Gwamnatin Somalia ta kaddamar da wani shirin sake tsugunar da 'yan gudun hijira sama da miliyan ɗaya Hoto: reuters / Photo: Reuters

Daga Hinda Abdi Mohamoud

Yayin da fari da ambaliyar ruwa da kuma tashe-tashen hankali da suka ƙi suka ƙi cinyewa ke ci gaba da ɗaiɗaita al'ummar Somalia, mutane masu yawa na tseren wa zuwa bayan garin birane, musamman babban birnin Mogadishu.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi ƙiyasin cewa, a faɗin duniya, ƙarin mutane za su zauna a garuruwa da birane ba fiye da a kauyuka zuwa shekarar 2026. An ce Mogadishu shi ne birni mafi saurin bunƙasa na biyu a duniya, galibi saboda yawaitar tuɗaɗowar 'yan gudun hijira, waɗanda kashi 79 daga cikinsu mata da ƙananan yara ne.

A cewar wani rahoton Ƙungiya Mai Zaman Kanta Refugee International, galibin miliyoyin mutanen da ke tserewa daga yankunan karkara zuwa birane a Somalia ba za su taɓa komawa gida ba, yanzu ko ma nan gaba. Wasunsu suna zaune a sansanonin wucin gadi tsawon sama da shekaru talatin.

Da yawa daga cikin 'yan gudun hijira na cikin gida (IDPs) su miliyan 4.3 a cikin ƙasar dole su nemi sababbin hanyoyin da za su rayu. Da yawansu sun rayu a matsayin manoma da makiyaya. Sana'o'isu ba su dace da rayuwar birni ba. Saboda haka, dole su nemi wata sana'ar daban.

Fatima Mohamed lise mai shekaru talatin da ɗaya ta zo sansanin 'yan gudun hijira na Asal tare da 'ya'yanta bakwai a watan Yuni shekarar 2023. Sansanin shi ne matsugunin iyalai kimanin 800 kuma ɗaya ne daga cikin sababbin unguwanni da aka kafa a bayan garin Mogadishu.

Kafin ambaliyar ruwan, Somalia ta fuskanci barazanar farinta mafi muni a cikin shekaru 40. Hoto / Reuters

Ta tsere ne daga gundumar Qoryoley a yankin Lower Shabelle na kudancin Somalia bayan fari ya halaka duk dabbobinta. Mijinta ya zauna don ya lura da gidansu da kuma 'yan kayayyakinsu da suka saura.

Aiki a shagunan sayar da abinci

"Mun samu kyakkyawar rayuwa a matsayinmu na makiyaya. Muna da shanu kimanin 40", ta faɗa. Yanzu ba mu da ko da guda ɗaya. Saboda haka ba ni da zaɓi illa na zo Mogadishu tare da 'ya'yana."

Babu wani tallafin jin ƙai da za a bai wa lisa da iyalinta da ta isa sansanin Asal. Sai ta tsorata saboda ba ta san yadda za ta ciyar da kanta ko 'ya'yanta ba. Sauran matan da suka riga ta zuwa sansanin sun shawarce ta ta je unguwanni masu makwabtaka ta nemi aiki.

"Ni da 'yata 'yar shekara tara da haihuwa muna fita da sassafe kullum domin neman aiki," kamar yadda take cewa. "Ayyukan kaɗai da muke iya samu sune na wankau da sharar wuraren da ake gine-gine inda ake biyan tsakanin $1 da $1.50 a yini. Wannan bai isa ya ɗauki ɗawainiyar muhimman abubuwa ba, amma fa ya fi babu."

"Sana'o'in karkara kaɗai muka iya kuma babu mai buƙatar su a birni."

Wasu da ba jami'an gwamnati ba ne, da ake wa laƙabi da "masu gadi" su ne ke kula Da sansanonin bayan birnin Mogadishu, kuma su ne ke shiga tsakanin mazauna sansanonin da mutanen waje.

Mazauna sansanin Asal ba su da wata sana'a takamaimiya guda ɗaya. Kamar lise da 'yarta, kowace safiya sai sun fita neman aiki. Nau'in ayyukan da mata kan samu sune share gidajen jama'a, da yi musu wankau da kuma wanke-wanke a shagunan abinci.

Yara na fara aiki ne tun suna 'yan shekaru huɗu ko biyar da haihuwa. Ƙananan yara mata suna wanke-wanke, maza kuma na wanke takalmi ko aiki a shagunan abinci.

'Yan kuɗaɗen da suke samu, tsakanin $1 da $2 a yini idan sun samu aikin da suka yi, shi ke dauwamar da su cikin talauci.

Zarce tunani

"Ina amfani da kuɗin da na samo na sayi shinkafa da wake ko masara. Sau ɗaya tal muke cin abinci a rana lokacin cin abincin rana," a cewar lise. Sauran lokacin sai mu sha shayi. Ni da 'ya'yana muna kwanciya ba mu ci komai ba."

Kamar sauran mata 'yan gudun hijira, lise tana fuskantar ƙalubalen da aka saba na cin zarafi daga maza, musamman jami'an tsaro, da masu kula da sansanoni da kuma wasu da suke da wasu muƙamai na hukuma.

Galibin matsugunai a sansanonin da itatuwa da ledoji aka yi su, kuma da yawa daga cikin ƴan gudun hijirar ba su da suturu masu kyau. Yawancin lokaci mata na neman mata da ƴan mata da lalata su kuma sai su ba su abinci da aikin yi.

"Maza na zuwa wajena da sunan za su taimake ni na samu wani aiki ko na samu abinci," a cewar lise. "Daga nan kuma, sai su ce suna son na rama wa kura aniyarta."

Hawa (ba asalin sunanta ba ne) ƴar shekaru saba'in da haihuwa da kuma jikarta ƴar shekaru uku da haihuwa sun kwashe watanni bakwai suna zaune a sansanin Asal. Lokacin da ta fara zuwa, tana ɗaya daga cikin mutane ƙalilan masu sa'a da suka samu ƴan wasu agajin jin ƙai.

Amma an dena ba ta agajin a watan Mayu bayan ta ƙi amincewa da buƙatar lalata daga ɗaya daga cikin mutanen da ke kula da sansanin kuma yake saka ido kan yadda ake raba kayan agaji.

"Lamuran rayuwata a yanzu sun zarce tunanin kowa. Abu mai wuya ne a yarda da dalilin da ya sa yanzu ba a ba ni tallafin abinci amma hakan ne gaskiya."

Rayuwar kiwo ta taɓarɓare

"Mai kula da sansanin ya buƙace ni da na aikata wasu abubuwan rashin kamun kai idan ina son abinci," inji Hawa. Na kaɗu kuma cikin fushi, na ƙi amincewa da buƙatarsa. Tun daga wannan lokacin ba a sake ba ni ko da ƙwayar hatsi ba.

Hawa ta ce akwai batutuwa da dama masu kama da nata. "Abin takaici ne," a cewarta.

"Yanayin ya fi kyau ga 'yan gudun hijira masu aikatau a gidajen mutane saboda mata ne ke zama a gida yayin da maza ke tafiya aiki," Hawa ta ce.

"Masu ba mu aiki da suka fi kyautata mana su ne mata tsofaffi. A wasu lokutan suna ƙara mana kuɗi,"

Yanzu da ba ta samun kayan agaji, Hawa na barin sansanin kowace safiya ta nemi aikin shara a wuraren da ake gine-gine da kuma a shagunan sayar da abinci. Wani lokaci takan yi wankau a gidajen da ke unguwannin da ke kusa.

Takan tafi aiki tare da jikarta. Wasu lokuta, tana barin ta a wajen sauran mata a Asal.

Ɗaya daga cikin matan da suka fi tagayyara a sansanin ita ce S’iido Hassan Moalim. Dole ta yi watsi da rayuwarta ta kiwo a gundumar Kuntuwaarey a Lower Shabelle bayan fari ya busar da ƙasa kuma ya halaka duka dabbobinta. Moalim ba ta yi aure ba kuma ba ta taɓa haihuwa ba. Shekarunta sittin da shida da haihuwa kuma ba ta gani.

Wankau

"Ni ɗaya nake rayuwa a nan," inji Moalim. "Na yi imani na fi kowa talauci a wannan sansanin. Ba na gani, ba zan iya aiki ba kuma ban samu katin shaidar karɓar tallafin abinci ba."

Wani lokaci maƙwabtan Moalim sukan ɗan sam mata ɗan abin da suke da shi amma galibin lokaci ba ta da komai. "Mai rauni ba shi da wani 'yanci," ta faɗa.

Lisho Mukhtar Adam ta zo sansanin Asal a ƙarshen watan Yunin 2023 bayan rikici a gundumar Kuntuwaarey ya tilasta mata tserewa daga gidanta tare da 'ya'yanta maza uku. Ta fara aiki a matsayin mai shara da wankau sannan ta ƙoƙarta ta saya wa 'ya'yanta abinci da kuɗin da ta samu.

Ta ce "ina wanke suturu sannan na share gidajen mutanen da suka fi ni ƙarfi. Ina samun tsakanin $1 da $2 a rana. Ina aiki lokaci mai tsawo don na iya kula da iyalina gwargwadon yadda zan iya."

Adam ta bayyana yadda wani lokaci 'yan gudun hijira masu aikatau a gidajen mutane kan sha duka a hannun masu gidansu, waɗanda wani lokaci sukan zarge su da sace musu kaya.

"Idan muka gama aiki, wasu mutanen na cewa ba su da kuɗin da za su biya mu sai dai mu dawo washegari mu karɓa," ta bayyana. Wasu ma ba sa taɓa biyan mu kwatakwata. Ba sa ganinmu da daraja. Galibin masu ɗaukar mu aiki suna mana kallon ƙasƙanci amma wasu waɗanda suke da ilimi suna ganin ƙimarmu."

Tana cewa ɗaukin da suke samu kaɗan ne. 'Yan sanda suna shagaltuwa da magance barazanar tsaro a Mogadishu da 'yan ta'addan Al Shabab ke yi.

"Babu mai sauraron mu," inji Adam. "Abin da kawai za mu iya yi shi ne mu sanar da manema labarai game da halin da muke ciki kuma mu yi fatan wani da ke da iko da alfarmar yin hakan zai taimake mu," tana roƙo.

"Galibin mutane sun yi gum da bakinsu game da batun saboda sun san idan suka yi ƙorafi za a kore su daga sansanin."

'Ina so na kafa Kasuwanci'

Mutanen da ke rayuwa a ɗaya daga cikin sansanin 'yan gudun hijira mafi daɗewa a Mogadishu da ake kira Allah dhowr suna fuskantar matsaloli makamantan na mutanen Asal.

Rahma Mohamed ta isa can tare da mijinta da 'ya'yanta huɗu a watan Janairu na shekarar 2022 bayan fari ya halaka dabbobin iyalin a gundumar Kuntuwaarey ta kudancin Somalia.

Kullum Rahma da mijinta za su tashi da wuri su taka zuwa unguwanni maƙwabta domin neman aiki. Suna barin 'ya'yansu a hannun abokanan zamansu a sansanin.

"Sau tari mutanen da nake yi wa aiki suna biya na ƙasa da adadin kuɗin da muka shirya," tana cewa. Za mu iya shiryawa kan $5 amma a ƙarshe sai su biya ni $3 kacal.

Duk da tarin ƙalubale a Mogadishu, Rahma ba ta da niyyar barin garin.

Duk da kallon 'yar gudun hijira da mutane suke mani, ina so na kafa Kasuwancina a nan domin na kula da iyalina.

Asmo Abdi Farah Ahmed 'yar shekara 15 da haihuwa ta halarci makarantar karatun Alkur'ani mai girma a gundumar Mushaan kafin fari ya tilasta mata ta gudu zuwa Mogadishu a shekarar 2023. Yanzu tana aiki tare da mahaifiyarta a matsayin 'yar aikatau da wankau.

"Yaran unguwanni masu makwabtaka da sansaninmu suna halartar makaranta kuma suna wasa tare," ta ce. Wani lokaci suna tsokana ta don ba na zuwa makaranta. Sun ce ni kawai 'yar ƙauye ce".

Ƴan gudun hijirar Somalia na zama a sansanoni daban daban, galibinsu a ciki da kewayen babban birnin Mogadishu. Hoto: Reuters

Ko waɗanda suka zauna a Mogadishu na tsawon shekaru ana musu kallon baƙi.

Masalaha na tafe

Mutane a nan har yanzu suna ɗauka ta a matsayin wanda ya rasa matsuguninsa, ɗan gudun hijira, duk da dai na zauna a nan tsawon shekaru 16," inji Mukhtar Abdalla Abdow mai shekaru 60 da haihuwa. Ya tsere daga garinsu na Janaale sama da shekaru 30 da suka gabata, da farko ya je birnin Galkayo da ke tsakiyar ƙasar, daga baya kuma ya zo Mogadishu. Na ɗauki kaina asalin mazaunin nan," ya bayyana.

Hukumar 'Yan Gudun Hijita ta ce "galibin daɗaɗɗun 'yan gudun hijira idan aka duba sosai sun yi kama da talakawan birane amma suna da buƙatu mabanbanta da na sababbin zuwa.

Amma wasu mazauna Mogadishu kamar Juweeriya Mohamed Ibrahim, tana da ɗabi'a ta maraba da 'yan gudun hijira.

"Ina musu kallon mutane kamar kowa da suka zo nan domin rayuwarsu ta fuskanci barazana sakamakon ambaliyar ruwa da fari da kuma tashin hankali," ta bayyana. "A wajena, idan sun zauna a Mogadishu na tsawon shekaru sama da biyar, na ɗauke su sun zama ƴan waje kamar ni."

"Wasu na yawan cewa su ba cikakkun 'yan ƙasa ba ne. Na yi imanin ba haka ba ne."

A matsayin wani ɓangare na masalaha ga matsalar, gwamnatin Somalia ta sanar da wani shirin sake tsugunar da an gudun hijira domin inganta rayuwarsu.

Firaministan ƙasar Hamza Abdi Barre ya kaddamar da Wani shirin warware matsalolin ƙasa mai suna National Solutions Pathways Action Plan ranar 4 ga watan Satumba a Mogadishu, abin da ya jawo kyakkyawan fata ga halin da ƴan gudun hijira ke ciki. Ana sa ran shirin na tsawon shekaru biyar zai gudana daga wannan shekarar zuwa 2029.

"Idan 'yan Somalia su miliyan ɗaya suka koma gudanar da rayuwarsu kamar kowa zai zama wani muhimmin mataki na samar da masalaha mai ɗorewa game da ƴan gudun hijira, don su zama wani bangare na al'umma don ciyar da ƙasa gaba," firaministan ya bayyana.

Marubuciyar, Hinda Abdi Mohamoud ita ce babbar editar Bilan, kafar yaɗa labarai ta mata zalla ta farko a Somalia da take da mazauni a Mogadishu.

TRT Afrika