Taken da ake yi wa tsohuwar shugabar ƙasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf na “Mace mai kamar maza” ya matuƙar dacewa da ita.
A matsayinta na wacce ta fara zama shugabar ƙasa mace ta farko a nahiyar Afirka, zamnata shugabar ƙsa bai zo da mamaki ba saboda aƙidun da aka san ta da su na ƙoƙarin ganin mace ta kai duk wani mataki da namiji ka iya kai wam musamman a yankin da maza suka mamaye duk wasu madafun iko.
“Da zarar an kai matakin karya aƙidar da aka saba da ita, to ba za a taɓa iya komaw abaya ba duk irin ƙoƙrin yin hakan,” kamar yadda Sirleaf ta taba faɗa shekara biyar da suka wuce a lokacin wani taro na TED inda ta yi magana a kan “Yadda mata za su iya jagorantarmu zuwa ‘yanci da adalci da zaman lafiya”.
Ƙarfin da ta yi amfani da shi wajen jaddada waɗannan kalamai sun yi matuƙar jan hankali da ba da ƙwarin gwiwa ga matan da suka halarci taron waɗanda yawancinsu matasa ne.
Ellen, wadda ta taɓa cin Kyautar Zaman Lafiya ta Nobel, ta kuma yi shugabancin ƙasar Laberiya daga shekarar 2006 zuwa 2018, ba jawabi kawai ta yi a kan batun “duk abin da namiji zai iya, mace ma za ta iya” ba.
Tana isar da saƙo ne kan batun da ba a faye mayar da hankali a kansa ba na shigar mata sha’anin shugabanci.
Taken da ake yi wa tsohuwar shugabar ƙasar Laberiya Ellen Johnson Sirleaf na “Mace mai kamar maza” ya matuƙar dacewa da ita.
Lokacin tsinkaye
A cikin shekaru goma da suka gabata, kalubalen zamantakewa da siyasa da tattalin arziki na Afirka da alama sun ƙaru musamman a kan mata na neman su kasance a sahun gaba wajen haifar da sauyi tare da karya al’adun da saka saba da su na dunƙufar da mata.
A tarihi, maza ne suka fi yin jagoranci da shugabanci a nahiyar Afirka, duk da cewa mata da dama ƙoƙarin kai wa ga ci, lamarin da ke nuna cewa ba wai kawai suna hawa matsayi na jagoranci ba amma sau da yawa suna da matsayi na musamman wajen kawo sauyi mai ma'ana.
Sauyi ne na tsari wanda Sirleaf ba wai kawai ke wakilta ba amma kuma tana la'akari da ɗaukar alhakin yada shi.
"Ni ce mace ta farko da ta zama shugabar wata al'ummar Afirka, kuma na yi imanin cewa ya kamata kasashe da yawa su gwada hakan," in ji Sirleaf a cikin jawabin bude taron na TED a Disamban 2019, inda ta jefa wannan kalubale ga sauran kasashen nahiyar.
A lokacin, ba shakka, Afirka ta riga ta samu ƙwararrun mata da yawa waɗanda suke yin abubuwa masu kyau da ke fitar da shahararsu.
Joyce Hilda Banda ta rike mukamin shugabar kasar Malawi daga watan Afrilun 2012 zuwa Mayu 2014, bayan da ta ɗare kujerar mulki bayan mutuwar wanda ta gada Bingu wa Mutharika.
A kasar Mauritius, Dr Bibi Ameenah Firdaus Gurib-Fakim ta kasance shugabar kasar daga watan Yunin 2015 zuwa Maris 2018, yayin da Saara Kuugongelwa-Amadhila, wacce ta zama Firaministan Namibiya a shekarar 2015, ta ci gaba da rike mukamin.
Tun watan Maris din 2021, Samia Suluhu ta zama Shugabar Kasar Tanzania, inda ta hau kujera mafi girman ƙalubale bayan mutuwar Shugaba John Magufuli. Ta kasance mataimakiyar Shugabar Kasar tun daga 2015 zuwa 2021.
A can ƙasar Namibiya ma, a kwanan baya ne Netumbo Nandi-Ndaitwah ta zama mataimakiyar shugabar kasa bayan da ta samu kashi 57 cikin 100 na yawan ƙuri’un da aka kaɗa a zaɓen ƙasar.
Karya aƙidun al’adu
A yayin da ake samun ƙaruwar matan da ke yin nasara wajen shiga madafun iko a Afirka, akwai wata ƙasa ɗaya da ta yi zarra a wani abu.
Kasar Rwanda, wadda sau da yawa ake kambama manufofinta na ci gaba, ita ce ke da mafi yawan mata a majalisar dokoki a duniya. Kasar ta Gabashin Afirka, wadda kashi 61.3% cikin 100 na ‘yan majalisarta mata ne ta zama abar koyi wajen shigar da mata harkoki da kuma daidaito.
To amma a nahiya mai kasashe 54, me ya sa da wahala a samu ƙsashe da dama da mata ke jagoranta?
Wata aƙidar ita ce a al’umma ta masu ra’ayin riƙau, mata sun fi so su ga maza na jagoranci maimakon maza, ko da kuwa matan za su iya.
Har yanzu akwai al’ummomin da ba su yarda mata su yi shugabanci ba a Afirka.
Duk da cewa ana ɗan samun sauyi a irin wannan lamari, har yanzu mafi yawa ba su yarda da mace ta shugabanci al’umma ba.
“Mutane na cewa mata ba sa tsayawa takara. Amma duk yadda muka yi ƙoƙarin da muka yi don mu kai ga ci, mutane sun fi son su zaɓi maza,” Anne Waithera, in ji wata mai son zama ‘yar majalisa a Kenya.
Sau biyu tana tsayawa takara ba ta samu.
“Sau da yawa nakan ji cewa mata ‘yan’uwanmu ma ba sa goya mana baya saboda ba su faye son zaɓarmu ba,” Waithera ta koka.
Wata aƙidar ita ce a al’umma ta masu ra’ayin riƙau, mata sun fi so su ga maza na jagoranci maimakon maza, ko da kuwa matan za su iya.
Wani bincike na Mujallar Forbes a 2023 ya nuna cewa mata sun fi iya yin kyakkyawan shugabanci.
"A karon farko a tarihi, shugabannin kamfanoni mata suna jagorantar kusan kashi 10% na kamfanoni na Fortune 500. Babu shakka wannan wani muhimmin ci gaba ne. Amma kuma yana nuna bukatar karin mata a kowane mataki na jagoranci," in ji binciken.
Kuma wannan ba batun wakilci bane kawai. Shugabannin mata suna da kyau ga kasuwanci.
Mata a sauran fannoni
A cikin gwagwarmayar tabbatar da adalci a zamantakewa da muhalli, matan Afirka sun tabbatar da bajinta a jagoranci.
Akashinga Rangers na Zimbabwe, wata ƙungiyar mata mai adawa da farauta, suna kare namun daji da kuma kawo sauyi ga al'umma ta hanyar karfafawa.
A harkokin kasuwanci kuwa, mutane irin su Ngozi Okonjo-Iweala 'yar Nijeriya, wadda ke rike da mukamin babbar daraktar Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya, sun nuna irin karfin da mata ke da shi wajen jagorancin tattalin arzikin duniya.
Akashinga Rangers na Zimbabwe, wata ƙungiyar mata mai adawa da farauta, suna kare namun daji da kuma kawo sauyi ga al'umma ta hanyar karfafawa.
Matan Afirka da ba su da yawa suna jagorantar ayyukan kiwon lafiya DA ilimi, da kawar da fatara.
Wadannan mata sun tabbatar da cewa shugabanci bai tsaya ga manyan ofisoshi ba kawai, yana tasiri har ma a tsakiyar al'ummomi.
Yayin da ake shigar da yara mata da yawa makaranta a fadin Afirka kuma aka ba su dama da kuma muryar da za a ji, mata na samun kudurin tashi tsaye don nuna bajinta.
Wata tsohuwar karin maganar na cewa- "A bayan kowane namiji mai nasara, akwai mace" – wataƙila a yanzu ba ta da tasiri sosai, sai dai idan har za a ci gaba da yaba wa mata masu goyon bayan mazaje, to su ma za su iya shiga sahun gaba a kowane lamari.