Cibiyar Taro ta WOW ta zamani ta Istanbul tana cike da kyakkyawan fata yayin da shugabannin 'yan kasuwa na Afirka da masana'antun Turkiyya suka hallara a wurin don taron 12-13 ga Fabrairu na dandalin hadin gwiwar masana'antu na duniya (WIC Forum).
Taron mai taken "Karfafa hadin gwiwa tare da Afirka, makoma mai dorewa", ya nuna tsarin jagorar dangantakar da ke tsakanin Turkiyya da nahiya ta biyu mafi girma a duniya - kudurin cigaban juna da hadin gwiwa bisa manufar raya kasa tare.
Tawagogin gwamnati daga Turkiyya da na kasashen Afirka sun taka rawar a zo a gani a yayin tattaunawar da aka yi tsakanin masana'antun da shugabannin 'yan kasuwa kan hanyoyin bunkasa hadin gwiwa da cin moriyar juna.
Habakar cinikayya
Mataimakin ministan kasuwanci na Turkiyya Sezai Uçarmak, ya sanya burin kasarsa a mahanga ta hanyar kwatanta kwarin gwiwar cigaban kasuwanci da nahiyar - daga dalar Amurka biliyan 5 shekaru 20 da suka gabata zuwa dala biliyan 37 a karshe - tare da yuwuwar samun ci gaba mai ban mamaki.
Wannan adadi bai da yawa idan aka yi la'akari da yadda muke magana kan kasae da ke kan gaba a yankinta kamar Turkiyya da kuma nahiya kamar Afirka, wacce ke da matsayi na biyu mafi girma a fannin kasa da yawan al'umma a duniya," in ji shi, wanda hakan ya sa ake sa ran a samu bunkasar kasuwanci tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka a nan gaba.
Taron ya baje kolin kayayyakin da Turkiyya ke ƙerawa, da fasahohin zamani, da masu samar da hidimomi iri-iri, da bai wa ‘yan kasuwan Afirka damar gano kayayyaki da abubuwan da za su taimaka wajen fadada kasuwancinsu ta hanyar yarjejeniyar hadin gwiwa.
Burin hadin kai
Kamar yadda masana'antun ke yin hulɗa tare da abokan kasuwancin Afirka na gaba, haɓaka tattaunawa da nufin tabbatar da yarjejeniyar kasuwanci, abin da ya faru shi ne muhimmancin dandalin WIC a matsayin mai taimakawa wajen samar da cigaba.
Mahalarta taron na kwanaki biyu - daga jami'an gwamnati har zuwa 'yan kasuwa - sun nuna kwarin gwiwa cewa taron zai karfafa alakar da ke tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka.

Dr Souleymane Touré, ministan gundumar Zanzan mai cin gashin kansa a Cote d'Ivoire, ya yi imanin cewa cigaba da yin hadin gwiwa da Turkiyya shi ne abin da nahiyar ke bukata don gane karfinta.
"Afirka gida ne ga yawan al'ummar a duniya masu ƙarancin shekaru. Fadin ƙasarta ya kai murabba'in kilomita miliyan 30.37, cike taf da albarkatun kasa. Nahiyar na ci gaba da kasancewa a bude don samun nasara a hadin gwiwa da mutunta juna ga al'adu da hakikanin siyasa," in ji Dr Touré.
"Mun yi imanin cewa, Turkiyya, tare da fasaharta ta zamani, na iya taimaka mana wajen bunkasa ci gabanmu da kuma tafiya cikin sauri ta hanyar bin zamani don cim ma burinmu na ci gaba."
Ministan zuba jari da hadin gwiwar kasa da kasa na kasar Sudan Ahlam Mehdi Sabil, ya ja hankali game da damar zuba jari da Sudan ke samu a fannin noma da masana'antu.
"Za mu iya ba da gudunmawa ga dabarun noma da samar da abinci na Turkiyya tare da manyan wuraren noma da albarkatun kasa," in ji shi.
Bunkasar sana'o'i
Bayan muradun ƙasa, mutane da dama da ke kasuwanci a karan-kansu sun samu halartar taron.
Moubinou Ademola Gafari, dan kasuwa daga Jamhuriyar Benin, ya ce yana neman hadin gwiwa a bangarori daban-daban.
"Na zo Istanbul ne domin samun kyakkyawar huldar kasuwanci, kasuwanni masu tasowa, da damarmaki a fannonin da nake aiki da su," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.

"Ina nan tare da abokan aikina don nemo kayayyakin da za su iya samun riba a fannoni daban-daban na Benin. Ina mai da hankali kan harkar masaka yayin da abokan aikina ke aiki a wasu fannoni kamar motoci, gine-gine da ayyukan jama'a."
Armand Yandoka daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda ya saba zuwa dandalin WIC, ya bayyana nasarorin da ya samu.
"Na san cewa wannan dandalin yana ba da damarmakin kasuwanci ga 'yan Afirka. Nakan samo sabbin abokan aiki da abokan kasuwanci a kowace tafiya," in ji shi.
"A bara, na sanya hannu kan kwangila a masana'antar kebul. A wannan karon, ina duba kayan aiki da fasahohin masana'antar gine-gine. Ina shirin komawa karo na gaba don duba kayan kwalliya."
Masu shirya taron WIC karo na 12 sun yi niyya don sauƙaƙe hulɗa kai tsaye tsakanin furodusoshi da masu saye, tare da kawar da masu shiga tsakani.
Mahalarta irinsu Fatma Sedek daga Sudan sun shaida irin tasirin da Turkiyya ta bayar a fagen kasuwanci a Afirka.
"Na lura cewa yawancin 'yan kasuwar Sudan da ke halartar taron na iya tattaunawa da Turkanci. A bayyane yake cewa sun gina harsashin kasuwanci a nan," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
Wasu suna ganin taron a matsayin damar bunƙasa. "Mun zo nan ne domin mu inganta manufofinmu na saka hannun jari, muna son 'yan kasuwar Turkiyya su bi mu har zuwa cim ma burin ƙasarmu," in ji Christopher Mogou daga Kamaru.