Asibitoci a El Fasher sun fuskanci hare-hare sau goma a kasa da watanni uku / Hoto: Getty Images

Daga Sylvia Chebet

Asibitoci a garin el-Fasher da ke yankin Arewacin Darfur na Sudan mai fama da rikici sun zama wajen da yakin da ake yi ya tarwatsa a baya-bayan nan a lokacinda aka sake tafka arangama tsakanin sojojin Sudan da mayakan RSF inda dukkan bangarorin ke take dokojin jin kai na kasa da kasa.

Harin 29 ga Yuli kan Asibitin Saudi, wanda Kungiyar Likitocin Komai Da Ruwanka ke kula da shi, shi ne hari na goma aka kai kan cibiyar lafiyar da ke kula da mutane miliyan 1.5 tun bayan fara kai hare-haren.

An kashe ma'aikatan lafiya uku a harin, an jikkata fararen hula 25, ciki har da wasu da aka tsugunar a wani masallaci d ake kusa da asibitin wand ashi ma harin ya same shi.

"Ba mu da tabbas din ko da gangan ake kai wa asibitoci hari, amma harin makon da ya gabata na nuni da maharan ba ruwan su da me za su lalata idan suka kai hari," in Stephane Doyon, shugaban sashen gaggawa na Kungiyar Likitocin Komai Da Ruwanka a Sudan yayin tattaunawa da TRT Afirka.

"Ba sa yin wani kokari na hana mutuwar fararen hula ko tabbatar da kare marasa lafiya da ma'iakan asibitoci. Sakamakon haka, ana rasa karin rayuka da dama."

Yaki ma yana da dokoki

Tun yake-yake na farko, daya daga cikin ginshikan wayewa shi ne tabbatar da an bayar d akariya ga mutanen da ba sa dauke da makamai, musamman marasa lafiya da wadanda aka jikkata.

Dokokin Jinkai na Kasa da Kasa da aka amince da su dukkan duniya, ko wasu kundin dokoki da ke bayyana yadda za a yi yaki, sun rarrabe karara tsakanin hari bisa kuskure da laifukan yaki.

Dokokin Jinkai Na Kasa da Kasa sun haramta kai hari kan fararen hula, ma'aikatan lafiya da wadanda aka jikkata. /Hoto: Reuters.

A Sudan, yawan hare-haren kwanan nan ba rarrabe wa tsakanin marasa lafiyan da ke samun kulawa da ma'aikatan da ke kula da su a asibitoci, kuma dukkan su na cutuwa da yakin da aka fara tun 15 ga Afrilun 2023.

Hare-Hare a kai a kai da ake ci gaba da kaiwa a asibitocin el-Fasher sun janyo daduwar mutuwar mutane a cikin watanni 15.

A kalla mutane tara aka kashe a asibitoci goma, an jikkata wasu 38.

Likitocin Komai Da Ruwanka na zargin akwai wata kullalllikan game da hare-hare a asibitoci, ba wai arashi ba ne.

"Bangarorin da ke yaki sun sani sarai cea nan wajen Asibitin Saudiyya ne, kuma sun sani cewa nan ne asibitin gwamnati da ya rage a garin wand ake iya kula da wadanda aka jikkata," in ji Doyon.

Daga hare-hare goma da aka kai a watanni uku da suka gabata tun bayan yakin ya tabarbare, hare-hare 4 an kai su kan Asibitin Sadiyya.

Asibitin Kudu, a daya bangaren, ya zuwa 8 ga Yuni ya fuskanci hare-hare sau biyar. Mayaka dauke da makamai sun shiga asibitin, sun bude wuta, sun sace kayayyaki, ciki har da motar daukar marasa lafiya. Marasa lafiya da ma'aikata sun tsere, kuma tun wannan lokacin aka daina amfani da asibitin.

"Babu wani waje da aka ware a garin don killace wadanda aka jikkata, ko matan da ke bukatar tiyatar gaggawa don kubutar da rayuwarsu yayin haihuwa, idan har wannan yanayi ya ci gaba," in ji Doyon.

"Asibitin Saudi ne wajen fake wa na karshe da ya rage da wadand aaka mamayi gidajensu ke zuwa don samun magani."

Mummunan rikicin kula da lafiya

Kwana guda bayan rikicin ya kacame a ranar 10 ga Mayu, an kai hari ta sama kan Asibitin Yara na Babiker Nahar. Rusin kwanon ginin sashen gaggawa ya rushe, inda yara kanana biyu da ma'aikaci daya suka mutu. Wani ma'aikacin kuma ya rasa lebensa.

Makamai masu linzami da aka harbo daga jiragen sama na yaki, ana amfani da jiragen yaki marasa matuka a yankunan da ke da jama'a da yawa a Sudan, kamar yadda MDD ta bayyana. Hoto / Reuters

"Yaran da ke buƙatar magani yanzu ana kula da su a wani karamin asibiti da ke da karancin kayan aiki. Idan sun samu raunukan yaƙi, ana kula da su a asibitin Saudiyya," in ji shugaban sashen agajin gaggawa na MSF.

MSF ta yi jinyar mutum sama da 2,000 da suka samu raunuka, yayin da wasu 300 suka mutu sakamakon raunukan da suka samu a cikin kwanaki 80 na farkon kazamin fada a el-Fasher.

Dokokin yaki, wadanda ke cikin yarjejeniyar Geneva da kasashe da dama suka amince da su, ciki har da Sudan, sun sanya iyaka yadda za a dinga gudanar da yaƙi.

A cikin watan Fabrairun bana, MDD ta ba da rahoton cewa ana amfani da makamai masu fashewa da ke da kai yin nisan zango, kamar makamai masu linzami da aka harba daga jiragen yaki, da motocin yaki marasa matuka, da bindigogin kakkabo jiragen sama, da harsasai, a yankunan da ke da dimbin jama'a a Sudan.

Rahoton ya yi nuni da wani lamari da ya faru a birnin Khartoum, inda makamai masu linzami 8 suka kashe akalla fararen hula 45 a watan Afrilun 2023 da kuma wani a cikin watan Yuni, lokacin da wasu makaman atilari biyu suka afka wa wata kasuwa a Omdurman, inda suka kashe fararen hula akalla 15.

A watan Satumba, fararen hula goma ne suka mutu a lokacin da wani bam ya tashi a wata tashar mota.

Tsakanin Mayu da Nuwamba 2023, an kai hare-hare 10 kan fararen hula a el-Geneina, babban birnin yammacin Darfur. A cikin dubban da aka kashe a can, akasarinsu 'yan kabilar Masalit ne, a cewar rahoton na MDD.

Rahoton ya bayyana cewa a Morni da Ardamata, an gano akalla gawarwaki 87 a wani kabarin bai-ɗaya.

Toshe hanyoyin kai agaji

A can el-Fasher kuwa, MSF ta damu da ci gaba da toshewar hanyar da manyan motocin da ke jigilar kayayyakin kiwon lafiya ke bi.

"Motocinmu sun bar N'djamena a Chadi sama da makonni shida da suka gabata, kuma ya kamata a ce sun isa el-Fasher. Amma ba mu da masaniyar lokacin da za a sako su," Doyon ya shaida wa TRT Afrika.

"A el-Fasher, muna da isassun kayan aikin tiyata kawai da za mu yi wa mutum 100 magani. Idan adadin wadanda suka mutu ya ci gaba da ƙaruwa, nan ba da jimawa ba wadannan kayayyaki za su ƙare, muna matukar bukatar manyan motocinmu su iso."

Wasu daga cikin manyan motocin na dauke da kayayyakin jinya da magunguna na yara a sansanin na Zamzam, wanda ya yi fama da matsalar karancin abinci mai gina jiki.

"Tuni, yara da yawa a can suna kan gaɓar mutuwa. Ana bukatar wadannan kayayyaki ne domin ceton rayukansu. Idan ba a ɗage takunkumon da aka yi wa ayyukan jinƙai cikin gaggawa ba, za a samu ƙarin asarar rayuka," in ji Doyon.

Yayin da kudaden magani ke ƙarewa cikin gaggawa, kungiyar ta MSF ta yi kira ga dakarun Sudan da ke yaƙi da su daina kai hare-hare kan asibitoci, tare da share hanyar isar kayayyakin jinya a el-Fasher. Har ya zuwa yanzu, ba a ji wannan roƙon ba.

Jerin hare-haren da aka kai asibitoci:

Mayu 11 - Asibitin Kula da Yara na Babiker Nahar: Yara biyu da mai kulawa sun mutu, yayin da wani mai kulawa ya rasa hannu bayan da rufin ICU ya rushe bayan wani harin da aka kai ta sama.

19 ga Mayu – Asibitin Saudiyya: An jefa bam a sashin kula da mata masu haihuwa, inda ya kashe mutum daya tare da jikkata wasu takwas.

Mayu 26 – Asibitin Kudu: Wani harsashi ya fado a cikin asibitin kuma ya raunata wasu mutane uku, yayin da tagogin dakin haihuwa da na motar daukar marasa lafiya suka farfashe.

Mayu 31- Asibitin Kudu: Wani harin bam din ya sake lalata asibitin fiye da na baya

3 ga Yuni - Asibitin Kudu: Wani marar lafiya ya rasu yayin da wani kuma ya jikkata bayan da aka sake kai wani harin bam din da kuma harbe-harbe. Sannan ruwan tanki wajen ya katse aka daina samun ruwa a asibitin.

8 ga Yuni - Asibitin Kudu: Mayakan RSF sun shiga asibitin, suka bude wuta, suka yi sace-sace. Marasa lafiya da ma’aikata sun gudu, aka daina komai a cikin asibitin

21 ga Yuni - Asibitin Saudiyya: An kashe wata mai sayar da magunguna a lokacin da take aikin dare, kuma ginin kantin sayar da magungunan ya lalace lokacin da aka kai harin bam a wurin.

27 ga Yuni - Asibitin Saudiyya: Wani bam ya fado a cikin harabar asibitin, inda ya karya tagar tare da lalata tankin ruwan. Wasu bama-bamai biyu sun fado a nisan mita 20 kacal a wajen ginin, kuma na hudu ya sauka a nisan mita 50 daga ofishin MSF.

29 ga Yuli - Asibitin Saudiyya: An harba harsasai biyu sun afka wa asibitin, inda suka kashe mutum uku tare da raunata 25.

TRT Afrika