Zimbabwe Conflict 1

Daga Mary Mundeya

Muchaneta Munodya da ke kauyen Mapfumo a gundumar Masvingo ta Zimbabwe na shayar da jaririnta dan mako biyu a lokacin da ta jiyo ihu da kururuwar mijinta Robert Maroyi, yana neman a ceci rayuwarsa.

Sai ta yi wuf ta fita waje inda ta ga kura ta rutsa shi, har ta cisge masa yatsu biyar-biyar na dukkan hannayensa. A lokacin da kurar ta hango matar, sai ta koma kanta da nufin kai mata hari.

Muchaneta wacce kurar ta lalatawa fuska, ta tsinci kanta a gadon asibitin da ke yankin, a kwance kusa da mijinta da shi kuma ta cire masa yatsu.

Ma’auratan sun shafe watanni suna jinya a asibitin wanda kudin da aka caje su ya fi karfin aljihunsu.

Ba su kadai wannan lamari ke shafa ba. Al’ummomin da ke yankunan da namun dajin ke da yawa a Zimbabwe sun shafe tsawon shekaru suna cikin yanayin ƙaƙa-ni-ka-yi saboda yawan fadan da suke yi da namun dajin da ke shiga ƙauyukansu don neman abinci da ruwa.

Lamarin yana jawo yawan fada tsakanin mutane da namun dajin inda ake asarar rayuka da jin raunuka.

Yadda abin ya faru

Da misalin karfe biyu na tsakar daren 18 ga watan Yulin 2022 mijin Muchaneta ya jiwo kukan dabbobinsa daga garken da suke daure.

Nan da nan sai ya dauki tocilan don ya je ya ga abin da ke faruwa.

“Mijina ya yi mamakin yadda kurar ta zura masa ido ba ta gudu ba duk kuwa da tunkararta da yake yi da haska ta da tocilan.

Kura ta cire wa mijin Muchaneta yatsun hannayensa/Photo TRT Afrika

“Sai ya fara yin hargowa don korar kurar, lamarin da ya sa ta dan matsa daga gaban garken dabbobin, amma kuma sai kawai ta afka masa a lokacin da ya juya don komawa dako,” Muchaneta ta shaida wa TRT Afrika a lokacin da take tuna yadda mummunan abin ya faru.

Da ta jiyo gurnanin mjinta, sai ta dauki wata tocilan din ta fita waje ta dauki sanda da nufin ta kare mijin nata.

“Ai kuwa kurar nan na hangoni sai ta kyale mijina wanda ke kwance a kasa magashiyan jinni na zuba daga hannaye da fuskarsa, ta yo kaina,” in ji ta.

A daidai lokacin ne mahaifin Muchaneta da kanin mijinta suka kawo dauki inda suka cece ta daga bakin kurar da ta yi nufin cinye ta da ranta.

Danta dan shekara 11 ya dauko wani langa-langa ya kori kurar da shi, wanda hakan ya sa ta gudu ta shige cikin jejin da ke kusa da wajen.

Barnar namun daji

Hukumar kula da gandun daji ta kasar, ZimParks, ta ce giwaye sun kashe fiye da mutum 80 a shekarar 2021 kawai, yayin da sauran dabbobi irin su kada da kuraye suka ji wa daruruwan mutane rauni.

A yanzu haka kasar Zimbabwe ta fi kowacce yawan mutanen da suka mutu sakamakon fada tsakanin mutane da namun daji a yankin Kudancin Afirka.

Fadan namun daji da mutane na munana a wasu kasashen Kudancin Afirka /TRT Afrika

Mai magana da yawun ZimParks, Tinashe Farawo ta ce yana da wahala hukumar ta iya amsa dukkan kiran gaggawar da ake yawan yi musu daga al’ummomin da ke bukatar taimako na harin dabbobi, saboda ba su da isassun kayan aiki da ma kudi.

“Ana samun fada tsakanin dabbobi da mutane a kowane sashe na kasar.

“Muna iya bakin kokarinmu a ko yaushe don ganin mun kai agaji da gaggawa, amma duk duniyar nan ZimParks ce kadai hukumar kula da gandun daji da ba ta samun tallafin kudi daga gwamnatinta.

Muna cin abin da muka kashe,” Farawo ta fada yayin amsa tambayoyi daga ‘yan jarida a wajen wani taro na gandun daji.

Sannan kuma al’umma ba ta goyon bayan tattalin gandun daji, wani abu da kwararru suka ce zai iya kawo karshen dabbobi da dama.

Duk da taimakon kudade da gwamnati ta amince a fitar ran 1 ga watan Nuwamban bara don tallafa wa iyalan da wannan bala’i ya rutsa da su, don su biya kudaden asibiti da na jana’iza, hakan bai wani burge al’ummar kasar ba.

Farauta

A shekarun baya-bayan nan, ana samun karuwar farautar dabbobin daji na ban mamaki, wanda a da can baya ya dan lafa.

Wani bincike na wata kungiya ta wasu lauyoyi da kwararru kan muhalli, Fauna and Flora Zimbabwe (FafloZim), ya gano cewa an kama Karin mafarauta a shekarar 2022 fiye da 2021.

Tun watan Yulin 2022, kungiyar ta wallafa batun kamun mutum 19 da gano hauren giwa 36 a Zimbabwe.

“Abin damuwa ne sosai ganin yadda aka gano haure 36 a cikin wata bakwai kawai. Hauren giwa 36 na nufin an kasha giwa 18 kenan,” a cewar binciken.

Kungiyar ta alakanta karuwar farautar dabbobin da talaucin da ke addabar mutane, wanda yake sake muni saboda farin da yake addabar Zimbabwe a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ke jawo gasar neman abinci da ruwa a tsakanin mutane da namun daji.

Dabbobin daji kamar giwaye da zakuna da kuraye na shiga cikin kauyuka sosai, abin da ke jawo mutane na asarar amfanin gonarsu ko kuma ma har su rasa rayukansu a kokarin kare dabbobi da abincinsu.

Kungiyar kula da namun daji ta Victoria Falls Wildlife Trust a yankin Hwange da ke yammacin Zimbabwe, ya ce zakuna sun kashe shanu 159 daga tsakanin shekarar 2020 da 2021, lamarin da ya jawo mummunan yanai ga mazauna yankin wadanda suka dogara da shanun a matsayin kudade don sayen kayan abinci a lokacin fari.

A kokarinsu na daukar fansar asarar da namun daji ke jawo musu, mutanen al’ummomin da ke yankunan da ake karewa ko wadanda suke yankin Sentinel Limpopo Safari a kan iyakar Zimbabwe da Afirka ta Kudu, na shiga yankin gandun dajin su kashe namun daji don samun abinci ko don su sayar.

An Ambato daya daga cikin shuganannin gundumar, Ketumile Mahopolo Nare a wata hira da aka yi da shi a baya-bayan nan yana cewa, “Kusan a yanzu kullum mutane suna kashe namun daji don ci ko sayarwa a yankin nan.

“Mutane na shiga ciki yunwa da tsanani don nemar wa iyalansu abinci sakamakon fari da asarar da ake samu sakamakon barnar da namun daji ke jawowa, don haka farautar dabbobi kamar su barewa da gada da sauransu sun zama jiki.”

Daraktar gandun dajin Sentinel Limpopo Safari, Vanessa Bristow ta ce abin takaici ne ganin yadda mutane suka mayar da farautar namun daji a mtsayin hanyar ramuwa kan hare-haren da dabbobi ke kai musu.

“Mutanen yankunan nan gani suke namun dajin nasu ne don haka suna da damar yin yadda suka so da su.

"Tun da sun ga ba sa samun komai daga harkar yawon bude idon da ake yi da gandun dajin, sai suke ganin kamar an yi watsi da hidimominsu ne ta yadda ba su da mafita sai yin farautar,” in ji ta.

Wani rahoto na Hukumar Kula da Namun Daji ta Duniya da kuma Hukumar Kare Muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya UNEP, ya yi gargadin cewa rikicin namun daji da mutane babbar barazana ce ga wasu dabbobin.

TRT Afrika