Children under 15 years old are among victims arriving at hospitals with gunshot, blast and shrapnel wounds. /Photo: MSF Yara ‘yan kasa da shekaru 15 na daga cikin wadanda abin ya rutsa da su da aka kai su asibitoci sakamakon harbinsu da bindiga ko rauni saboda fashewa bam. Hoto: MSF

Daga Sylvia Chebet

A wani ɗakin ba da agajin gaggawa a Asibitin Koyarwa na Bashair a Kudancin Khartoum da ke Sudan, wata tawagar likitoci ce suka duƙufa cikin fargaba don ceto rayuwar Riyad ɗan wata 18.

Yaron yana cikin tsananin ciwo da tashin hankali a lokacin da mahaifiyarsa ta kai shi asibitin, in ji likitocin.

"Nan da nan, sai na ji dile na kawai na ceto rayuwarsa," kamar yadda wani likita na ƙungiyar agaji ta MSF, Dr Moeenya shaida wa TRT Afrika.

"Bai yi komai ba balle ya cancanci shan wannan wahalar; kawai an haife shi ne a yankin da ake yaƙi, kuma ya zama aikina na ba shi kulawar da ta dace don ya rayu.

A yayin da ake bikin Ranar Yara ta Duniya ranar 20 ga watan Nuwamba, ƙungiyoyin agaji sun koka kan yadda yara ke ci gaba da fuskantar wahalhalu a Sudan da kuma yankunan da ake rikici.

Riyad na daya daga cikin miliyoyin yaran da ke fuskantar wahalhalun da yakin Sudan ya jawo, wanda ya barke a watan Afrilun shekarar 2023, bayan da aka samu baraka kan shirin kasar na mika mulki ga dimokuradiyya.

Yaron ya tashi daga barci ba shiri a gigice bayan da wani harsashi ya same shi a kirjinsa, lamarin da ya yi sanadiyyar wargaza zaman lafiyarsa.

“Tawagar likitocin sun yi yaki na tsawon sa’o’i hudu domin ceton ransa. Ya kasance cikin rai-kwakwai mutu-kwakwai a tiyatar, sakamakon zubar jini mai yawa,” Dr. Moeen ya kara da cewa.

Harsashe a ƙirjin jaririn

Ko da yake tawagar ta yi nasarar dakatar da zubar jini, harsashin ya maƙale a cikin kirjin Riyad.

Asibitin Koyarwa na Bashair na ɗaya daga cikin cibiyoyin kiwon lafiya na ƙarshe da ke aiki a kudancin Khartoum, kuma ba shi da ingantattun kayan aikin tiyata.

MSF ta ce tsare-tsare na hana shigar da magunguna tun daga watan Oktoban 2023 sun gurgunta ayyukan kiwon lafiya a galibin asibitocin Sudan.

“Yaro dan watanni 18, harsashi ya huda ƙirjinsa, abin tunatarwa ne game da rayukan da ba su ji ba gani ba sakamakon yaƙi. A cikin yanayi na hargitsi, tare da ƙarancin kayan aiki, mun yi yaƙi don ceton rayuwarsa. Babu wani yaro da ya cancanci shan wahala irin wannan,” in ji likitan.

Khartoum, wanda ya taɓa zama babban birni mai hada-hada, ya zama filin daga tun kafin a haifi Riyad.

Yaron mai shekara daya da rabi yana daya daga cikin yara 314 da aka yi wa tiyatar harbin bindiga da raunuka a cikin 2024 kadai, in ji MSF.

Ana yawan jikkata yara

"Idan muna duba yaran da suka ji rauni a yakin abin na ba mu tausayi matuƙa, amma juriyarsu ta fuskar radadin da ba za a iya misaltawa ba yana ƙara azama wajen jajircewa, komai hatsari ko kalubale," in ji jagoran likitocin na MSF.

Tsakanin Janairu da Satumba 2024, MSF ta yi jinyar jimillar mutum 6,557 da suka samu raunuka a yaƙin, a cibiyoyinta a fadin jihohi 11 daga cikin 18 na Sudan.

A Asibitin Bashair, kashi 16 cikin 100 na marasa lafiya da suka ji raunuka a yaƙin sun kasance yara ‘yan kasa da shekara 15 ne.

A karshen watan Oktoba, an garzaya da mutane fiye da 30 da suka jikkata zuwa asibitin a cikin kwana guda, sakamakon fashewar wani abu a wata kasuwa mai nisan kilomita daya daga wajen.

Sha biyu daga cikin wadanda aka kawo dakin gaggawa yara ne ‘yan kasa da shekara 15. Da yawa sun samu raunuka da kuma ƙuna.

An kawo wata yarinya 'yar wata 20 da wani ƙarfe ya ji mata mummunan raunin a kanta.

"Abubuwan da ke faruwa irin wannan sun zama ruwan dare," in ji shi. “Mun gode Allah waccar yarinyar ta tsira. Wasu kuma ba su da sa’a sosai,” Dr. Moeen ya lura.

Zafafa yaƙi

Yawan samun lamarin da ke jawo mutuwa ko jikkatar mutane da dama - inda ake kai marasa lafiya da yawa asibiti cikin kankanin lokaci - ya zama ruwan dare yayin da fadan ya tsananta a cikin birni.

Ƙananan asibitocin da ke aiki suna cikin matsanancin matsin lamba kuma ma'aikatan kiwon lafiya suna fafutuka don sarrafa duk abubuwan da ake buƙatu.

Baya ga tiyata masu sarƙaƙiya, akwai sauran ayyukan jinya kamar irin magance munanan raunukan ƙuna da suka zama ba sa yiwuwa a yi a birnin wanda farar hula ke ƙara fuskantar hare-hare.

"Duk da ƙarancin kayan aiki da rashin tsaro, da ɓarna, muna ci gaba da tsayawa tsayin daka - muna ba da kulawar ceton rai ga wadanda hare-hare suka rutsa da su," in ji likitan MSF.

Asibitin Bashair ya kuma fara samun karuwar yara da mata masu juna biyu da ke fama da tamowa.

Akalla mata da yara 4,186 ne aka yi wa gwajin rashin abinci mai gina jiki tsakanin watan Oktoba da Nuwamban 2024, inda sama da 1,500 daga cikinsu ke fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.

“Wadannan alkaluma na tashe-tashen hankula da rashin abinci mai gina jiki sun nuna yadda mutane ke cikin matsanancin tsoro, ciki har da yara, da suke fama da su a Khartoum. Dole ne bangarorin da ke rikici su tabbatar an kare fararen hula. Ya kamata a ba da damar kayayyakin jinya su isa duk asibitocin da ke Sudan,” in ji Claire San Filippo, Jami’in Hukumar Agajin Gaggawa ta MSF.

Ranar Yara Ta Duniya

Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye a gida da waje ga bangarorin da ke rikici da su ajiye makamai.

Da yake ƙarin haske kan tasirin yaƙi a kan yara, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce: "A Ranar Yara Ta Duniya, muna bikin kananan yara a cikin danginmu. Amma a yau kuma lokaci ne da za mu gane babban kalubalen da yara ke fuskanta a cikin rarrabuwar kawuna mai cike da tashin hankali."

Yaƙin da ake yi a Sudan ya raba mutum fiye da miliyan 11 da muhallansu, lamarin da ya haifar da rikicin gudun hijira mafi girma a duniya.

TRT Afrika