A watan Satumba aka gudanar da Taron Yanayi na Afirka a Nairobi. Hoto: TRT Afrika

Daga Coletta Wanjohi

Wani yaro ne yake wasa tare da yin tsalle ya tsallake wata babbar kwata, can kuma muryar wata mace ce take masa ihu kan ya kula.

Sautinta ya gushe bayan da wani sauti daga lasifika ya mamaye yankin. Wani mutum ne da ke kira ga jama'a kan su fito a yi gangami tare da su.

Yana kuwwa da harshen Swahili yana fadin "Twendeni, twendeni," wanda ke nufin "Mu tafi, mu tafi".

Mose Wanja, mutumin da ya kafa Kungiyar Adalcin Zamantakewa ta Mathare, na jagorantar matasa zuwa Tafkin Nairobi da yake kwarara ta unguwannin marasa galihu. Kogin, wanda nan ne masarmar ruwa ga jama'ar da ke kewayensa, na bukatar a tsaftace shi.

Kananan manoma da ke wannan ƙauye mai mutum sama da 200,000, na amfani da ruwan tafkin don ban ruwa a gonakinsu.

Wanja da abokan aikinsa na gudanar da "gangamin adal gain muhalli" don kyautata yanayin mahallansu.

"Muna tunanin Mathare na iya zama ingantaccen wajen zama. Ba mu da bishiyoyi a unguwanni, hakan ya sanya muka yi tunanin shuka su tare da yin ado ga Mathare," in ji Wanja, yayin tataunawarsa da TRT Afirka.

Wadannan matasa na Mathare sun ƙaddamar da shirin a 2014, inda suka gyara filayen da ke gab da kogin tare da dasa bishiyoyi tare da samar da filin wasan yara.

"Bishiyoyi halittu ne na musamman; mutum na iya samun waraka idan ya je wajen da ke da bishiyoyi," in ji Wanja.

"A baya nan wajen zubar da shara ne. Mun gyara shi don amfanin jama'a tare da ba shi sunan Filin Shakatawa na Jama'ar Mathare. Za ku ga yadda wajen yake da tsaro ga matasa."

Ana matsa lamba ga manyan masu gurbata muhalli kan su dauki matakan yaki da illar hakan. Hoto: AP

Har yanzu ana ci gaba da ƙawata filin shaƙatawar. Ana kwashe dukkan dattin da ke yankin, sannan an saka liluna don shaƙatawar yara.

Matasan Matsare na daukar matakai da hannayensu wajen bayar da gudunmawar yaƙi da sauyin yanayi.

Gwagwarmayar ta yadu

A tsallaken iyakar Uganda, wani mutum da yara kanana na yankin suka baiwa lakabin "Janaral din Bishiyu", na shirin gudanar da taron shekara na wata cibiya da ya kafa don wayar da kan jama'a.

Joseph Masembe, mai fafutuka na karbar bakuncin yara kanana a Bukin Kyautata Yanayu, inda yake koya musu muhimmancin shuka bishiyoyi.

Shirinsa, mai taken "Kananan Hannaye Sun Zama Kwarra", ya shahara a tsakanin yara da suke kwashe tsawon rana suna wasa da rawa kafin daga baya su koma gida da 'ya'yan itatuwar bishiyoyin.

Masembe ya shaida wa TRT Afirka cewa "Na fara wannan yunƙuri mai sauki a 2012 da manufar ganin na sanya kowanne yaro na Uganda ya dasa bishiya aƙalla guda ɗaya."

"Mayar da hankali kan bishiyoyin kayan marmari shi ne saboda amfaninsu ga jiki. A tsohuwar al'adar Afirka, da wahala ka samu mutum ya sare bishiyar kayan marmari, muna son dawo da wannan al'ada ta hanyar ƙarfafa gwiwar yara so nuna kauna ga bishiyu."

Somalia na daga kasashen Afirka da mummunar ambaliya ta shafa a 2023. Hoto: AA

Shekaru 11 bayan fara wannan gangami, Masembe ya kai gangamin ga makarantun firamare a fadin kasar.

"Batun kare muhalli ya ta'alaka ga yara kanana saboda za su fi mu daɗewa a raye a nan gaba," in ji shi.

Yarjejeniyar Nairobi

Wanja da masembe na daga cikin tawagar masu fafutuka da suka mayar da hankali kan cewa shugabannin Afirka su cika alkawarurrukan da suka sanya hannu a kai a wajen Taron Sauyin Yanayi na Afirka da aka gudanar a tsakanin 4 da 6 ga Satumba 2023.

A karshen taron an fitar da sanarwar cewa duniya na bukatar sake zage damtse don komaw akan turba don tabbatar da dumin duniya kan 1.5°C kamar yadda aka amince a taron Paris a 2015.

Wani babban kalubale kuma shi ne dole ne a rage yawan fitar da iskar carbon a duniya da kaso 43 a wadannan shekaru goman.

Taron ya yi tsokaci da cewa duk da yadda nahiyar ke da kasho 40 na albarkatun samar da makamashi mai sabuntuwa a duniya, dala biliyan 60, kaso biyu kawai na dala tiriliyan uku da aka ware don zuba jari a fannin samar da makamshi mai sabuntuwa ne ya zo Afirka.

Yarjejeniyar Nairobi ta ce "Muna kira ga shugabannin duniya da su amince da tsarin raba tattalin arzikin duniya da iskar carbon, wanda dama ce ta bayar da gudunmawa ga daidaito da jin dadin kowanne bangare."

Afirka na fitar da kasa da kaso 4 na iskar carbon amma ita ce ta fi illatuwa da tasirin sauyin yanayi. Hoto: AP

Ma'anar raba kasashe da iskar caebon na nufin daina amfani da makamashi irin su man fetur da iskar gas da kwal, a koma amfani da makamashi mai sabuntuwa da ba ya fitar da iskar carbon.

Sanarwar Bayan Taro ta Nairobi ta bayyana cewa shirin mayar da duniya mai amfani da carbon kadan na bukatar zuba jarin dala tiriliyan huɗu zuwa dala tiriliyan shida a shekara.

Samun damar mika wadannan kudade na nufin a sauya fasalin ta'ammali da kudade, inda gwamnatoci da manyan bakunan kasashe da bankunan 'yan kasuwa da masu zuba jari da sauran masu ruwa da tsaki a fannin tattalin arziki za su hada hannu waje guda.

"Kudaden da Kasa ke samu sun ta'allaka ga me aka gani a kasa; batu ne na kadarori da tsabar kudade.

"Muna da wuraren zuke iskar carbon, muna tsaftace muhallanmu, mun zama masu shanye iskar carbon da wasu ke fitarwa, amma ba ma smaun komai daga hakan, ba ma gani a kasa." in ji shugaban kasar Kenya William Ruto, yayin jawabi ga taron.

"Domin cimma wannan buri muna bukatar kawo sabon tsarin zuba jari da damarmakin kudade, musamman ga makamashi mai sabuntuwa, mun yarda da lokaci ya yi da za a tattauna kan harajin fitar da iskar carbon."

Kwararru na cewa dazukan Afirka na zuke tan miliyan 600 na iskar carbon a shekara, sama da duk wani daji a duniya.

Kenya, ta yi kira da babbar murya, ta wata Dokar Sauyin Yanayi ta 2023 a Satumba, wada ta ba ta damar kafa hukumar magance iskar carbon tare da nada jagororinta.

"Ba mu bai wa kowa ko da taki daya na fili ba. Muna kan kammala samar da dokokin da za su kula da su," in ji Shugaba Ruto a wajen Taron Sauyin Yanayi na COP 28 da aka gudanar a Dubai.

"Muna samar da dokoki don kawo tsafta da nagarta kan batun iskar carbon da harajinta, kasuwanci da kasuwanninta. Muna son tabbatar da an samu nagarta sosai."

An rawaito Bankin Duniya na goyon bayan Afirka don samar da dokoki kan iskar carbon.

Kudin shigar iskar carbon

A Kenya, wasu matasa da suke aikin tsfatace tafkin Nairobi na bibiyar Sanarwar Bayan Taron Nairobi.

Taron Sauyin Yanayi na Afirka a Nairobi ya ja hankalin masu fafutuka da ke neman a dauki matakai. Hoto: TRT Afrika

Humprey Omukuti ya jagoranci kokarin gyara wani bangare na wannan Kogi na Nairobi inda Wanja da sauran matasa da suke ta yunkurin tabbatar da Mathare ya ci gaba da zama mai dauke da korran bishiyu.

Kungiyar da ake kira Manoman Karkara, na da ra'ayin cewa shuka bishiyar bamboo a gabar tafkin zai taimaka wajen hana gurbacewar muhalli.

Omukuti ya shaidawa TRT Afirka cewa "Ina bibiyar shugabanninmu sosai da yadda suke aiki da sanarwar taron na watan Satumba, kuma yana da sha'awar mayar da hankali kan yadda za su mayar da hankali su yaki iskar carbon mai lahani ga muhalli."

Ya yi amanna da cewa akwai dan rudani tare da hakan saboda ya shafi shuka bishiyu.

"Tambayarmu guda daya ita ce ko kudaden da gwamnatocinmu na Afirka suke samu na harajin iskar carbon za su dinga isa ga kungiyoyin irin namu da kw agwagwarmayar shuga bishiyu," in ji Omukuti.

"A dukkan wadannan birane na Afirka, akwai matasa da dama da ba su da ayyukan yi; me ya sa ba za a karbi wadannan kudade, a ba su ta yadda za a kara yawan bishiyun da ake shukawa ba?

"Hakan zai sa kowanne bangare ya amfana, saboda za a bawa matasan aiki kuma kasar za ta samu karin kwarran shuke-shuke."

Ra'ayi mafi rinjaye a tsakanin masu wannan aiki irin su Omukuti shi ne cewa mafi yawancin shugabannin na tsammanin kungiyoyin sa kai su yi aikin inganta muhalli su kadai.

Omukuti ya ce "Suna bayar da kudade ga manyan kamfanoni, maimakon tallafa mana mu yaki wannan matsala.

"Wannan nahiyarmu ce, kuma za mu so mu zama wani bangare na ayyukan yaki da sauyin yanayi, amma kuma ta hanya mafi girmamawa da inganci."

Yana da ra'ayin abu mafi muhimmanci shi ne tabbatar da Kudirin da Aka Cimma a Nairobi ya yi aiki a dukkan Afirka.

TRT Afrika