da suka kware wajen kula da tsofaffi a fadin nahiyar Afirka.
A kasashen Afirka da dama, musamman ma birane, kula da tsofaffi ya zama babban kalubale da a wani lokacin ya kan zama tashin hankali da masaifa a wannan zamani.
Rahotanni kan tsofaffi da ke mutuwa sakamakon rashin issashen kulawa ta lafiyar kwakwalwa da na sauran sassan jiki suka dada yawa.
"Rashin samun goyon bayan al'umma da talauci da cin zarafi daga yan'uwa na jiki na na daga cikin abubuwan da ke yawan shafar lafiyar tsofaffi, bincike ya tabbatar da cewa mutanen da shekarunsu ya ja suna fuskantar ire-iren nau'ikan cin zarafi ciki har da tashin hankali da rashin kulawa da watsi da rashin girmamawa,'' a cewar hukumar lafiya ta Duniya WHO.
A Gabon, cibiyar kula da lafiyar tsofaffi daya tilo da ake shi yana Asibitin Melen a Libreville, kuma cibiyar na aikin kula da dattijai da aka kawo su bisa ga aminciwar yan'uwansu ko kuma suka kai kansu ko bisa ga shawarar likita.
Ga wadanda ba sa son a kai su wannan wuri mai kamar gida bayan ritayarsu, Ayiky Care yana samar da madadi hakan.
Shirin kamfanin na samar da kulawa ga tsofaffin wadanda 'ya'yansu suka shagaltu a wajen ayyukansu da kuma wadanda suke zama su kadai kuma ba sa son zama a cibiyar da aka ware don kula da su wadda ke hada da asibiti.
Selly Ba wata masaniya kan zamantakewa 'dan Senegal ya yi hasashen samun karin adadin tsofaffi wadanda ke bukatar kulawa ta mussaman cikin 'yan shekaru masu zuwa.
''A halin yanzu tsofaffi na wakiltar kashi 5 cikin 100 na al'ummar Afirka, ana sa ran adadin zai karu zuwa kashi 9 cikin 100 nan da shekara ta 2050. Wannan karin zai kara yawan bukatun samar da kariya da kiwon lafiya a tsakanin tsofaffi,'' kamar yadda ta shaida wa TRT Afirka.
''Yana da muhimmaci tun daga yanzu a yi nazari kan matakai da hanyoyin da za a bi wajen tallafa musu.''
Nauyin da ya rataya kan iyali
A al'adun Afirka akan daura hakkin kula da tsofaffin kan iyalansu, Amma kamar yadda Selly ta bayyana iyalai da dama kan gaza daukar wannan nauyi saboda matsalar matsin tatallin arziki ko kuma rabuwa a tsakanin iyali.
Hakan ya sa wasu kasashe a nahiyar samar da manufofi samar da kariya da kuma tsarin Fansho, amma ana bukatar a kara azama a kai.
Masana sun yi imanin cewa samar da tsarin shiri kamar na Ayiky Care shine mafita.
Ayiky Care yana daukar kwararrun ma'aikatan lafiya wadanda suka daina aiki a cibiyoyin gwamanti.
Kazalika kamafanin Rodolphe ya hada gwiwa da asibitocin gwamnati da masu zaman kansu a Gabon inda suke aikin samar da kulawa ga tsofaffi har gida.
Daga ciki har da ma'aikata wadanda aka horar da su wajen ba da kulawa na tsawon wasu sa'o'i da aka gayyade ko kuma su zauna tare da marasa lafiya a kowane lokaci, bisa ga tsarin da suka zaba.
Abin da ya sa labarin Ayiky Care ya fita daban shine yadda Rodolphe ya kafa shirin ta hanyar amfani da asusun ajiyarsa.
“Ina da wasu kudade da aka bani a matsayin sallama bayan korata da aka yi ba bisa ka'ida ba daga wani babban kamfanin hakar ma’adinai na manganese, inda na yi aiki a matsayin mai aikin fassara na tsawon shekara guda,” in ji shi.
"Gabannin farawarmu, don dole na rufe Ayiky Care na tsawon shekara biyu saboda bulla cutar Korona. Tun daga lokacin zuwa yanzu dai mun ba da tallafin jinya ga tsoffi akalla 35 a yankin."
Daga cikin iyalan da suka ci moriyar ayyukan Ayiky Care har da Yannick Essono Lee, da ke zaune a babban birnin Gabon.
Yayin da suke fama da ayyukansu na yau da kullun, shi da matarsa sun tuntubi kamfanin Rodolphe bayan kaddamar da shirin don kula da mahaifiyarsa da ke fama da rashin lafiya.
"Na gano shirin ne a wurin wani taron kuma na ga ya gamsar da ni. A mafi yawan lokuta akwai matukar wuya wajen kula da tsofaffi yayin da mutum ke aiki.
Akwai tsare-tsare na musamman a Turai da ke samar da irin wannan sauki, amma ana mafi akasari yanayin da sarkarkiya," in ji Yannick.
"Don haka, lokacin da mahaifiyata ta kamu da rashin lafiya, na tuntube su, ban kuma yi da na sani ba. Ana samun ma'aikatan dake aiki da safe da yamma ako da yaushe cikin mutuntaka da jin kai,''
Mahaifiyar Yannick ta murmure bayan zama na wasu lokuta da ta yi a cibiyar kana ta koma gida cikin iyalinta.
A cewar Dr Louis Niamba, wani mai bincike kan al’amuran al’umma daga Burkina Faso, ''cudanyar zamantakewa na da matukar muhimmaci a rayuwa da lafiyar kwakwalwa da gangan jikin duk wani rukunin mutane masu rauni ciki har da tsofaffi”.
Rodolphe yana fatan bude gidan kula da tsoffi wadanda suka yi ritaya irinsa na farko a Gabon wata rana tare da fadada ayyukan kamfaninsa zuwa sauran kasashen Afirka.