Daga Abdulwasiu Hassan
Rabi'atu Jibrilla ta zura wa ɗanta mai shekara biyu idanu, tana kallon abin da kowace uwa ke tsoro.
''Ba shi lafiya, kamar ma babu jini a jikinsa,'' ta bayyana cikin damuwa, yayin da take jiran lokacin ganin likita ya yi a wata cibiyar kula da marasa lafiya ta ƙasa da ƙasa wato Red Cross (ICRC) da ke Mubi a jihar Adamawa a arewa maso gabashin Nijeriya.
Lokacin da aka haifi yaron yana yana da ƙoshin lafiya. ''Na yaye shi daga shan nono a lokacin da yake shekara ɗaya da wata tara, daga nan ne ya soma rama,'' kamar yadda Rabiatu ta gaya wa TRT Afrika.
Binciken likita bai zo da wani mamaki ba. Ɗan Rabi'atu na fama da matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki, yanayin da ke ƙara zama ruwan dare a arewacin Nijeriya.
''A bara, asibitoci a yankin sun ba da rahoton ƙarin kashi 24 cikin 100 na adadin yawan yaran da ke fama da rashin abinci mai gina jiki, idan aka ƙwatanta da sauran shekarun da suka gabata,'' in ji rahoton Red Cross.
Ƙungiyar da ke da hedkwatarta a birnin Geneva ta bayyana samun ƙaruwar matsalar rashin abinci mai gina jiki wadda ke nuna yadda iyalai ke fama da matsi a yankin Tafkin Chadi wajen samun abinci.
Girman matsalar
Alkaluman da hukumomin agaji suka fitar na nuni da cewa kimanin mutum miliyan 1.6 ne za su fuskanci ƙarancin abinci a yankin Tafkin Chadi a watanni masu zuwa, yayin da ake ci gaba da fuskantar illar rikice-rikice da sauyin yanayi.
''Daga watan Afrilu zuwa Yunin bana, ICRC ta yi rajistar karin kashi 48 cikin 100 na matsalar rashin abinci mai gina jiki tare da matsalolin kiwon lafiya a tsakanin yara 'yan kasa da shekaru biyar a cibiyoyin kiwon lafiya da na tallafawa, idan aka kwatanta da na shekarar 2023,'' in ji rahoton.
Aliyu Dawobe, kwararre kan sadarwa a ICRC, ya ce alamun sun nuna manyan ƙalubalen da ke gaba na rashin abinci mai gina jiki.
"Asibitoci a faɗin Mubi a Adamawa, da Maiduguri a Borno, da kuma Damaturu a Yobe sun ba da rahoton karuwar matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki da ake dangantawa da raguwar samun abinci.
"Halin da ake ciki a arewa maso gabashin Nijeriya na da matukar tayar da hankali," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Tasirin rikici
Rikicin da aka kwashe sama da shekaru 10 ana yi a yankin wanda ya haɗa da na 'yan ƙungiyar Boko Haram masu ɗauke da makamai ya janyo ƙarancin abinci a halin yanzu.
A cewar ofishin kula da ayyukan jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya, OCHA, akalla mutum miliyan biyu da rikicin ya raba da muhallansu ne ba za su iya samun damar komawa gidajensu ba duk da sauƙin lamarin.
Ambaliyar ruwa da ta haifar da ɓarna a Maiduguri da Mubi da kuma wasu sassan jihar Yobe a baya-bayan nan ta ƙara yawan matsalar da yankin ke ciki.
''Manoma suna ta fatan girɓar amfanin nomansu a makonni kaɗan masu zuwa, kafin ambaliyar ruwan ta afku, inda ta shafe komai. Lamarin da ya ƙara sanya al'umma cikin mawuyacin hali,'' in ji Dawobe.
Dawobe na fargabar a ‘yan watanni masu zuwa matsalar ƙarancin abinci za ta iya ƙara ta’azzara matukar ba a kai ga kawo ɗauki ba.
"Da alama babu wata hanyar kuɓuta ga al'ummar da abin ya shafa wadanda suke fama da illar ambaliyar ruwa da sauyin yanayi, da rikice- rikice," in ji shi.
Yaƙin jinƙai
A watan Afrilu, Dawobe ya wallafa a shafinsa na X "labarin wata uwa mai shayarwa daga arewa maso gabashin Nijeriya, wadda ta sha yin gudun hijira ".
Fatsuma da iyalanta sun yi tafiyar kwanaki biyar daga garin Baga na jihar Borno domin isa Maiduguri bayan tashin hankalin da ya afku a garin da ke kan iyakar Tafkin Chadi a shekarun da suka gabata.
Goye da jaririnta ɗan wata bakwai a bayanta da kuma wani ɗanta mai shekaru uku a hannunta, ba ta da wani zaɓi da ya wuce yin tafiyar mai matuƙar wahala.
Da taimakon iyayenta, Fatsuma ta koma garin Geidam mai tazarar kilomita 300 daga arewa maso Yammacin Maiduguri. Kazalika shi ma Geidam, an kai masa hari bayan shekaru uku, nan ma dangin Fatsuma suka sake yin hijira.
A wannan karon, ta koma Gashua ne mai nisan kilomita 100 daya Yammacin Geidam.
Gwagwarmayar da Fatsuma ta yi wajen samun matsuguni da maido da rayuwarta, da kuma ciyar da ‘ya’yanta, ya nuna irin halin da ɗimɓin al’ummar Arewa maso Gabashin Nijeriya suke ciki.
Masu sa ido kan al'amura dai na cewa ana buƙatar haɗin gwiwa don shawo kan matsalar kafin ya wuce gona da iri.
"Don magance wannan lamarin, muna buƙatar mu haɗa kai tare." kamar yadda Dawobe ya shaida wa TRT Afrika yana mai ƙarawa da cewa, "dole ne gwamnati ta tabbatar da cewa an kare fararen hula tare da samun damar zuwa gonakinsu don yin noma. Kuma ko da a cikin yanayi na rikice-rikice, dole ne a mutunta yara da mata."
Ga sauran mutane kamar Rabi’atu, rayuwa ta ta’allaƙa ne da fatan wata rana za a wayi gari da cewa nan ba da daɗewa komai ya zo ƙarshe inda su da ‘ya’yansu za su iya rayuwa cikin ƙoshin lafiya ba tare da tsoro ko yunwa ba.