According to the report, what happens in the next five years will determine the future of life on Earth.

Daga Sylvia Chebet

Ana fuskantar gagarumin koma baya a dazuka, kuma tasirin hakan na ke shafar ɗan adam.

Rahoton Asusun Kula da Namun Daji na Duniya (WWF) kan halittun duniya na 2024 ya bayyana cewa shekaru 50 zuwa 2020, an samu raguwar yawan namun daji da aka sa ido a kansu a faɗin duniya da kusan kashi uku cikin 100.

Ƙididdigar halittun duniya, wanda ke nuni da ma'auni yanayin bambance-bambancen halittu bisa ga yanayin inda suke rayuwa a ɗoron ƙasa da cikin ruwa, an samu raguwar kashi 76 cikin 100 idan aka hada su duka.

Yakunan Latin Amurka da Caribbean sun fi ko ina samun wannann ragi da kaso 95 cikin 100, yayin da Arewacin Amurka ya samu matsakaicin ragi na kaso 39 cikin 100.

Yankin Turai da Asiya ta Tsakiya suma sun fuskancin raguwar da kashi 35 cikin 100.

"Waɗannan alƙaluman suna da ban tsoro ga dukanmu da muka nuna damuwa kan yanayin duniyarmu," in ji Darakta Janar na WWF Kirsten Schuijt a cikin rahoton da aka fitar.

Masana sun danganta yanayin da asarar muhalli, da yawan amfani, da kuma gurbatar yanayi. Sauran barazanar sun haɗa da yaɗuwar cututtuka da sauyin yanayi da kuma illar barnar wasu nau'ikan halittu.

Schuijt ya bayyana cewa raguwar da aka samu ''manuniya ce ga la'akari da cewa raguwar ita ce "mala'i ne na matsananciyar matsananciyar damuwa da sauyin yanayi biyu da kuma asarar yanayi - da kuma barazanar rushewa ga tsarin ka'idoji na dabi'a wanda ke ƙarƙashin duniyarmu mai rai".

Halittun cikin ruwa mau tsafta ne suka fi shan wahala da karewa da kashi 85 sai na tsandauri da kashi 69, sannan na teku kuma da kashi 56.

Kwararrun na cewa wannan na nuni ga karuwar matsin lamba da ake yi wa koguna, tafkuna, tekuna da kasa masu danshi saboda yawaitar kiwon dabbobi, kamun kifi, amfani da kasar noma, rushe dazuka, gurbatar yanayi, da janye ruwa.

Kifayen da ke cikin ruwa mai tsafta, misali, na yawan fuskantar barazana daga madatsun ruwa da sauran sauyi maganarar ruwa, wanda ke hana su sauya wajen zama.

Samar da abinci ne babban jagora wajen kashe halittun, wanda ke da kashi 70 na amfani da ruwa, kuma yake fitar da iskar carbon da kashi daya cikin hudu.

Fitar da iskar carbon na taimaka wa sosai wajen dumama duniya.

Rahoton na WWF ya kuma yi gargadi kan cewa gurbata yanayin zama da rayuwar halittu na iya jefa duniya cikin yanayi mai hatsari matukar ba a dauki matakan gaggawa na magance illar ba.

Rahoton ya ce abinda zai faru nan da shekaru biyar masu zuwa ne zai bayyana makomar rayuwa a duniya.

To hakan duk ya zama mummunan yanayi ga duniya kenan?

"A yayin da lokaci ke kurewa, har yanzu ba mu makara ba wajen kawo gyara," in ji Schuijt.

"Dama da karfin sauya wannan illa na hannayenmu."

Yadda lamarin yake a Afirka

Kenya ce kasar da ta zama fitila wajen bayar da kariya bayan daukar matakai da dama, inda ta tabbatar da cewa yin abinda ya kamata ba tare da tsagaitawa ba a hadin kai zai taimaka waje kare halittun da suke karewa tare da tabbatar sun ci gaba da wanzuwa.

A yayin da namun dawa ke karewa a duniya baki daya, kasar ta Gabashin Afirka ta dawo da hibbar yawan namun dawa musamman zakin Afirka, giwa, da bakin mugun dawa.

Yawaita bayar da kariyar ya kawo daidaituwar lamarin tare da kara yawan wadannan namun dawa a kasar Kenya.

"Daduwar bakin mugun dawa a Kenya daga 400 a 1980 zuwa 1,004 a 2023 babbar nasara ce ga wadannan halittu da ke fuskantar hatsarin karewa," in ji Jackson Kiplagat, shugaban shirin bayar da kariya ga halittu na EEF yayin tattaunawa da TRT Afrika.

Kenya ta saka ɗamba da buri a Dabarun Kasa na Kare Halittu da SHirinta don tabbatar da dawo da rayuwar halittu mai dorewa a kasar.

"Kenya na kan gaba wajen bayar da muhimmiyar gudunmawa don yaki da sauyin yanayi tare da dawo da kyawun duniya, saboda aiki da Tsarin Kare Halittu na Duniya da Yarjejeniyar Paris, da sauran yarjeniyoyi da tsare-tsaren kasa da kasa," in ji Mohamed Awer, shugaban zartarwa a ofishin WWF na Kenya.

"Sake ninka burin kasar na cim ma Kalubalen Bonn son dawo da lafiyar hekta miliyan 10.6 na kasar da ta lalace mataki ne da ke kan turba mai kyau."

Tunanin gogayya

Wadannan kokari da ake yi ba su isa ba.

Kokarin da ake yi ga kakkautawa a nahiyar da ma duniya baki daya na bukatar cim ma manufofin kasa da kasa kan duniyar, yanayi da cigaba mai dorewa nan da 2030.

"Idan har za mu dakatar da lalacewar duniya a matakin da ake bukata don kauce wa fada wa mummunan yanayi, dole ne kudaden da ake bukata don yaki da sauyin yanayi su shiga hannun kasashe har zuwa ga matakin farko don gina wa da kare al'ummun da illar ke yi wa barazana." in ji Awer.

Rahoton WWF wani sabon gargadi ne da nuni ga karuwar hatsarin karewar halittu da lalacewar duniya da samun kariya.

Yana kuma bai wa duniya damar daukar matakai a kan lokaci don kawar da mummunan yanayin da ake ciki, dawo da yawan halittu, da sanya duniya ta wanzu cikin aminci da samun kariya.

TRT Afrika