Panama Drugs / Photo: AP
A baya, Rufaro Machingura mashahuriyar ‘yar kwallon kafa ce a Zimbabwe,

kuma abar koyi gun yara masu tasowa. Ta shahara da lakabin “Super Striker”, wanda tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya rada mata.

Har a yau ita ce mace ‘yar kwallo da ta fi shahara a kasar, bayan ta kasance wadda ta ci kwallon da ya kai kungiyar kwallon kafa ta mata ta kasar, wato Mighty Warriors ta lashe Kofin Zakarun Kwallon Kafa na COSAFA a Afirka ta Kudu.

Sai dai ta rasu tana da shekara 31 kacal a watan da ya gabata, wato ‘yan shekaru kadan bayan ta amsa cewa tana fama da matsalar shan miyagun kwayoyi, wadda ita ce ta hana mata ci gaba da harkar wasanni, kuma a karshe ta lahanta lafiyarta.

Labarin Rufaro wani madubi ne kan yadda masifar shan kwaya ke addabar matasan wannan kasa.

Annobar shan sinadarai ba bisa ka’ida ba ta kazanta, kuma tana lalata rayuwar daidaikun mutane da ma danginsu. Hakan ne ya janyo yawaitar kiraye-kiraye kan a dauki tsauraran matakai kan masu sha da fataucin kwaya a cikin al’ummomin kasar.

Labarin sanannun mutane kamar Rufaro, da kuma mashahurin mawakin Hip Hop Tinasha Gonzara, sukan dauki hankalin jama’a jifa-jifa.

Amma fa dubban sauran mutane da matsalar kwaya ta shafa sukan kare ne kawai a matsayin alkaluman kididdiga da ke cikin rahotannin hukomomi.

Bincike ya ta’allaka annobar mu’amala da kwaya kan yawaitar rashin aikin yi, da kuma masu amfani da kasar wajen fataucin kwayoyi, irin su hodar ibilis zuwa wasu kasashen duniya.

Yakin da ba a samun nasara

Cikin shekarun da suka gabata, hukomomin tsaro sun kaddamar da shirye-shirye salo-salo don dakile wannan matsalar, wadanda suka hada da kai samame, da kafa shingayen bincike. Amma duk da haka abin ya ci tura.

A shekarar 2021, shugaban Zimbabwe Emerson Mnangagwa ya kafa kwamitin ministoci, wanda ya fito da tsarim Shirin Kasa kan Kwayoyi, tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025, wato ZCLDN.

Sai kuma Shirin Magancewa da Sauya Halayya kan Matsalar Shan Giya da Sinadarai a Zimbabwe. Sai dai ba a bayyana wa jama’a irin cigaba ko nasarorin da aka samu karkashin wannan shiri ba.

Duk da dai babu alkaluma daga gwamnati game da yaduwar miyagun kwayoyi a kasar, wani rahoto na Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, kan lafiyar kwakwalwa a tsakanin matasa a yankin Afirka, ya nuna cewa kasar ce ke da mafi yawan matasa ‘yan shekara 15-19 masu ta’ammuli da mummunar al’adar shaye-shaye.

Rahoton ya kara da cewa adadinsu ya kai kashi 70.7 cikin 100 tsakanin maza, da kuma kashi 55 cikin 100 tsakanin mata.

Kididdigar da Gamayyar Kungiyoyin Farar Hula da Masu Yaki da Kwaya na Zimbabwe suka tattara, ta bayyana cewa kashi 60 cikin 100 na wadanda ake kwantarwa a asibiti, saboda matsalar shan kwaya ne.

Kashi 80 cikin 100 daga cikinsu mutane ne masu shekara 16 zuwa 25, har da mata ‘yan makaranta.

“A matakin da ake kai yau, kashi 60 cikin 100 na marasa lafiya da aka kwantar a asibitin lura da kwakwalwa, suna fama da matsalar da ta danganci shan kwayoyi da sinadarai ba bisa ka’ida ba,” a cewar Donald Mujiri, mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiya da Kulawa da Yara ta kasar.

Jami’in Shirin ZCLDN, mai suna Knowledge Mpempe, ya yi imanin matsalar cin hanci da rashawa ne sanadin yaduwar ta’ammuli da kwaya.

Ya kara da cewa, “Shan kwayoyi da sinadarai ba bisa ka’ida ba, alama ce karara ta wata babbar matsala. Matsalar kuwa ita ce rashawa da masu fatauci da kawo kwayoyi.

“Don haka idan har muka dakile samar da kwayoyin, a bayyane yake cewa bukatar kwayar za ta kau.”

An sanya Zimbabwe a mataki na 157 cikin kasashe 180 a Jadawalin Bayyanar Rashawa, wanda wani rahoto ne na shekara-shekara da Kungiyar Transparency International take tattarawa.

Matattarar kwayoyi

Yayin da fataucin kwaya ya kasance ruwan dare a Zimbabwe, yawanci saboda iyakokin kasa marasa tsaro, kasashen Afirka ta Kudu da Zambiya da Mozambik sun zamo sabbin tushen samun miyagun kwayoyi, wadanda suka hada da “bronclear” (wani ruwan magani mai dauke da sinadarin kodin).

Akwai kuma “Moonshine” wanda aka fi sani da “tumbwa” ko “kozoda”, da crystal meth”, da manyan kwayoyi kamar “Diazepam, Ketamine, da Pethidine, da morphine da Fentanyl”.

Rahotannin gidajen jaridu na yankin sun nuna cewa cikin shekarun da suka gabata, an kama sama da mata 50 suna fataucin kwaya.

Rahoton Afirka ya bayyana cewa mata ‘yan Zimbabwe shida sun rasa rayukansu sakamakon hadiyar kwayoyi da suke hadiyewa a cikinsu a yayin safar domin kaucewa kamu su.

Baya ga kwayoyin da ake shigowa da su kasar, ‘yan kasar suna mamaye kasuwanni da sinadarai masu araha, kuma masu matukar bugarwa, kamar su “musombodiya”, wanda wani abin sha ne mara kala da ake yi da sinadarin “ethanol” ko garin burbushinsa, da aka sarrafa kuma ake yadawa yawanci a tashoshin bas da unguwannin marasa galihu.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan kwaya masu kananan shekaru sukan jika tsumman kashin yara da bilic cikin ruwan zafi, sai su shaki tururinsa don ya bugar da su.

“Mashaya kwaya sukan sha kowane irin abu da suke tunanin zai gusar musu da hankali ko ya bugar da su, wanda ya sa ake yawaitar samun masu buguwa ta hanyoyin da ba a saba gani ba,” a cewar Dr Johannes Marisa, shugaban Kungiyar Jami’an Lafiya da Kula da Hakora Mai Zaman Kanta” ta Zimbabwe.

Ya kara da cewa akwai bukatar samun karin cibiyoyin sauya tunani, saboda kasar na fama da yawaitar mashaya kwaya masu bukatar gyaran zuciya.

Ya kuma tabbatar da cewa, “Cibiyoyin sauya tunani masu kula da mashaya kwaya sun yi karanci sosai a kasarmu, kamfanoni masu zaman kansu za su taka muhimmiyar rawa wajen kafa irin wadannan cibiyoyin.”

A farkon watan nan, Hukumar ‘yan-sanda ta Zimbabwe ta kaddamar da wani shiri a fadin kasar mai suna, “Gujewa miyagun kwayoyi da sinadarai”.

Ya zuwa ranar 10 ga Fabrairu, shirin ya kama mutanen da ake zargi da sayarwa da masu ta’ammuli da kwaya har 1,903.

Ministan Harkokin Gida da Al’adu da Tarihi, Kazembe Kazembe ya ce hukomomi suna bibiyar wasu manya-manyan masu safarar kwaya.

Ya kara da cewa, “’Yan sanda ba sa kasa a gwiwa a wannan yaki kan miyagun kwayoyi. Muna yakar amfani da kwaya da sanadarai ba bisa ka’ida ba, kuma da gaske muke yi.

“Akwai ‘yan-sanda da ‘yan siyasa a cikin wadanda muke tuhuma, kuma za su fuskanci fushinmu.”

TRT Afrika