A kalla mutane 550 ne suka mutu, yayinda kusan mutum miliyan biyu suka rasa matsugunansu sakamakon ambaliyar ruwa a baya-bayan nan a Chadi.. / Photo: AFP

Daga Firmain Eric Mbadinga

Yadda sararin samaniya ya tsaya cak tsakar dare na iya kawar da hankula. Kamar yadda Dieudonne Alladoum ya yi kawaici a lokacin da yake kallon tantuna da irin ibtila'in da ya samu rayuwarsa sakamakon ambaliyar ruwa a Chadi.

Alladoum da ke zaune a N'Djamena babban birnin kasar ta tsakiyar Afirka da ba ta da iyaka da teku, ya yi asarar kusan komai da ya mallaka sakamakon ambaliyar da aka dinga fuskanta tun watan Yuli. Haka ma Sob-hinka Damaris da iyalanta.

Abu daya da ke ci gaba da rike wadannan mazaje da iyalansu shi ne fata nagari da suke da shi ga kawunansu.

"Tsawon watanni ina wannan waje tare da matata da yarana. Rayuwar babu dadi. Muna bukatar tabarmi, tantuna da kayan amfani cikn gaggawa, amma har yanzu ba mu samu wani taimako ba. Muna juriya ne kawai saboda akwai dan abinda za mu iya yi." Alladoun ya fada wa TRT Afrika.

Mutuwa da rushewar gine-gine

Rugugin tsawa da walkiya na sanya tsoro da fargaba ga kasar da ake yawan samun ruwan sama mai karfi, wanda ba abu ne da aka saba gani ba musamman ma a saharar arewa maso-gabashin kasar.

An samu mamakon ruwan sama a wannan shekarar inda ambaliya ta kashe mutane da lalata dukiyoyi a dukkan lardunan kasar 23.

Alkaluman da gwamnati da Majalisar Dinkin Duniya suka tattara, sun bayyana mutane sama da 550 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwan, mafi yawan su sun dilmiye a ruwa. Sannan ibtila'in ya shafi kusan mutane miliyan biyu.

Asarar da aka yi ta hada da rushewar gidaje 164,000, mutuwar dabbobi 60,000, da amfanin gona da ya kai yawan hekta 250,000.

Gwamnati 'za ta taimaka wa' wadanda lamarin ya shafa

Ruwa ya mamaye gidan Alladoum a N'Djamena bayan kogunan Chari da Logone, da suka karye suna gangarowa yankunan jama'a.

A yayin da dubunnan wadanda suka rasa matsugunansu suke rayuwa a sansanoni, wurare 'yan kadan ne aka amince da su kamar irin su Farcha Milezi da Basilique, dukkan su da ke N'Djemena.

Muhimmancin gwamnati ta amince da sansanonin shi ne, hakan zai sanya a dinga kai musu kayan tallafi na abinci da jin kai.

A watan Satumba, sakatare janar na ma'aikatar walwala, Mahamat Abdelkerim Bagari, ya ce gwamnati za ta tallafa wa wadanda ibtila'in ambaliyar ruwarn ta shafa, wanda masana harkokin muhalli suka bayyana da illar sauyin yanayi.

 Kwanakin baya gwamnatin Chadi ta sanar da ware dala 942,000 don biyan bukatun gaggawa na wadanda ambaliyar ta shafa. / Photo: AFP

'Ban san me zan yi ba'

"Zan iya tabbatar muku cewa a wadannan lokuta na kalubale, sashen ya bayyana kokarin da muke yi na samar da tallafi," in shi a yayin da rukunin wasu mutanen da suka rasa matsugunansu ke iso wa sansanin Farcha Milezi..

Bayan ga tantuunan da gwamnati ta samar don wadanda ambaliyar ta shafa, dubunnan mutane sun kafa nasu da kansu.

Damaris, mahaifiyar wani yaro da ma wasu yaran manya, ta tafi da iyalanta zuwa tantunan a lokacin da ruwan kogin Chari ya mamaye gidansu. Ta damu da dan karamin dan ta, wanda tun wannan lokacin yake fama da gudawa.

"Ban sna me zan yi ba. ya zama lallai gwamnati ta nemo mana mafita. Ba mu da abinci. Ruwa ya kewaye mu amma ba mu da urwan sha. A wasu lokutan, muna amfani da ruwan da ke malale ne," ta fada wa TRT Afrika.

Ana bukatar taimakon kusan dala miliyan 100

Irin labaran Damaris ake samu a larduna irin su Lac, Mandoul, Moyen Chari, Tandjile, da Mayo-Kebbi Est. Ofishin Ayyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya ya lissafo wadannan larduna a matsayin wadanda ke cikin yankunan da lamarin ya fi munana.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasshen cewa ana bukatar dala miliyan 97 don bayar da tallafin da ya kamata ga mutanen da cikin mawuyacin hali sakamakon ambaliyar.

Gwamnatin Chadi, wadda ta bayyana kasafin CFA miliyan 580 (dala 924,000) don magance bukatun gaggawa, ta nem taimako daga angarori da dama.

Firaministan Chadi, Allah-Maye Halina, ya yi roko a hukumance a ranar 4 ga Oktoba.

Lamarin ya shafi makarantu

Alphonse Djobsou, shugaban wata makaranta a SOkolo da ke wajen birnin n'Djemena, na damuwa matuka inda ya tuna yadda dalibansa ba sa iya smaun damar zuwa makaranta.

"Tun 2022 muke fuskantar irin wannan ambaliya. Amma a bana ne aka fi samun ruwan saman. Ruwa ya yi awon gaba da makarantu, inda dalibai da iyayensu suka tarwatse. Mahukunta sun ce mu jira har sai nan da wata guda za a koma makaranta," ya fada wa TRT Afrika.

"Mun bayar da shawarar mahukunta su gina matsafar ruwa a kauyen don hana afkuwar ambaliyar ruwa bayan an samu ruwan sama."

A watan Oktoba, an aika sojoji su taimaka wajen sauya wa jama'a matsuguni zuwa wurare masu tsaro. an kafa kwamitin kar ta kwana na agaji da bayar da kariya na kasa game da ambaliyar ruwan, da manufar daukar matakan da suka dace, ciki har da gyara hanyoyin ruwa, musamman a birane.

Mahukunta sun ce an raba wa jami'an ayyukan jin kai da ake aiki tare a su kaya da suka kai na dala miliyan 20,4 don rarraba wa ga yankunan da ibtila'in ya shafa.

TRT Afrika