Bayan juyin mulki, har yanzu kasar mai makwabtaka da Nijar na fama da matsalolin takunkumin da aka kakaba wa kasar ta Nijar. Hoto: AFP

Daga Firmain Eric Mbadinga

Kasashe masu makwabtaka da juna na yankin Yammacin Afirka, Nijar da Benin suna ta fama da rikice-rikicen tattalin arzikin a tsakaninsu, lamarin da ke kara illata kasashen biyu ba tare da wata kasa da yankin sun shiga tsakani ba, inda aka ware, ana kallonsu suna kidansu, suna rawarsu.

Rashin samun wata kasa daga yankin Afirka ko wata kungiya daga cikin kungiyoyin yankin da za su shiga tsakani domin sulhunta rikicin da ya faro daga karamin sabani a kan zirga-zirgar mutane da kayayyaki ya kara damalmala matsalar ta diflomasiyya.

Tun a watan Afrilu ne Jamhuriyar Benin ke ta korafi, inda ko dai shi da kansa Shugaban Kasa Patrice Talon ya fito ya yi maganar, ko kuma wasu ministocinsa su yi a game da zargin da yake yi cewa kasar Nijar na watsi da ka’idojin duniya da na yankuna da ke lura da zirga-zirgar mutane da kayayyaki tsakanin kasashe.

Wadannan korafe-korafen sun biyo bayan bukatar da Shugaba Talon ya mika wa hukumomi a Nijar na su bude iyakokinsu bayan Kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin da ta kakaba mata a makon karshe na watan Fabrailu. An sanya wa Nijar takunkumi ne bayan juyin mulkin da aka yi wa tsohon Shugaban Kasar Mohammed Bazoum a watan Yulin 2023.

A lokacin da takunkumin ke aiki, Nijar ta assasa Kungiyar Alliance of Sahel States, ko kuma L'Alliance des Etats du Sahel (AES) tare da kasashen Burkina Faso da Mali, inda suka kara nisantar da kansu daga ECOWAS.

Bayan shugabannin sojin Nijar sun ki bude iyakokinsu da Benin ne Shugaban Kasar Benin shi ma ya yanke shawarar sanya man fetur da sauran kayayyakin da suke fitowa daga Nijar a cikin kayayyakin da suke bukatar lasisin amincewa kafin su wuce ta tekun kasar.

“Idan hukumomi a kasar Nijar sun yanke shawarar yin alaka da mu a hukukmance, sai a fara barin jiragen ruwan suna shigowa ko wucewa ta kasarmu,” inji Shugaba Talon a wata tattaunawa da ya yi a ranar 8 ga Mayu, inda yake magana game da jiragen ruwan man fetur.

Kimanin kwana 11 bayan wannan maganar, sannan bayan wani kamfanin China da ke aikin hako man fetur a Nijar ya shiga tsakani, an yi jigilar miliyoyin gangan man fetur ta cikin tekun Benin. Amma a ranar 23 ga Mayu, sai Benin ta sanar da rufe tekun wanda ke tsakaninta da Nijar.

A bangaren Nijar din kuwa, ba a samun gamsassun bayanai daga bangarenta a game da lamarin wanda zai gamsar da mutane dalilinta na cigaba da rufe iyakokin, sai dai tana yawan nanata cewa akwai sojojin Faransa a cikin kasar ta Benin.

Idan ba a manta ba, a watannin baya ne Jamhuriyar Nijar ta bukaci sojojin Faransa su fice mata daga kasarta.

“Mun yanke shawarar kulle iyakokinmu na Benin ne saboda sojojin tsohowar kawarmmu wato Faransa, kasar Benin suka koma bayan sun fice daga Nijar,” inji Ali Firay Ministan Nijar na yanzu Mahamane Lamine Zene a wata sanarwa da ya fitar a ranar 17 ga Mayu.

Sabani da ya dade ana yi

Masu lura da al’amura suna tunanin wannan sabanin zai iya rikidewa zuwa rikici a tsakanin kasashen ECOWAS da ake tunanin Faransa na da karfin iko a kansu da kuma kasashen AES da suka fi kusanci da kasar Rasha.

Shugaban kasar Benin yana jigilar mai ta hanyar oi. Hoto: @Présidence du Bénin

Moustapha Abdoulaye, wani masani a harkar diflomasiyya da tsaro ya yi amannar cewa akwai bukatar a shiga tsakani domin samun maslaha a tsakanin kasashen biyu da suke da dadaddiyar alaka.

Har yanzu, wani kamfani ne kawai ya yi yunkuri shiga tsakani domin samun maslaha, wato kamfanin man fetur na China National Petroleum Corporation, wanda yake aikin hako mai a Nijar.

“Nijar ta yanke shawarar barin ECOWAS domin assasa Kuniyar AES, musamman da kasar Burkina Faso. Wannan rikicin na Nijar da Benin zai iya zama wani yakin bayan fage tsakanin wasu kasashen daban.”

Ra’ayoyi mabambanta

Shi kuma Dokta Romaric Badoussi, wani masani ne game da ECOWAS dan kasar Benin, ya ce ba ya ganin wata alakar rikicin da wata fadar bayan fage na wasu kasashe.

“Ba na ganin sabanin a matsayin rikicin bayan fage na wasu kasashe ECOWAS da AES. Sabani ne kawai na lissafin siyasa da shugabannin mulkin soji na Nijar suke yi. Suna mulkar kasa ce wadda take fama da matsaloli da yawan gaske daga bangarori da dama,” in ji shi.

“Kana ganin yadda mutanen kasar suke nuna rashin jin dadinsu, musamman a kan tsadar kayan abinci.”

A daidai lokacin da ake cigaba da tafka muhawa a kan laifin waye da kuma tunanin illar matsalar da kasashen biyu, su kuma mutanen Nijar da Benin suna cigaba da dandana zafin sabanin.

Kowane bangare na jin radadin yadda Nijar ta rufe iyakokinta din nan, da kuma yadda ita ma Benin ta hana wucewa ta iyakokinta zuwa wasu kasashe, wanda yake shafar zirga-zirga mutane da kayayyaki daga kowane bangare.

“Ina tunanin dole hukumomi a Nijar da Benin su nemo mafita a game da wannan matsalar. Kuma babu mafita face su zauna su fahimci juna domin a samu maslaha. Sai dai matsalar ita ce shin kasashen biyu sun shirya samun maslahar?” in ji Abdoulaye.

Sai dai yana tunanin za a iya samun maslaha. “A diflomasiyya, makiyinki a jiya, zai iya zama abokinka a gobe, sanna abokinka na jiya zai iya zama makiyinka a gobe. Babban abin da ake bukata shi ne samun maslaha da fahimtar juna.”

TRT Afrika