Daga Firmain Eric Mbadinga
Ranar 13 ga Satumban 1958, ta kasance daya daga lokuta mafiya muni a tarihin Kamaru, da sauran yankunan Afirka bayan mulkin mallaka.
Suna cewa lokaci na warkar da ciwuka, amma sakon dan shekara 66 bi yi wani tasiri sosai ba wajen hade kan kasar da sojojin Faransa a wancan lokacin suka rusa ta.
Babban abu mafi muni shi ne kisan gillar da aka yi wa Ruben, a lokacin yana da shekaru 45 kuma yana Sakatare Janar na Kungiyar Jama'ar Kamaru (UPC).
Nyobe ya buya a dajin da ke kusa da kauyensu Song Mpeck da ke tsakiyar Kmaru a lokacin da ya tsira daga alburasa da ake harba masa saboda ya yi kira ga 'yan mulkin mallaka na Faransa su bar kasar tare da 'yanta Kamaru.
A wani matakin ramuwa bayar da misalin hukunci kan irin mai tawaye kamar wannan, inda wadanda a karhe suka kashe shi, sun ja gangar jikinsa da ta ha harbi a cikin tabo zuwa kauyen Liyong mai makotaka da nasu kauyen.
Tsawon shekaru da suka wuce an binne akidun Um Nyobe tare da shi a wani kabari da ba a yi masa alama ba.
Har sai a shekarar 1991, shekaru 33 bayan mutuwar sa, aka yi dokar da ta bayar da damar amfani da sunansa wajen tuna ranar kwatar 'yancin kai ta Kamaru.
Wannan Jumhuriya da ke da mutane kusan miliyan 29, inda rabin jama'arta a yanzu ba a haife su ba a wancan lokacin, suna gwagwarmaya su tabbatar da kima da darajar Um Nyobe ta hanyar nuna yadda rayuwarsa ta kasance.
Sadaukarwa da gwagwarmaya
Jean Baptiste Ketchateng , dan jaridar Kamaru, na bayyana ayyukan Um Nyobe a matsayin kishiyar tsanani a yayin da yake bukatar samar da hadin kai, 'yancin kai da adalci a tsakanin 'yan kasa.
"Shi da abokansa na wannan lokacin na a ra'ayi iri guda. Su sdaukar da dukkan rayuwarsu don kasar ta samu 'yanci tare da inganta, 'yantar da 'yan Afirka da ake yi wa mulkin mallaka da 'yan adam baki daya. Sakamoon da suka samu shi ne kora, rikici da kisa," ya fada wa TRT Afirka.
Um Nyobe ba lallai ne ya amfana da zuba jrin da ya yi wajen ganin an kafa kasa mai adalci, 'yanci ga kasarsa, amma wannan gwagwarmaya ta sadaukar da kai da ya yi ta ta samar da kishin kasa mai karfi a tsakanin 1950 da 1971, ba a Kamaru kawai ba har ma a dukkan Afirka.
Masanin tarihi dan kasar Kamaru kuma malami mai bincike Achille Mbembe na da ra'ayin cewa yakin kwatar 'yanci da samun mulkin kai na jama'ar Afirka, kamar yadda aka gani a tare da Um Nyobe, na da amfani har a wannan zamanin.
Mbembe ya kara da cewa "Har yanzu ba mu fara tsirurutar madarar ayyukan nasu. Na tabbata cewa lokaci zai zo. Sannan ne za mu gano asalin jin dadin gagwarmayar sa, taurin kan sa, manufar da yake fada da 'yacin dabi'u, hanyarsa ta hada tunani da rayuwa waje guda, da kum fita a hadu da duniya baki daya."
Farkon rayuwa da gwagwarmaya
Um Nyobe ya fara rayuwarsa ne da gwagwarmaya a yankin kudancin Kamaru, yankin da ya kasance a karkahin mulkin mallakar Jamusawa a tsakanin 1884 da 1916, inda har zuwa 1960 kuma ya kasance a karkashin Turawan mulkin mallaka na Faransa.
Batun sanin kai, adalci da kyautatuwar zamantakewa ne suka zama jgon gwagwarmayarsa.
Bayan ya kammala karatunsa. Um Nyobe ya shiga aikin gwamnati a lokacin mulkin mallaka, inda ya samu kwarewa lamba daya kan irin rashin adalcin da jama'arsa ke fuskanta.
Ketchateng ya yi tsokaci da cewa abubuwan farko da Nyobe ya fara samun kwarewa a kai na d ayawa ciki har da aiki a matsayin sakataren kotu, wanda ya sanya shi fahinmtar wahalhalun da ake fuskanta daga mulkin mallaka, ya kuma sake habaka ilinsa na sanin dokoki.
"Ya shugabanci kungiyar 'yan kwadago ta kasar ta farko, wadda aka kafa bayan 'yakin duniya na biyu a Kamaru. Ya wakilci Kamaru a lokacin tana karkashin mulkin mallakar Jamus a wajen babban taron da ya samar da Gwagwarmayar 'Yancin Dimokuradiyyar Afirka, wand daga baya faransa ta karfe da amfana da shi." in ji Ketchateng.
Um Nyobe ya kuma shiga gwagwarmayar neman inganta rayuwar jama'a, ciki har da gwagwarmayar adawa da kara wa'adin zaman 'yan mulkin mallakar Jamus a kasar.
A 1947, shi da abokan gwagwarmayarsa sun kirkiri jam'iyyar siyasa ta farko a kasar ta RS, wadda 'yan mulkin mallaka na Faransa suka rushe ta ba da jima wa ba.
Bayan nuna rashin tsoro, bayan shekara guda sun sake kafa jam'iyyar UPC, sun dinga kokarin wayar da kan jama'a don nuna adawa da mulkin mallaka. Jam'iyyar ta fadada ayyukanta zuwa ga arewacin kasa da yake karkashin mulkin Turawan Ingila.
A watan Yulin 1955, 'yan mulkin mallakar Birtaniya da Faransa sun haramta dukkan ayyukan jam'iyyar.
Murmushin karshe
Bayan ja da zuwa sashen Nyong-et-Kelle da magoya bayansa, Um Nyobe ya kafa Dakarun Kwatar 'Yancin Kai na Kamaru (ALNK), wanda suke dauke da makamai.
Girmamar da suka yi ya sanya Turawan faransa 'yan mulkin mallaka kara yawan farautar masu gwagwarmayar kwatar 'yancin kai.
Tun bayan amincewa da Doka mai lamba 91/022 a ranar 16 ga Disamban 1991, wadda ta janye haramcin tuna wa da Um Nyobe - Kamaru ta fara ayyukan sanya shi a sahun gaba a tarihinta.
"Mafi yawan 'yan kasarmu ta Kamaru da ma na Afirka baki daya ba su san waye Um Nyobe ba. Wasu ne suka yi amfani da mutuwar sa wajen juya ma'anar ayyukan da ya yi, inda suke nuna sabanin gwagwarmayar da ya yi a kasar ta neman 'yancin kai.|" Ketchateng ya fada wa TRT Afirka.
Mbembe, wanda rubututtukan da ya yi suke karin haske game da tirjiyar 'yan Kamaru ga 'yan mulkin mallaka, na daga cikin ayyukan da suka kawar da mummunar fahimtar da aka yi wa Um Nyobe.
Littafinsa na 1996 'La naissance du maquis dans le Sud-Canmeroon, 1920-1960: histoire des usages de la raison en colonie' ya taka rawa sosai a wannan kokari da aka yi.
A 2007, an girke gunkinsa a garin Eseka na tsakiyar Kamaru don girmama shi da tuna wa da shi.
Ya zuwa yau, Faransa ba ta amince tana da hannu a kisan gillar da aka yi wa Um Nyobe ba. Sai dai ma akasin haka, gwamnatin mulkin mallaka na dora laifin rikicin da ya kai ga kashe shi kan UPC.