Daga Sylvia Chebet
A yarda ko kar a yarda, akwai yanayin da ke zama ''zamantakewar rayuwar al'umma da ƙwayoyin cuta'', sai dai ba kamar sauran ƙwayoyin halitta da ake iya taka musu birki ba, waɗannan ƙananan ƙwayoyin halittu suna yaduwa ne cikin rigingimu da tashe-tashen hankula.
Masana harkokin kiwon lafiyar jama'a dai na tsoron wannan haɗin na rikice-rikice da yaduwar ƙwayoyi cuta, kamar yadda yakan faru a wasu sassan duniya.
A yanzu dai babbar cibiyar da cutar Mpox ta barke, wadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana a matsayin ''mai barazana ga lafiyar al'umma'' ita ce Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, ƙasar da ta jima ta fama da rikice-rikice na ƙungiyoyin 'yan tawaye da dama.
Ƙungiyar agaji ta Médecins Sans Frontières (MSF), wadda aka fi sani da Doctors Without Borders, ta ce an samu rahoton bullar cutar a yankunan da ke da yawan jama'a kamar Goma- birnin da ke da yawan mutane miliyan biyu- da kuma wasu wurare da dubban daruruwan mutane suka nemi mafaka saboda rikicin 'yan bindiga da ya addabi yankin Arewacin Kivu.
''Fiye da mutane 23 aka tabbatar sun kamu da cutar a Arewancin Kivu a makon jiya kadai, amma mun lura cewa adaɗin ya ƙara yawa.
Kazalika an samu yaduwar cutar a sansanonin 'yan gudun hijira, inda aka tabbatar mutane 11 ne suka kamu da cutar,'' kamar yaddaAgnese Comeli wadda ta ke jagorantar ayyukan ƙungiyar MSF kan cutar MPOX a Goma ta shaida wa TRTA frika.
Barkewa cutar a sansanonin da ke cike da ɗimbin jama'a yana da matukar tayar da hankali ga ƙungiyar agajin ta likitoci.
"Tsarin kula da cutar Mpox shi ne samar da riga-kafin yaduwarsa, ta hanyar inganta hanyoyin tsafta da maganin taƙaita zafin cutar da kuma gyara wurin ciwon," in ji Comeli.
Rashin tsaftar yanayi
Ƙwararru a fannin kiwon lafiya sun bayyana damuwa kan ƙarancin yanayin taƙaita yaɗuwar cutar da kuma kula da shi a ciki da wajen Goma.
''Ta yaya za mu yi tsammanin iyalai da suke zaune a ƙananan matsunai, ba tare da samun isasshen ruwa da wuraren tsafta ko ma sabulu ba su aiwatar da matakan kariya?
Ta yaya yaram da ke fama da rashin abinci mai gna jiki za su samu arfin kawar da cutar?'' a cewar Dakta Tejshri Shah, kwararriya kan cututtukan yara da sauran cututtuka masu yaɗuwa da ke aiki tare da MSF.
Dakta Shah ta kuma bayyana damuwarta game da yawan yadda ake cin zarafi da fyaɗe ga 'yan mata da matan da ke zaune a sansanonin.
''A wani taron ba da shawarwari da na halarta tare da waɗanda suka tsira daga fyaɗe, na ci haɗu da wata mata da ke zaune da 'ya'yanta bakwai a ƙarkashin wani matsuguni na leda, abokin zamanta ya guje ta bayan ya ci zarafinta,'' kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
Kwararriyar likitar a MSF ta yi imanin cewa aiwatar da matakan kariya daga cutar Mpox a cikin sansanonin yana da matukar wahala.
''Idan ƙurajen Mpox suka feso wa matar da na haɗu da ita wadda ta tsira daga fyaɗe, za a ce mata ta canza tsummar amfanin mata, ta wanke komai sosai, sannan ta ware kanta har sai ta samu sauƙi.
Amma ta yaya za ta yi wanka ba tare da sabulu ba, kuma da litar ruwa kaɗan da ake samu a kullum? in ji Dakta Shah.
"Ta yaya za ta keɓe kanta, tare da kare 'ya'yanta a yayin da suke zama tare a ƙarƙashin matsuguninsu na leda? Idan ta ware kanta, wa zai sama musu abinci da za su ci? Wa zai deɓo musu itace? Wa zai rarrashi sabon jaririn?"
Taimakon riga-kafi
Zuwan maganin riga-kafin cutatr Mpox a DRC da ke fama da rikici ya samar da kyakkyawan fata ga masana kiwon lafiya da ke ƙoƙarin shawo kan barkewar cutar.
"Mun yi farin cikin samun kashin farko na alluran JYNNEOS kusan 100,000 na rigakafin Mpox a DRC, inda ake sa ran samun ƙarin wasu 100,900 a gaba," a cewar Jean Kaseya Darakta janar na Cibiyar Kula da yaduwar Cututtuka ta Afirka (CDC).
A ƙarshen makon jiya, an samu allurai kusan 200,000 a kasar.
Mpox yana yaduwa a larduna da dama a ƙasar da ke yankin Afirka ta Tsakiya. Tun daga farkon shekarar 2024, ma'aikatar lafiya ta DRC ta ba da rahoton samun fiye da mutane 4,901 waɗanda aka tabbatar sun kamu da cutar, yayin da mutane kusa 630 suka mutu.
Masana kiwon lafiya sun ce waɗannan alƙalumaman suna wakiltar yadda ake ɗaɗa samun karuwar masu kamuwa da cutar da kuma mace-mace idan aka kwatanta da shekarun baya.
Yayin da dogon jiran samun riga-kafin cutar ya zo ƙarshe, rashin wadatar yawan jama'a na zama babban ƙalubale.
"Alurar riga-kafin MPox da WHO ta ba da shawara akai yana da tsada, kuma har yanzu samunsa ba wadata ba yawan buƙatun da ake da shi a kasa ba." in ji Comeli.
A taƙaice dai, allurar riga-kafi kaɗai ba zai kawar da matsalar ba. Masana kiwon lafiya sun yarda cewa inganta yanayin rayuwa yana da matukar muhimmanci wajen yakar irin wannan annoba.
Kazalika kawo ƙarshen rigingimun da aka daɗe ana fama da su zai bai wa al'ummar DRC da ke gudun hijira damar barin yanayin rashin tsafta a sansanonin kana su koma gidajensu cikin aminci, tare da rage rauninsu wajen ɗaukar cutar ta Mpox.