Wata kasuwa a kasar Kenya:. / Photo: Reuters

Daga Dayo Yusuf

Steve Wanyolke yana karbar albashi a duk ranar 26 ga wata, amma hakan ba ya sanya shi wani farin ciki inda ban da na wani dan adadi da ke shiga asusunsa na banki.

"Albashin na kamar caka wuka a zuciya ne duk kowacce rana. Yana tuna min cewa ni talaka ne," ya fada cikin raha.

Aikin da yake yi a matsayin mai raba a binci a gidan sayar da abinci na biyan sa Steve abin da da kyar zai ishi mutum rayuwa a gari irin Nairobi.

Bayan biyan kudin haya, abinci da kudin mota, babu wani abu da zai rage masa da zai ishe shi yin wani abu na jin dadin rayuwa saboda tsadar rayuwa a Kenya.

Da yawa kamar Steve na yin korafi cewa albashinsu ba sh da daraja irin wadda yake da ita a baya.

Steve ya shaida wa TRT Afrika cewa "shekaru bakwai da suka gabata, ina aiki a gidan sayar da abinci ina na ke karbar albashi kasa da yadda na ke karba a yanzu.

Amma kuma, ina iya biyan bukatuna, har na samu 'yan canji. Yanzu kuwa, albashina na kare wa nan da nan bayan na karbe shi a karshen wata."

Abin da ya fi munana halin samun kudade na Steve shi ne biyan bashi da ke cikin kasafin kudinsa a kowanne wata. Ya san me ke faruwa amma ba zai iya rayuwa ba ba tare da cin bashi ba.

"Takardun albashina na bayyana ina biyan bashin da na ci a banki, sannan wani bangare na tafiya ga kungiyar cin dadin ma'aikata. Ana yanke wadannan kudade kai tsaye daga albashina, ba ma na ganin kudin," ya fada cikin korafi.

Pubilius Syrus, marubicin yaren Latin da aka haifa a shekarar 85 BC a Antioch da ke cikn Turkiyya a yanzu haka, shi m aya taba korafin rayuwa irin wannan da Steve ke yi, a lokacin da ya ce "Bashi bautar da mai 'yanci ne".

Yawaitar cin bashi

Duk da cewa tattalin arzikin Kenya na cikin matsala, kwararru na yin gargadin jama'a na iya tsintar kansu a cikin amwuyacin hali saboda rashin amfani da kudade ta hanyar da ta kamata.

A mafi yawancin lokuta, hakan na da alaka da karancin sani ko ma rashin sanin gaba daya kan yadda za a dinga juya kudade.

"Mutane da dama sun bar makaranta saboda rasin sanin yadda za su juya kudade," in ji Charles Macharia, wani mai bayar da shawara kan kashe kudade da ke Nairobi.

Yana da muhimmanci tun da fari a fahimci yadda za a tsara ta yaya za a kashe kudaden da ake samu."

Steve ya kuma ce duk da yawan basussukan da yake da su, ba zai iya rayuwa ba tare da cin bashin ba, yana cewar ai kasashe ma na fama da bashi da ya yi musu katutu.

Kwararru kan kashe kudade sun bayyana cewa hanya mafi sauri wajen kubuta daga yanayin kunci - ba wai cin bashi daga abokai, 'yan uwa, wajen aiki ko banki - ba shi ne mafita ba a koyaushe.

Mutanen da suke cin bashi a lokacin da ba su gama biyan wanda ke kansu ba, suna kan hanyar tsuduma kawunansu a cikin kangin bashi.

Jan ra'ayi ga cin bashi cikin sauki

A Kenya, kamar yadda yake a kasashe da dama masu tasowa da ke burin bunkasa, saukaka yanayin cin bashi na nufin mutane gama-gari na iya samun sukunin kudade.

Ma'aikatan sashen neman kwastomomi na bankuna na karakaina a titunan babban birnin Nairobi don bayyana wa jama'a basussuka masu saukin samu.

Haka kuma, tsarin biyan kudaden ta wayar hannu na watso muku bashi a kan fuskokinku. Wannan na iya zama mai albarka idan mutum na neman tsabar kudi cikin gaggawa.

"Ku fahimci sharuddan cin bashi. Ku san yaya kudin ruwa yake aiki, kudaden da yadda za a biya su don kare kai daga boyayyen wani abu da zai hana mutum biyan bashin," Charles ya bayar da shawara.

"Manufar ita ce a takaita cin bashi sai lokacin da ake da bukatu masu muhimmanci sosai da za su iya dawo da riba, a kawar da sha'awar cin bashi a koyaushe."

A kauracewa kin biyan bashi

Wata babbar ka'ida mai muhimmanci ita ce kaurace wa cin bashi daga bankuna ko sauran hukumomin bayar da bashi, matukar ba ya zama dole ba.

Kwararru na bayar da shawara ga 'yan kasa da su mayar da hankali kan bashin da ake ci don kasuwanci, kamar na sayen kadara ko juya don samun riba da kuma biyan bashin.

Wani tarko kuma shi cin bashi daga hannun wadanda ba su da dokokin aiki wadanda a koyaushe idan bukata ta kama su za su zo su bayar da basussuka kuma saka sharuddan da suka saba wa doka.

Wadannan masu bayar da bashi na son mutane su dinga biyan kudaden ruwa, a yayin da suka gaza biyan asalin kudin da suka karba bashi.

A ra'ayin Steve, tunanin rage yawan bukatunsa a rayuwa ya gajiyar da shi, duk da ya fahimci hakan zai taimaka masa wajen warware matsalolinsa.

"Ina dimauta da shiga tsananin damuwa a duk lokacin da na kalli shekarun da na dauka ina aiki, amma babu wani abu da zan iya nuna wa da na mallaka," ya fada wa TRT Afrika.

Charles na bayar da shawarar neman taimakon kwararru idan mutum ya fada kangin bashi, gaza biya ko karayar arziki.

"Ku nemi shawarar kwararru tare da tattauna wa da wanda ya ba ku bashi don sake kulla yarjejeniya, idan hakan ya zama dole," in ji shi. "Kar ka yi kuskure, bankuna sun fito ne don neman kudi. Idan ya zama dole sai ka ci ba shi, to ka yi amfani da shi ta hanya mai kyau. Kuma ka koyi rayuwa daidai kudin da kake samu."

TRT Afrika