A makonnin baya-bayan nan an ga yadda labarai ke ta yaɗuwa a kan masu zargin cewa an sace musu al’aurarsu sakamakon yin musabaha da wasu.
Wannan lamari ya rika jawo mutane na ɗaukar matakai a kan wadanda ake zargi da aikata hakan, inda a lokuta da dama akan lakaɗa musu dukan da kan sanya su fita hayyacinsu.
Duk da cewa lamarin ya yi sauƙi a baya-bayan nan, amma a lokacin da yake kan ganiyarsa ya faru a jihohi irin su Kano da Bauchi da Kaduna da wasu da dama har ma da babban birnin Nijeriya, Abuja.
Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta Abuja ta ce a cikin wani mako ɗaya a watan Oktoba sai da ta gurfanar da mutum 14 a kotu kan zarginsu da yaɗa labarin ƙarya na cewa an sace wa wasu mazakuta, abin da ya ɗaga hankulan mazauna birnin.
Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya NAN ya kuma rawaito cewa a cikin makon sai da mutane suka yi gaban kansu wajen yi wa fiye da mutum 12 da ake zargin su sace al’aurar wasu duka.
Wani labari mai alaƙa
Sai dai Kwamishinan ƴan sandan Abuja Haruna Garba ya shaida wa NAN cewa da aka kai waɗanda suka yi ihun sace musu al’aurar asibiti, sai aka tabbatar da cewa mazuktarsu na nan ba abin da ya same ta.
Mene ne ainihin abin da ke faruwa?
Kwararru a Nijeriya sun ce babu gaskiya a batun cewa akwai wani siddabaru da zai sa a sace wa mutum al’aurarsa, inda suka ce shafi mulera cuta ce da take da alaka da kidimewa, da ake kira anxiety disorder a turance.
A wata hira da TRT Afirka, kwararren likitan kwakwalwa a Asibitin Malam Aminu Kano, Farfesa Auwal Sani Salihu, ya ce “babu wani mutum da yake iya sace wa wani al’aura kamar yadda mutane suke ikirari, yana mai cewa ya kamata a rika kai duk wanda ya yi ikirarin an sace masa al’aura asibiti maimakon wurin ‘yan sanda.”
Baya ga Nijeriya da wasu kasashen Afirka, akwai irin wannan matsalar a nahiyar Asiya, amma a can ana kiranta da Koro Syndrome ne, inda su ma za a ji mutum ya buga ihu kawai yana cewa al’aurarsa ta ɓace ko ta koma ciki, amma idan aka duba sai a ga tana nan.
“In dai akwai wani da zai iya cire maka al’aura kuma babu ciwo babu jini sai dai kawai a ji wajen ya warke, to ai mu likitoci da sai mu daina tiyata ma. Da sai mu samo musu su dinga yi wa mutane tiyata ba tare da yanka su ba,” in ji Dokta Salihu.
“To amma gaskiya babu wanda zai iya irin wannan abu,” likitan ya ƙara da cewa.
Dokta Salihu ya ce wannan yanayi wani nau’in rashin lafiya ce da shi wanda yake ikirarin an sace masa al’aurar yake fama da ita mai suna anxiety disorder.
“Wato cuta ce da take da alaƙa da kiɗima da ruɗewa, don haka kamata ya yi a kai wanda ya shiga irin wannan hali asibiti a kwantar masa da hankali a kuma tabbatar masa cewa abarsa tana nan kuma in ya nutsu zai ji harbawarta.