Daga Sylvia Chebet
Hasashen da ake yi na yadda duniya za ta kasance nan gaba da matsalar ƙarancin abinci da kuma tasirin hakan, ba wai alamara ba ce a halin yanzu.
Ƙaruwar yanayin zafi da ruwan sama da ambaliya da ƙaruwar ƙwari da tsuntsaye na gona da cututtuka duk suna kawo koma baya ga ayyukan aikin gona a faɗin duniya.
Alkama wadda ta kasance abincin da kimanin mutum biliyan ɗaya da rabi ke amfani da shi a ƙasashe masu bunƙasa da masu tasowa, ciki har da Afirka, ita ma ba ta tsira ba, duk da cewa ta kasance wata shuka wadda za a iya noma ta a wurare daban-daban da suka haɗa da kan tudu da kwari.
A daidai lokacin da kimiyya ke neman mafita dangane da barazanar da bil'adama ke fuskanta game da hakan, wasu sabbin bincike biyu da wata cibiya da ke Mexico da ke bincike kan inganta irin masara da alkama mai suna International Maize and Wheat Improvement Center (CIMMYT) ta yi, ya gano cewa, komawa kan irin alkama na shekarun baya zai iya kawo sauyi ga samar da alkama da tabbatar da wadatar abinci a faɗin duniya.
Dakta Matthew Reynolds, wanda shi ne shugaban fannin nazarin alkama a cibiyar, haka kuma ɗaya daga cikin masu gudanar da duka binciken biyu ya bayyana cewa duka alamun farkon suna bayar da ƙwarin gwiwa.
"Tuni muka soma ganin tasirin hakan a Habasha da Sudan da Masar da Afirka ta Kudu da Kenya da Aljeriya da Maroko da Tunisia da Libiya," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
"Muna wata gaɓa mai hatsari. Hanyoyin da muke da su na inganta iri a yanzu sun yi mana amfani, sai dai akwai buƙatar su magance ƙarin ƙalubalen da muke da su waɗanda sauyin yanayi ya haddasa."
Binciken ya mayar da hankali ne kan wata matattarar ajiye irin alkama kusan 800,000 da ke wurare 155 a faɗin duniya.
Waɗannan sun haɗa da "iri na daji" da na shekarun baya, da waɗanda manoma suka samar waɗanda sun jure wa matsalolin muhalli tsawon miliyoyin shekaru.
Duk da cewa kaso kaɗan na cikin irin wannan irin da aka inganta aka yi amfani da su a hanyoyin noma na zamani, tuni hakan ya samar da amfani mai kyau.
Duka cikin ƙwayoyin halitta ɗaya
Ɗaya daga cikin binciken wanda aka wallafa a mujallar Global Change Biology, ya yi duba ne dangane da yadda wannan irin na alkamar na daji ke da juriya ta ɓangaren rayuwa da muhalli
Binciken ya nuna cewa tun daga shekarar 2000, girbe alkama wadda ke jure wa cututtuka ya yiwu ba tare da amfani da kimanin lita biliyan ɗaya ta maganin ƙwari ba, wadda ya kamata a yi amfani da ita wurin feshi domin kiyaye cututtuka.
"Da a ce tsirran daji ba su bai wa alkama ƙwayoyin halitta da ke jure wa cututtuka ba, da yadda ake amfani da maganin feshi ya ninka sau biyu, wanda hakan zai yi illa ga lafiyar bil'adama da kuma muhalli," in ji dakta Susanne Dreisgacker, wadda jami'a ce a CIMMYT kuma ɗaya daga cikin masu binciken.
Ƙara amfani da sabbin irin ya ƙara adadin alkamar da Amurka ke samarwa wadda ta kai ta dala biliyan 11.
Hakan ya taimaka wajen killace miliyoyin kadada ta filayen daji da sauran wurare.
Binciken ya nuna cewa an girbe sabbin iri waɗanda ake kula da yadda ake inganta su da samar da su a Masar da Afghanistan da Pakistan ta hanyar amfani da tsirrai na daji waɗanda ke saka su su yi kyau da kuma iya juriya.
"Hakan na nufin ƙarin dama ga manoma ta fuskar iri daban-daban domin jure wa yanayi da ƙarancin matsalolin yanayi," kamar yadda Dakta Reynolds ya bayyana.
Kamar yadda masu bincike suka bayyana, wasu daga cikin irin alkama da aka yi gwaji a kansu sun rinƙa nuna halayya irin ta tsirran daji, inda girmansu ya ƙaru da kusan kaso 20 cikin 100 a cikin zafi da fari idan aka kwatanta da irin waɗanda ake da su.
Bincike na biyu wanda aka wallafa a mujallar Nature Climate Change, ya yi bayani game da buƙatar da ake da ita wajen ƙara faɗaɗa bincike da kuma amfani da iri daban-daban domin jure wa yanayi.
Daga cikin irin halayen da ake buƙata irin na alkamar ya nuna akwai fitar da jijiyoyi sosai ta yadda za su samu ruwa da kyau, da jure wa zafi da kuma ƙara ingantawa da iya rayuwa ko da ba a samu ruwan sama da wuri ba ko a lokacin ambaliya.
Inganta iri na zamani ya mayar da hankali kan wasu sabbin nau'ukan tsirrai waɗanda ake kira "star athletes" waɗanda matasan tsirrai ne da tuni suka nuna cewa suna da kyau.
Bambance-bambancen kwayoyin halittar dangin alkama na daji na da juriya duk da cewa suna ɗaukar lokaci kuma ana kashe kuɗi, haka kuma hatsarinsu ya fi na gargajiya da ake amfani da su.
Sai dai sabbin fasahar da ake da su sun sauya lamarin.
Yankin da bai bayyana ba
"Muna da kayan aikin da za mu iya gano ƙwayoyin halitta na tsirrai waɗanda a baya masu inganta su ba sa iyawa," a cewar Dakta Benjamin Kilian, ɗaya daga cikin marubuta sannan shuagaban shirin Crop Trust's Biodiversity for Opportunities, Livelihoods and Development project wanda ke bayar da goyon baya wurin amfani da tsirrai a faɗin duniya.
Daga cikin irin waɗannan kayan aikin na fasaha waɗanda da Turanci ake kiransu next-generation gene sequencing da big-data analytics da remote sensing technologies da satellite imagery.
Na ƙarshen wato satellite imagery na bayar da dama ga masu binciken su sa ido kan halaye waɗanda suka haɗa da yanayin girma ko kuma jure wa cuta a faɗin duniya.
Sai dai amfani da irin waɗannan ƙwayoyin halitta yadda ya kamata na buƙatar haɗin kan duniya.
"Tasiri mafi muhimmanci na zuwa ne ta hanyar faɗaɗa raba kayayyakin fasaha," in ji Dakta Kilian.
Sabbin fasahohin na bayar da dama ga masu bincike kan tsirrai su kula da aikawa da halaye masu kyau na tsirran daji domin mayar da abin da ake gani a matsayin mai hatsari zuwa mai amfani da jure wa sauyin yanayi.
"Fasahar tauraron ɗan'adam na mayar da duniya tamkar ɗakin bincike," in ji Dakta Reynolds.
"Idan aka haɗa da ƙirƙirarriyar basira domin ƙara inganta tsirrai, za mu iya ganin mafita dangane da juriyar yanayi.
Hakan shi ma zai yi aiki ga sauran tsirrai waɗanda ke jure wa yanayin tsirran daji.