Ana ci gaba da kallon kirifto a matsayin wani ƙalubale ga jama'a da kuma lokacinsu. / Hoto: TRT Afrika

Asalin Bitocin wadda aka ƙirƙiro a 2009 ba wai kawai batu ne na Satoshi Nakamoto ba, wanda ya ƙirƙiro shi, wanda mutum ne da ba ma a san ko wane ne ba, inda ya fito da wani tsari na kuɗin intanet ba tare da wata hukuma ɗaya tilo da ke sa ido a kai ba.

Bitcoin wanda shi ne kuɗin kirifto na farko a duniya sai da ya zama barazana ga duk wata harkar cinikayya wadda ta shahara.

Zuwa 2024, yanayin jin daɗi da annashuwa da aka shiga sakamakon sabon tsari na samun kuɗi ya jawo masu amfani da kirifto sun ƙaru, tun daga Amurka zuwa Turai da Asia da Afirka.

Aminu Auwalu Yakasai, wanda asalin ɗan jihar Kano ne a Nijeriya, na daga cikin waɗanda suka gaskata kirifto, duk da cewa yana sane da cewa akwai ƙalubale a tattare da harkar.

A kwanakin baya lokacin da idan aka kira kalmar "kirifto" mutane ke zare ido saboda rashin yarda, zai yi jayayya - sau da yawa ba tare da wata fa'ida ba - game da yadda ake buƙatar cire kuɗin daga banki ba tare da ta rasa darajarta ta ainihi ba.

Yakasai na kallon yadda ake saka sabbin kudin na kirifto a manhajoji da yadda suke ƙara daraja su kuma sauka wanda hakan ke nufin kirifton ta zo kenan.

Yakasai ba shi kaɗai ba ne a wannan tafiya. Abdullazeez Aljassawee daga Jos da ke Nijeriya, na daga cikin waɗanda suka samu riba daga mining na kirifto.

A cikin bayanansa, ya yi saurin ƙarawa da cewa duniyar kirifto na ɗauke da hatsari iri-iri, sakamakon ya sha tafka asara. Labari mai daɗin shi ne ribar da Aljassawee ya samu ta fi asarar da ya tafka.

Duniyar kirifto na cike da hatsari iri-iri, inda a wani lokacin masu amfani da kirifton ke tafka asara. / Hoto: AA

Fasahar Blockchain

Fasahar Blockchain wani tsari ne na littafin ajiye bayanan kasuwanci amma wanda yake a kan intanet da ke ajiye bayanai na cinikayya, wanda ke kama da littafin da ma'aikatan hada-hadar kuɗi ke amfani da shi domin ajiye bayanai na kuɗi.

Yin abubuwa a bayyane da kuma tsaro na daga cikin ginshiƙin wannan tsari. Sakamakon bayanan ba a wuri ɗaya suke ba, kuma duk wani ciniki da aka yi yana tare da na baya, sauya bayanan lamari ne mai matuƙar wuya.

Masu kirifto na amfani da wannan tsarin na fasahar blockchain domin samun damar yin abubuwa a bayyane. Idan aka yi cinikayyar Bitcoin alal misali, ana tura cinikin ne a kan network. Daga nan ne sai a saka cinikin kan wani sabon fasahar ta blockchain.

Yadda ake samun haɓakar ƙungiyoyin 'yan kirifto

Ana ci gaba da kallon kirifto a matsayin wani ƙalubale ga jama'a da kuma lokacinsu, sai dai hakan bai hana waɗanda suka saka kansu yin mining ɗin abin da suke son yi ba.

Yakasai na shafe akasarin lokacinsa na rana a kan manhajojin nan na mining, haka shi ma Aljassawee.

"Mining ɗin kirifto ba ɓata lokaci ba ne kuma ba zai taɓa zama ɓata lokaci ba sakamakon za ka rinƙa samun ilimin fasahar blockchain," kamar yadda Aljassawee ya shaida wa TRT Afrika.

"Haka kuma za ka koyi yadda za ka yi cinikayya da kirifto a manhajojin saye da sayar da kirifto kamar Binance, OKX, Bybit, KuCoin, Remitano da sauransu."

Yakasai ya yi amannar cewa waɗanda ke shakkun darajar kuɗin kirifto su je su yi nazarin mece ce fasahar blockchain kafin su yanke shawarar zuba jari a ciki.

"Ilimi sinadarin rayuwa. Ina da yaƙinin cewa waɗanda ke gardama da faɗan abubuwa iri daban-daban a cikin jahilci, ba su san komai game da shi ba, hakazalika idan ta fashe, sai su shiga ruɗani su nemi cewa suna son samun kuɗi a dare ɗaya, wanda hakan ba zai yiwu ba," kamar yadda ya yi bayani.

Sakamakon yadda masu son kirifto ke ƙaruwa a Afirka da ma sauran sassan duniya, masu shakka game da lamarin na ganin za a samu gazawa a nan gaba.

Sai dai ga sauran jama'a irin su Yakasai da Aljassawee, duniyar kirifto na ci gaba da zama wata hanya ta samun arziki.

TRT Afrika