Daga Mazhun Idris
Awon zafi a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya, wadda ke yankin da ke samun matsakaicin ruwan sama duk shekara, yakan yi yawan da har yakan hana mutane sakat.
Kwamishin lafiya na jihar, Abubakar Yusuf ya faɗa kwanan nan cewa, tsananin zafi a Kano cikin watan Maris, da Afrilu, da Mayu, da Yuni ya kai tsananin da ya "haifar da tarin matsalolin lafiya."
Cikin watan da ya gabata, awon zafi ya kai har digiri 45 a ma'aunin Celsius, inda gari ya zama "babu iska."
Jihar Kano tana tsakiyar yankin duniya mai yanayin Sahel savannah daga arewaci, da kuma Guinea savannah daga kudanci.
Bugun zafi
Takura da futa hayyaci da gajiya na daga cikin matsalolin da tsananin zafi ke haifarwa. bugun jini na daga cikin cututtukan da zafi ke haifarwa.
Bugun zafi shi ne mafi tsanani daga cututtukan da zafi kan haifar, wanda har yakan iya zama barazana ga rayuwa.
Wani rahoto na shekarar 2023 da Cibiyar Adrienne Arsht-Rockefeller Foundation Resilience Center (Arsht-Rock) ta fitar ya ce dubban mata ne a Nijeriya ke cikin barazanar kamuwa da cututtuka masu alaƙa da tsananin zafi.
Rahoton ya yi ƙiyasin cewa wasu mata 204,000 a Nijeriya da Amurka da Indiya za su iya shan fama da matsalar matsanancin bugun zafi.
Dubban bishiyoyi
Ganin yadda tsananin zafi ke yi wa rayuwar miliyoyin mutane barazana a Nijeriya, sai wata ƙungiya ta matasa a Kano da ake kira da "Make Kano Green" wato "A mayar da Kano koriya" ta fara wani shiri na inganta yanayin muhalli a Kano ta hanyar dasa bishiyoyi, da kuma wayar da kan mutane a kan buƙatar inganta muhalli.
Wasu masu fafutukar kare muhalli ne suka kafa ƙungiyar a shekarar 2019.
"Mun samu damar dasa dubban bishiyoyi. Kashi 47 cikin 100 na bishiyoyin sun riga sun girma," kamar yadda Ismail Auwal, ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar ya shaida wa TRT Afrika.
Auwal ya ce a yanzu a a Kano ana ganin yadda mutane ke fafutukar neman inuwar da za su fake don kauce wa tsananin zafin da ake yi a Kano.
Kwararowar hamada
Ƙungiyar Make Kano Green na tsoron cewa idan har ba a yi wani abu da gaggawa ba don hana lalacewar muhalli a Kano, to kuwa tsananin zafin da ake fuskanta a garin ba zai taɓa gushewa ba.
“Muna sane da babbar barazanar kwararowar hamada, shi ya sa muka taru domin wayar da kan al’ummar Kano muhimmancin kiyaye muhalli musamman kiyaye dazuka,” in ji Auwal.
Kungiyar matasan na da burin dasa itatuwa akalla miliyan daya, ba wai a Kano kadai ba, har ma da sauran sassan Nijeriya a cikin shekarar 2024.
Sai dai Auwal ya ce hakan zai yiwu ne ta hanyar taimakon masu sa kai masu ra'ayi daya da kuma sauran kungiyoyi abokan hulda.
Har gaba da Kano
"Fafutukarmu ta kiyaye muhalli a yanzu ta wuce Kano kawai. Muna ayyuka a jihohi 12 na Nijeriya, ciki har da Kebbi da Zamfara da Katsina da kuma Nasarawa," ya faɗa.
Saƙon Auwal a Ranar Kiyaye Muhalli da Duniya da aka yi ranar Laraba 5 ga watan Yuni shi ne kiyaye muhalli aiki ne da ya rataya a wuyan kowa, kuma rashin yin ɗaukar mataki a kan sauyin yanayi ba abin da zai jawo sai taɓarɓarewar al'amura.
Sauran sassan Afrika da suka haɗa da Gabashi da Kudancin Afirka suna fuskantar ambaliyar ruwa da mahaukaciyar guguwa da tsananin fari da ake alaƙantawa da tasirin sauyin yanayi. A sakamakon haka, ɗaruruwan mutane sun rasa rayuwarsu.
Ana bikin Ranar Muhalli ta Duniya ne da Hukumar Kula da Muhalli ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙirƙiro a duk ranar 5 ga watan Yuni, tun daga shekarar 1973.
'Farfaɗo da muhalli'
Miliyoyin mutane ne a faɗin duniya suke bikin ranar, wadda takenta ya kasance "farfaɗo da muhalli da yaƙi da kwararar hamada da yadda za a magance fari."
Saudiyya ce za ta karɓi baƙuncin Taron Muhalli na (COP 16) na shekarar 2024wanda Majalisar Dinkin Duniya ta samar don yaƙi da kwararar hamada, a watan Disamba.
"Ba za mu iya mayar da hannun agogo baya na, amma za mu iya inganta dazuzzuka, da farfaɗo da wuraren da ake samun ruwa da kuma farfaɗo da ƙasa. Mu ne al'ummar da za mu iya samun maslaha da muhalli," a cewar UNEP.