Daga Pauline Odhiambo
Kwakwalwa babbar gaba ce da ke warware matsaloli – idan ba ta fada cikin tunanin abubuwan da suka faru a baya ba, tana mayar da hankali ne kan tunanin abin da zai faru a nan gaba.
Abin da Emily Banyo, mai shekara 28, take yi da kwakwalwarta kenan. Ya kamata ta sani cewa matsalar kwakwalwar da take fuskanta tsawon shekaru da kuma yadda akai-akai take fada wa tsananin tunani wajen yaki da haka, inda take neman maganin matsalolin da take ciki.
Matsalolinta da damuwarta ya sa ta kafa kamfanin Utalii Creative ta fara kafa shi ne don ta rage damuwarta gabanin ta rikida zuwa wani tsari na magance matsalolin kwakwalwa.
"A shekarar 2019, na ji kamar kwakwalwata ta fashe. Ina aiki da wani kamfani a lokacin, aikin ya sa ni cikin wani hali," kamar yadda matar 'yar Ugandan ta bayyana, wacce matsalolin kwakwalwarta suka fara lokacin tana daliba a Afirka ta Kudu, inda ta rika shiga damuwa saboda dabi'un nuna kin jinin baki.
"Lokacin da na nemi taimako, na yanke shawara yin wani aiki da kwakwalwata saboda na kauce wa tsananin tunani, da kuma fargabar da ke tattare da hakan," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
Bayan amfani da wannan shawara, Emily ta kai ziyara shagunan wasannin Game a babban birnin Uganda wato Kampala don yin wasanni masu sarkakiya da ke taimaka wajen ba zuciya natsuwa.
Ta fahimci cewa akwai abubuwan da ake rasa wa a Afirka daga jerin zabin da ake bai wa kwastomomi. "Ina ganin yadda ake wasan game na Puzzle a hasumiyar Eiffel Tower da Grand Canyon da sauran muhimman wuraren tarihi, amma ina son samu abu daga Afirka," in ji ta.
Ta koma gida gwiwarta ta yi sanyi a ranar, amma kuma ta koma da sabon tunanin kasuwanci.
Lokacin da muka shaida wa mahaifinta aniyyar kafa kamfanin wasanni na Puzzle wanda zai mayar da hankali kan Afirka, ya ji dadin hakan kuma ya yi tambayoyi da za suka mata jagora zuwa ma'aikatar yawon bude ido.
Bayan wani dan lokaci sai aka kaddamar da samfari don bunkasa shi zuwa gaba.
"Ni da mahaifina mun zabi sunan 'Utalii' ya kasance sunan kamfaninmu, wanda yake nufin yawon bude ido a harshen Swahili," in ji Emily, wacce ta yi aiki da daya daga cikin manyan kamfanonin yawon bude ido a Afirka ta Kudu yayin da take birnin Cape Town.
Tsarin aikin kwakwalwa
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce buga wasanni irinsu lido da dara za su iya taimaka wa lafiyar kwakwalwa da lafiyar jiki.
Wani nazari ya nuna cewa wasannin da ke sa kwakwalwa tunani suna taimaka wajen kaifinta da kuma lafiyarta, wanda hakan yake taimaka wajen kariya daga cututtukan mantuwa kamar Dementia da Schizophrenia da Alzheimer da sauransu.
Masana sun ce kwakwalwa tana sakin sinadarin da ke jawo nishadi wato Dopamine idan mutum ya warware wata matsala, wanda hakan yake taimaka wa lafiyar kwakwalwa.
Ga Emily da mahaifinta abubuwa na tafiya yadda ya kamata har sai bayan barkewar annobar korona a shekarar 2020.
"Daga farko mun so mu sayi samfari game daga China, saboda a nan kudin samar da su yana da sauki, amma saboda annobar sai komai ya tsaya cak," in ji ta.
Samun kamfanin Uganda wanda yake da duka abin da ake bukata yana da wuya samu a wajen uba da 'yarsa. Mutane biyun sun yi ta yin nazari kan kamfanoni da dama gabanin su samu wanda ya dace sosai.
"Kudin da ake kashewa wajen samar da su ya yi sama da nunki 30 fiye da kudin da aka yi kiyasi, amma a karshe mun samu kamfani da samar mana da su cikin farashi mai rahusa. Sun samar da samfarin wata shida daga bisani," in ji Emily.
Kafin a samar da samfarin, mahaifiyar Emily wacce masaniya ce kan dabi'un yara, ta bayar da shawarar yadda za a tsara wasan Puzzles na Utalii Creative don taimaka wa lafiyar kwakwalwar yara.
"Ta nuna min yadda za a yi amfani da Puzzles wajen kara koyon karfafa kaifin basira da fahimtar bambancen abu," in ji Emily.
Saboda yadda take da kwarewa a fannin yada labarai hakan ya sa cikin sauri ta fara tallata wasannin Puzzle din da ta samar.
"Suna fatan isa ga 'yan yawon bude ido a kasuwa. Shekarun da na yi aiki a shagon da ke sayar da tsaraba ga matafiya a Afirka ta Kudu ya sa na fahimci dabi'ar 'yan yawon bude ido, wadanda a kodayaushe suke son komawa da wani abu gida."
Bayan samar da samfarin, komai ya tafi daidai ga uba da 'yar har bayan da wata matsalar lafiya ta gaggawa ta rusa musu tsare-tsarensu.
"Mahaifina ya samu shanyewar barin jiki, kuma a matsayinmu na danginsa muna masa fatan samun koshin lafiya. Duk wani kudi da muka ware don zuba wa a kasuwanci, sai da muka koma muka kashe su wajen yi masa magani, wanda ya kwashe tsawon shekara daya da wata biyu. Gaba daya matsalar ta shafi lafiyar kwakwalwarmu," in ji Emily.
Bangarorin sun dace
Bayan mahaifinta ya murmure, an dawo da tsare-tsaren kafa kamfaninta inda ta samar da wasannin game na Puzzle guda 1,000 masu alaka da Afirka.
"Yanzu muna da wasannin Puzzle da aka yi musu tsari don amfani a Afirka da ado mai kayatarwa — misali, wasan Ugandan Rolex, wanda yake da farin jini kuma yana dauke da wata alaka ta musamman ta kasar.
Mun yi amfani da wannan alama kuma muka samar da wasan Puzzle daga nan sai muka kawata shi da wasu bayanai na wurare," kamar yadda Emily ta yi bayani.
A halin yanzu kamfanin Utalii yana samar da game din Puzzle daga guda 99 zuwa 500, ko da yake wannan wani bangane na wani babban buri da Emily take da shi dangane da kamfaninta.
"Babban burin shi ne samun lafiyar kwakwalwa da bunkasa martabar Afirka da gyara sunanta ta hanyar amfani da kayayyaki da kafafen yada labarai da kuma wasannin game. Mu rika bayar da labarin kanmu da samun wakilci daga kowane bangare saboda muhimmancin kare lafiyar zukatanmu da kuma al'adunmu," in ji ta.