Daga Hamza Kyeyune
A duniyar hada-hadar kudade, samun halayyar kaffa-kaffa wajen kashe kudi na iya fuskantar gurguwar fahimta a matsayin "ajiye kudade don wata rana", da kuma ma'anar rashin abun hannu.
Daukar irin wannan mataki na zuwa ne don tsoron me ka iya zuwa ya komo, wanda yanayi ne da ke sanya mutum ya ajiye wani abu saboda ɓacin rana.
Ranar 30 ga Oktoban kowacce shekara ce aka ware a matsayin Ranar Tanadi da Tattali ta Duniya, don zaburar da mutane su dinga ajiye wasu 'yan kudade don bacin rana kamar faduwar darajar kudi da rashin lafiya da hatsari ko kuma rasa wata kadara.
Wani abu da ake yawan mantawa da shi, shi ne tunanin 'yancin sarrafa kudade a zamanance - ko tunanin cewa mutum ba zai taba dauwama a talauci ba - a matsayin abubuwan da ke sanya wa a ajiye kudade.
Mafi yawan mutane sun fahimci muhimmancin tanadi, kuma sun amince da su dinga ajiye wani bangare na abun da suke samu don amfani a nan gaba.
Sai dai kuma, cimma wannan manufa ya zama wani kalubale saboda dalilai da dama. Kamar yadda batun yake, zuciya na so, amma tsoka ta hana.
Bambancin samun kudade
Alkaluman 'Global Findex Database' sun bayyana cewa kaso 55 na manyan mutane a kasashe masu tasowa na iya samun kudaden magance matsalolin gaggawa cikin sauki a tsawon wata guda, inda kaso 45 kuma aka bar su a baya.
Wannan na nufin a yayin da manufar ajiye kudade abu ne da aka fahimce shi a ko ina, kusan ko wanda ya fi kowa karancin samun kudi na son ajiye wani abu, ana bukatar zage damtse sosai don cimma wannan manufa.
A babban birnin Uganda mai hada-hada na Kampala, kai komon yau da kullum na cakuduwa da matsalolin kudade da ke tasowa.
Gama-garin mutane a titunan birnin na cewa ba su da isassun kudaden biyan bukatun yau da kullum, ballantana mutum ya ajiye dan wani abu.
Halin tattalin arziki da ake ciki yanzu, tare da hauhawar kayayyakin masarufi da ke lamushe kudaden mutane, sun sanya gwagwarmayar rayuwa cikin wani hali sama da batun adana kudade.
"Idan akwai kudin ajiyewa, ba za ka ajiye abun da ba ka da shi ba. Kafin ka iya ajiye kudi, dole ne ka bai wa wasu hidimominka muhimmanci, ko kuma ajiyar ba za ta yiyuwa ba. Ba za ka iya boye kudin da ka awahala ka samu ba alhalin kana jin yunwa," in ji wani matashi da ya zanta da TRT Afirka.
Yana daya daga cikin miliyoyin mutane da ke fuskantar wannan kalubale. Gwagwarmayar rayuwa a kowacce rana na zaburar da mutane ga ajiye kudade daga cikin zukatansu.
Kadan na da rana
Ko a Uganda ko a wata kasa daban ta Afirka da ma duniya baki daya, an tabbatar tare da yarda da cewar tsimin kudade na daga cikin manyan halayen ɗan'adam.
A littafinsa da ya fi samun karbuwa mai suna Atomic Habits, marubuci Ba'amurke James Clear ya yi bayani game da bambancin da ke tsakanin tsimi da kuma tsimi a matsayin wani tsari na sauyin hali.
"Za ku iya sanya halayya ta zama abar sha'awa idan za ku iya koyon hada halayyar waje guda da kwarewa mai kyau," in ji shi.
Samar da tsarin kashe kudade, yayin da mutum ke ajiye wani adadi na kudi, hanya ce mai taimaka wa sama da mutum ya ce wai yana da kalubalen da zai hana shi ajiye dan wani abu bayan biyan bukatunsa.
Manufar ita ce cewa da zarar ka dan ajiye wani dan adadi na kudade, za ka samu karfin gwiwar ci gaba da adanawa.
Hakan kuma na taimaka wa mutum wajen daidata kai ga gaskiyar cewa, ba kamar sauran abubuwa a duniyar yau ba, babu gaksuwa ta nan da nan game da ajje kudade.
To shin mutanen da ba sa samun kudade da yawa ko suke gwagwarmayar neman na kai wa baki za su yi burin tanadin kudi?
Alkaluma sun bayyana cewa lokaci shi ne babban abokin tafiyar dabarar tsimin kudade, ba tare da duba ga yawan kudaden da ake ajje wa don amfanin gobe ba.
Ajiye kudade 'yan kadan na tsawon lokaci, na sanya wa a tara dukiya mai yawa da za ta taimaki rayuwar mutum.
Ba abu ne da za a ce wai wadanda ba sa samun kudade da yawa ba za su iya ajiye kudi ba.
Ko mutanen da suke talakawa za su iya tanadin wani dan kudi wanda a hankali zai taru ya yi yawa a tsawon lokaci.
Dole ne a koyi wannan al'ada da adana kudi da tsimi: babu wata gajeriyar hanya, in ji masu bayar da shawara kan ta'ammali da kudade.
Hanyoyin ajje kudade
A yayin da iyalai da kungiyoyin zamantakewa suka kasance a kan gaba na wuraren da ake samun kudaden biyan bukatar gaggawa, yana da muhimmanci a fahimci irin bambancin da wadannan bangarori biyu suke da shi.
Kimanin rabin talakawa da suke koma wa ga 'yan uwa da abokai a yayin da suka shiga matsala, za su yi ikirarin cewa ba sa samun irin taimakon da suke so. Wannan adadi na sauyawa idan abun ya shafi masu kudi sosai.
Hanya daya da za a samu mafita ita ce mutanen da ba sa samun kudade da yawa shi ne su ma su fara ajiya a tsawon lokaci don magance matsalar bukatar kudin gaggawa da ka iya zuwa.
Shaidun gani da ido da alkaluman tattalin arziki sun bayyana cewa hakan za ta iya tabbatuwa.
Wasu kwararru na bayar da shawarar sauya ma'anar "Kudaden da za a iya kashewa" zuwa tsimi mai tsami. Suna muhawarar cewa ajiye wasu kudade ya kamata ya zama bangaren daukar nauyin rayuwa, wanda dole yana bukatar boye wani abu.
Mafara na iya zama darajta lokaci sama da kudi, abu daya tal da bai zama mara iyaka ba