Daga Dayo Yussuf
Tushen al'adun karimci na Tanzaniya shi ne "ubuntu", tsohuwar kalmar Afirka da take nufin "nuna jinƙai ga ɗan'adam" wanda ke kwatanta falsafar Mwalimu Julius Nyerere da ya yi wa ƙasar da ya kafa.
Wannan ƙa'idar jagora ta fi dacewa da kalmar Swahili "karibu" - ma'ana "maraba" - da ake yawan amfani da ita a harkokin kasuwanci da ayyuka a Tanzaniya.
A duk wani shingen binciken kan iyaka, baƙo zai iya sa ran za a gaishe shi da murmushi na gaske da tausasawa wanda nan take ya bambanta wannan ƙasa ta Gabashin Afirka da ke kusa da Dutsen Kilimanjaro da sauran shahararrun wuraren yawon buɗe ido.
Bayan da yankin Tanganyika ya samu 'yancin kai daga Biritaniya a shekara ta 1961, Mwalimu Nyerere abin da ya sa a gaba shi ne maido da tsarin 'yan'uwantaka na Afirka da ake ganin kamar mulkin mallaka ya rusa.
Mafarkin haɗin kan 'yan Tanzaniya don yin aiki tare don gina al'ummarsu shi ya share fagen samun "ujamaa," tsarin jin dadin gurguzu da aka inganta wanda ke da nufin ci gaba da lalata tsarin jari-hujja tare da tabbatar da kwanciyar hankali na ci gaba.
Ta'azzara neman dogaro da kai
Wasu ƙwararrun sun yi imanin cewa neman samun ƙasa mai walwala ya daƙusar da ƙoƙarin da al'adar da tsofaffi suka fi sabawa da ita a Tanzaniya.
Agnes Kinyua, wacce ke koyar da tarihi a Jami'ar Daystar da ke Nairobi a Kenya ta shaida wa TRT Afrika cewa "Idan ka dubi tsarin jari-hujja, ya shafi harkokin kasuwanci ne. Da zarar ka yi, za ka samu. Kuma abin da ka samu naka ne. Jama'a suna da ƙwarin gwiwa saboda akwai lada da ake jira a samu a kowane kokari."
"A gefe guda kuma, shi kuwa tsarin guruguzu ana nufin yin aiki tare da raba wahala da ladan. Matsalar ita ce yadda hakan ke sa wasu yin tunanin, 'Ko da ban yi aiki ba, zan samu na cin abinci'. Tsarin yana haifar da lalaci."
Tanzania babbar kasa ce mai fadin murabba'in kilomita 947,300. An albarkace ta da ƙasa mai albarka da albarkatun ƙasa kamar ma'adanai.
"Tanzaniya a tarihi tana da abubuwa da yawa da za ta amfana da su. Bayan samun 'yancin kai, ana iya buƙatar wani nau'i na jari hujja," in ji Agnes, duk da cewa an yi taka tsantsan don kada a yi shakkar tushen falsafar Mwalimu Nyerere.
Babbar gardama game da gurguzu ita ce cewa 'yan kasa ba sa ƙara ƙoƙarin ganin sun yi aiki tuƙuru don amfanin ƙasar da al'ummarta.
“Mutane sun dogara ga ƙasar, kuma da yawa ba sa ƙoƙarin saka hannun jari ko aiki tuƙuru,” in ji Agnes.
Nuna wariya a yanki
Makwabtanta su Kenya da Uganda, wadanda suka sami 'yancin kai a lokaci ɗaya da Tanzaniya, sun ɗaɓɓaka zuba jari a matsayin tagwayen ginshikan ci gaba.
Dukansu sun sami damar haɓaka tattalin arziƙinsu cikin sauri da jawo hankalin masu zuba jari daga waje da yawa, saboda gasar kasuwanci ta ba kowa damar taka rawa don samun wadata.
Don haka, shin tsarin gurguzu a Tanzaniya bai sami fa'ida ta wani abu daban ba? Bayan haka, shin har yanzu ba ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe mafi kwanciyar hankali a siyasance da zaman lafiya a nahiyar ba?
Masana tarihi da masana tattalin arziki suna jayayya cewa gurguzanci ba zai ɗore ba, suna ba da misalai da ƙasashen duniya waɗanda durƙushewa saboda kura-kuran da ke tattare da shi.
"Tsohuwar Tarayyar Sabiyet na bin tsarin gurguzu. Har yanzu Koriya ta Arewa mai ra'ayin gurguzu ce, duk da cewa ana kallonta a matsayin kurkuku da ta zama mallakin dangin Kim Jong Un. Ba za a iya fita daga kasar ba, kuma babu wanda ya san abin da ke faruwa a can," Agnes ta shaida wa TRT Hausa .
Duk da haka, wasu ƙasashe sun sami hanyar haɗa tsarinsu da gurguzu don samun ci gaba ba tare da inganta tsarin jari-hujja ba.
"China tana bin tsarin kwaminisanci na zamantakewa, gurguzu na tattalin arziki da gurguzu na siyasa. Amma a shekarar 1990, sun canza manufofin tattalin arziki kawai. A fannin zamantakewa, har yanzu 'yan gurguzu ne. Kuma ku dubi matakin da tattalin arzikin China ya kai," in ji Agnes.
Alamomin gurguzu
Ko da yake aƙidar gurguzu a Tanzaniya ta samo asali, har yanzu akwai alamun tsohon tsarin.
"A tarihi, yawancin juyin halitta yana zuwa ta hanyar sauyi na tsararraki. Sabbin 'yan zamani ba sa jin cewa ya zama tilas su bin sawun magabata," in ji Agnes.
"A Tanzaniya, tsarin karatun makarantu na duniya ne. A bayyane yake cewa tushen tsarin gurguzu bai ƙare ba, amma yakan yi rauni yayin da matasa ke jin kasancewarsu."
Batun yaushe ya dace Tanzaniya ta manta da tsarin gurguzu abu ne da har yanzu ake muhawara a kansa.
Yayin da wasu ke nuna shakku game da kwanciyar hankali da tafiyar hawainiya na rayuwa a baya, wasu na jayayya cewa lokaci ya yi da za a yi la'akari da tsarin gurguzu da ya bambanta da jagoranci da hangen nesa na Mwalimu Nyerere, wanda ke ci gaba da samun karbuwa ba kawai a Tanzaniya ba har ma a fadin nahiyar da sauran sassan duniya.