Al'ummomi da dama a Kenya na fama da karancin asibitoci. / Hoto: James Muriuki

Daga Sylvia Chebet

Gida ya kasance wani wuri mai aminci ga dan'adam – wanda mafaka ce da babu mai son rabuwa da ita a kowane dalili.

Esther Muthoni ta yanke shawarar mayar da gidanta asibiti ga al’ummarta da ke zaune a gefen gari ba tare da bata lokaci ba bayan wani asibiti da mijinta ya bude fiye da shekara goma ya fuskanci barazanar rufewa daga asalin mai gidan.

Sai dai Esther ba ta da masaniya cewa aikin nan da ta yi zai cike gibi matuka a fannin kiwon lafiya.

Asibitin na Zamzam Medical Services wanda ke Tsaunukan Ngong da ke wajen Nairobi babban birnin Kenya a halin yanzu yana kula da marasa lafiya 13,000 a duk shekara.

Asibitin ya zama wani zabi ga dubban mutane sakamakon yawan da aka yi wa asibitocin Nairobi wadanda ke kula da marasa lafiya sama miliyan biyar duk shekara.

Mafari mai kyau

Wannan aikin na Esther ya soma ne a lokacin da ta shaida wa mijinta, wanda likita ne, wani burinta a rayuwa.

Mutane da ke makwaftaka da su na jiransa ya dawo daga wurin aiki kowane dare domin duba matsaloli daban-daban na lafiya da ke damunsu.

“An soma aikin asibitin Zamzam saboda mun ga amfanin amsa kiran al’umma na gaggawa,” kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

“Akwai wata mahaifiya wadda danta ke jijjiga, abin da ya sa ta shiga damuwa har ta bar mu da shi ta tafi. Mun yi masa magani sannan muka aika mata shi gida,” kamar yadda ta tuna.

“A hankali, layin da ke asibitin ya kara tsawo, inda mutane da dama suka nemi su rika zuwa asibitin da daddare. Ta haka ne muka yi tunanin bude asibitin na Zamzam.”

Esther da mai gidanta sun karbi hayar wani dan karamin daki a kusa. “Komai na tafiya ne da wurin.

Ya kasance zauren karbar baki da wurin duba marasa lafiya da wurin sayar da magani da wurin mai karbar kudi,” kamar yadda ta bayyana yadda lamarin ya soma.

Asibitin ya soma ne daga daki daya na tsawon shekara 13, kafin wani lamari da ba a yi zato ba ya taso: wato batun kora.

Zabi daya ne kawai ya rage a yanzu. “Wurin da asibitin Zamzam yake a yanzu gidanmu ne a baya,” in ji Esther.

Dole ne ta sa muka yi komai cikin gaggawa – muka bar gidan, muka rushe wasu bangwaye sannan muka kara wani gini inda muka sa jami’an lafiya suka duba wurin domin amincewa da shi.”

UNICEF ta ce sama da yara 60,000 ke mutuwa a Kenya kafin su kai shekara biyar da haihuwa musamman saboda cututtukan da za a iya kiyayewa. / Hoto: Reuters

Duka wannan aikin har da batun kwaskwarima suna bukatar kudi wanda mijin Esther ba ya da su, musamman bayan ya rasa aikin yi na tsawon lokaci bayan an tashi asibitinsa ta farko. Wannan ya kara kasancewa wani kalubale.

“Ba mu da kudi,” in ji Esther. “Mun tunkari wata cibiyar kudi amma an hana mu. Ana kallonmu a matsayin masu hatsari a sana’a.”

Kwatsam sai kungiyar Medical Credit Fund, wadda kungiya ce mai zaman kanta wadda ke bayar da tallafi ga kanana da matsakaitan masana’antu a wasu kasashen Afirka ta fara shiga Kenya a lokacin.

Sai Esther da mijinta suka yi amfani da dama ta farko da suka samu inda suka samu bashinsu na farko ba tare da bayar da jinginar wani abu ba.

A wani kalubale da suka samu a yunkurinsu, asibitin Zamzam bai kai ingancin zama asibiti ba a lokacin da masu bayar da bashin ke kokarin fitar da kudin.

“Sun bayyana cewa muna zaune a dakin kula da marasa lafiya na musamman. “A lokacin babu tsare-tsare masu tsauri game da kiwon lafiya. Da zarar wurin na da tsafta, babu wata damuwa kuma.”

Matsala ta kai

A daidai lokacin da asibitin ya soma habaka bayan gwaje-gwaje da dama, sai mijin Esther ya kamu da shanyewar barin jiki.

Da a ce Esther ba ta da jajircewa a lokacin mutuwarsa ta ba zata, da mafarkinsu na asibiti ya tafi da mijin kabari.

“Da asibitin ya kasance dakin kula da marasa lafiya na musamman ko kuma da an rufe shi ma. Gudanar da asibiti akwai tsada; kana bukatar kudi. Haka kuma wannan kudin a wani lokaci babu su a kasa.

"Za ka yi aiki kuma za ka yi zaton a biya ka kudinka, sai dai kudin ba sa zuwa a lokacin da ake bukatarsu,” kamar yadda Esther ta bayyana a daya daga matsalolin da ake fuskanta na gudanar da asibiti.

A yanzu tana samun bashi ta cibiyoyin kudi ta hanyar amfani da wayarta domin samun kudi wadanda ke taimaka mata gudanar da ayyukanta na yau da kullum, da biyan kudin wuta da ruwa da sauran gyare-gyare.

“Sai na ji na samu kwarin gwiwa matuka,” in ji Esther. “Daga farko na kasa samun bashi daga banki ba tare da bayar da jingina daga wani ba.

"Ba lamari bane mai sauki ga mace ta mallaki kadara. Wannan ne ya sa ya kasance lamari mai wahala samun bashi daga cibiyoyin kudi.”

Karfi bisa karfi

Esther ta koka kan kalubalen da ke tattare da gudanar da asibiti. / Hoto: Peter Muriuki

Asibitin Zamzam ya kara fadada tun bayan da Esther ta mayar da gidansu asibiti. Asibitin na da bangaren haihuwa da hakori da dakin gwaji da bangaren gashin kashi. Asibitin ya kasance wurin ceton rayuwar al’ummar yankin.

Farida Rimanto, wadda ta girma a unguwar, ta shaida yadda asibitin ya samu sauyi daga shagon sayar da magani zuwa babbar cibiyar lafiya.

“Duka yarana na wurin,” in ji Farida. “Lamari ne da ya kasance mai sauki tun daga farko har karshe.”

Esther na da yakinin cewa asibitinta a hankali ya soma kai wani mataki da zai iya kara girma.

“Ina kallon Zamzam a matsayin babban wuri wanda zai iya bayar da taimakon da ake bukata ba tare da an tura marasa lafiya wani wuri ba,” in ji ta.

“Ina son Zamzam ya zama wani wuri wanda za ka iya shiga ya kasance an yi maka komai. Wannan shi ne mafarkin da da mijina yake da shi.”

Esther ta bayyana cewa duk da bashi ya zama wani lamari da za ta iya samu cikin sauki, amma duk da haka akwai wasu kalubale.

“Akwai bukatar saukaka samun lasisi da kuma haraji. Ga kowane bangare, akwai matakan samun lasisi.

"Sai ka je hukumar kula da asibitoci wadda ke kula da asibitin baki daya sannan hukumar kula da dakunan gwaji sannan magunguna.

"Idan kana da bangaren sikanin sai ka je hukumar da ke kula da wannan bangaren,” in ji ta.

TRT Afrika