Daga Abdulwasiu Hassan
Tattalin arziki da kasuwancin halal na duniya ya samo asali ne daga dokokin Musulunci, ya taso a matsayin mai kawo sauyi a kasuwancin kasashen Afirka da ke da sama da mutum biliyan guda, kuma zai taimaka wa matasansu.
Kasancewar yanki mai matasa mafi yawa a duniya - da matsakaicin shekaru na 18 - kasashen Afirka sun fara himmatuwa wajen ganin sun tanadi dukkan kayan aiki.
Kungiyar 'ISS African Futures' da ke hasashe game da makomar nahiyar da cigabanta, ta ce akwai kashi 43 na 'yan Afirka da ke kasa da shekaru 15, sannan 'yan kasa da shekaru 30 kuma sun kai kashi 28 na yawan jama'ar.
Duk da wannan dama, rashin ayyukan yi na damun nahiyar, inda ke jefa matasa da dama cikin hatsarin aikata muggan laifuka da yin gudun hijira mai hatsari da halakar da su a yayin kokarin tsallaka tekun Bahar Rum don neman damarmaki masu tsoka.
Ga yankin da ke da dimbin arzikin albarkatun kasa, kwararru na takaicin ganin yadda ake ta kokawar gudun hijira.
Dr Yahaya Yakubu, malami a sashen tattalin arziki a Jami'ar Za'adu Zungur, Gadau, tsohuwar Jami'ar Jihar Bauchi, na da ra'ayin cewa kawai lokaci ake jira na kasashen Afirka su ribaci hanyoyin habaka da kusan suke boye a sarari.
"Kasuwancin kayayyakin halal na bunkasa cikin hanzari a duniya, hakan na zuwa ne saboda bukatar d aake nuna wa ta kayayyakin da suke halal a tsakanin masu sayayya Musulmai da ma wadanda ba Musulmai ba.
Ya zuwa 2024, ana kiyasta darajar kasuwar kan dala tiriliyan 2.7," Dr Yakubu ya fada wa TRT Afrika.
Tsarin fannoni da yawa
Halal, kalmar Larabci da ke nufin "abin da aka yarda a yi" duba ga dokokin Musulunci.
Ya shafi dukkan wasu al'amura na sha'anin kudi, yawon bude ido, da ma sutura, ba wai iya kan abinci batun halal ya tsaya ba.
"Halal na karfafa aiki da dokoki, aiki da gaskiya bisa doron shari'a," in ji Dr Yakubu.
Isa Ali Pantami, wanda tsohon ministan tattali arzikin fasahar zamani ne a Nijeriya daga 2019 har zuwa watan Mayun 2023, ya ce kasashen da ba su da alaka da shari'ar Musulunci sun samu dama sama da kasashen Afirka wajen tallata kasuwancin halal.
"Idan ka yi duba na habakar kasuwancin halal, an yi hasashen cewa ana juya dala tiriliyan 7.7 a wannan fanni nan da 2025," in ji Pantami.
"Wannan kudi ne mai yawa. Bari mu takaice, Afirka na da yawan mutane biliyan 1.4 d akudaden shiga na cikin gida da ya kai dala tiriliyan 3.2."
Pantami, wanda ya halarci Taron Kayayakin Halal na Duniya a Istanbul, Turkiyya, ya bayar da misali da kasar Barazil wadda ba ta da alaka da da al'adar Halal amma kuma tana amfanida kasuwancin.
"Barazil ba kasar Musulmai ba ce, amma idan ana kwatanta jama'arta da na Nijeriya. Na samar da dala biliyan 23 daga kasuwancin kayayyakin halal," in ji Pantami.
A wajen taron na Istanbul, wanda Cibiyar Tabbatar da Inganci Tsakanin Gwamnatoci ta Kasashen Musulmi da hadin gwiwar Kungiyar Hadin KAn Kasashen Musulmi da ma Ma'aikatar cinikayya da Hukumar Tantance Kayayyakin Halal na Turkiyya, da yawan mahalarta sun yi magana ta gaskiya game da kasashen Afirka da ba sa aikata katabus a damarmakin da kasuwancin halal ke bayarwa.
Me za a iya yi
Domin amfana da damarmakin da ke tattare da kasuwancin halal, kwararru na cewa gwamnatoci da masu zuba jari a kasashe Afirka na bukatar zuba jari a tsare-taren dokoki, kayan more rayuwa, da kuma wayar da kan jama'a sosai.
Idan ka dauki Nijeriya, kasar na bukatar zuba jari sosai don cim ma burinta a matsayin ta na babbar mai taka rawa a kasuwancin halal.
"Hanyoyin sufuri, kayan sanyaya abinci, da dakon kayayyaki na bukatar habaka wa don tabbatar da za a samar da kayan halal tare da rarraba su cikin tsari a cikin ida da ma kasashen duniy," Dr Yakubu ya fada wa TRT Afrika.
Ya kuma kawo misali kan tallafin da gwamnatoci za su bayar na karfafa gwiwar masu zuba jari ta haaka hadin kai da kungiyoyin kasa da kasa da ke da alaka da kasuwancin kayayyakin halal.
"Wani bangare da ke da muhimmanci da kasar ke bukata na magance matsalar ta hanyar kara wayar da kan mutane a tsakanin masu samar da kaya da masu saye kan ingancin kayan halal," in ji Dr Yakubu.
Sakamakon da za a iya samu
Idan kasashen Afirka suka yi amfani da damar kasuwancin halal, kwararru sun ce za su amfana sosai.
"Idan Nijeriya ta samu yadda take so, misali, za ta iya samar da ayyuka 500,000 cikin shekaru biyar zuwa goma daga kasuwancin kayan halal," in Pantami.
"Za mu iya gogayya da Barazil sannan mu wuce ta a wannan lokaci saboda mun fi kusa da masu cin halal da kasuwancin halal a al'adance."
Lokaci ne kawai zai bayyana irin damarmakin da wannan yanki zai iya amfana daga kasuwancin halal.
Kwararru na da ra'ayin cewa za a iya fara wannan tafiya ta hanyar aminta da cewar matasan Afirka ba sa bukatar tafiya don neman wani arziki da su ma suna da shi a gida.