Daga Dayo Yusuf
A yau, wahalar gangamin da ake gudanarwa a mafi yawancin lokuta na kasancewa matsala boyayyiya da ke jiran addabar wannan tunani mai kyau.
Tun shekarar 1977 ake gudanar da bikin Ranar Mata ta Duniya a ranar 8 ga Maris din kowacce shekara a matsayin gangamin fitowa da bayyana hakkokin mata, bikin na zama wata ilhama a ko da yaushe.
Masu fafutuka sun yi amanna cewa batun Ranar Mata na bukatar fito da halin da ake ciki karara, ta yadda za a magance matsalar gaza kallon batutuwan da idon basira.
A wasu lokutan, cakuduwar bukatun da ke da muhimmanci wajen tunkarar su ne ke janyo tsaiko a ayyukan da ake yi.
"Mutane na fara yin abu mafi karanci don su zama masu aikata daidai a siyasance game da hakkokin mata. Kawai suna tunawa da wannan rana su kara gaba," in ji ma'aikaciyar sadarwa ta Kenya Terryanne Chebet, wadda ta kafa kungiyar 'Africa's Leading Ladies' yayin tattaunawa da TRT Afirka.
"Muna bukatar ci gaba da wannan, saboda duk da mun damu cigaba, akwai sauran aiki da yawa don daidaita tsakanin yara mata da yara maza."
Kungiyar Chebet na aiki a matsayi mai tallafawa mata inda take da mambobi sama da 400,000 a fadin nahiyar.
Muhimman manufofi
Taken Ranar Mata ta Duniya ta bana - "Zuba Jari a Kan Mata" - na da manufar janyo hankalin zuwa ga karfafawa mata a yanayin zamantakewa, siyasa da tattalin arziki a duniya baki daya.
A yayin da tunanin da ke tattare da taken ya wuce suka, ba kowa ne ya gamsu da cewa akwai wasu manufofi da aka tattara waje guda da suka wuce na tuna wa da ranar kawai ta hanyar bukukuwa ba, wanda ba wani abu da suke sauyawa.
Terryanne ta ce "Yana da kyau a yi bikin, amma ba a yin zuba jari yadda ya kamata kan mata yara da manya."
"Misali, idan ka yi zuzzurfan kallo ga matsayin al'umma, ilimi na bude kwakwale, amma waye kake tunanin zai zama na farko da za a fara ajiyewa ida iyalai suka gada biyan kudin makaranta?
"Za ka ji cewa ya kamata yarinya mace ta samu 'yancinta matukar dai yaron ya kammala samun nasa."
Dama iri daya
Tallafawa ta fuskar tattalin arziki ne babbar manufar taken 2024. UN Women sun bayyana cewa babbar hanya daya ta magance talauci a tsakanin al'umma shi ne a karfafawa mata ta fuskar tattalin arziki.
Idan aka samu mata da yawa da ke tallafawa iyalansu, to an fi samun habakar tattalin arziki da bunkasa a tsakanin jama'a.
Amma alkaluman MDD sun yi nuni da cewa mata a Afirka da ma dukkan sauran sassan duniya na ci gaba da fuskantar kalubale wajen samun damarmakin tattalin arziki, da suka hada da takaitacciyar damar samun ilimi, kudade da damarmakin ayyukan yi.
This is precisely what makes Terryanne sceptical. Wannan ne abin da ya sanya Terryanne zama mai dar-dar.
Ta ce "Idan ka yi bincike ta yanar gizo da kalmar 'kudi', kaso 90 na hotunan wadanda za su fito na maza ne da ke da kudade."
"Ya zama kamar har yanzu ana bukatar amincewa da mata ko sake karfafa musu gwiwa wajen zuba jari da daukar matakan tattalin arziki.
Ana daukar matakai da dama a yau don ganin an tafi tare da mata, amma hakan ba ba zai kwatantu da yadda aka bar mu a baya."
Terryanne ta ci gaba da bayanin cewa zuba jari a kan mata na nufin ba s damar neman ilimi da smaun horo daidai da maza, baya ga samar da yanayin da za su gudanar da ayyukan ko koyon sana'oi'.
"Ta hanyar cike gibin da ke tsakanin maza da mata a wuraren ayyuka da goyon bayan mata su yi shugabanci a sha'anin kasuwanci da masana'antu, za mu iya cimma babbar damar wanzar da cigaba mai dorewa," ta fada wa TRT Afirka.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ma ya nuna rashin jin dadinsa game da tafiyar wahainiya da ake samu wajen habaka da bunkasar mata a duniya.
"Cikakkiyar damar doka ta mata za ta samu nan da shakara 300. Wannan yanayi abin cin fuska ne. Rabin bani adam ba za su iya jira tsawon karni uku don samun 'yancinsu ba.
Muna bukatar daidato a yanzu," in ji shugaban na MDD a wani sako da ya fitar na Ranar Mata ta Duniya ta 2024.
Matsayin shugabanci
Masu fafutuka sun yi amanna da cewa gwagwarmayar neman daidaito tsakanin mata da maza wata gasa ce ta tsere.
Ta zama ba kowane yake gudu a sahu daya da sauran abokan tseren ba, wanda hakan ke sanya bangare daya ke jan daya bangaren zuwa baya.
Terryanne ta tabo batun alamun da ta fahimta a duniya - inda mata da yawa suke gwagwarmayar samun daidaito inda suke kuma nuna majinta a iyawarsu duk da irin kalubalen da suke fuskanta.
"Kenya abar bayar da misali ce. Muna ganin mata da yawa suna shiga siyasa, duk da cewa da yawan su suna faduwa a kan hanya tun kafin a gudanar da zabe," in ji ta.
"Suna shan matukar wahala kafin su samu damar samun tikitin takara a zabe, ko da kuwa kujera ce mafi kankanta ta siyasa. Abu mai kyau shi ne cewa mutane a yau sun bude idanunsu suna son karbar kujerun mulki."
Terryanne ta ce " Wani batun mara dadi shi ne game da me ma ake yi ne don ganin an karfafawa mata. "Bai kamata a yi amfani da wannan wajen yakar neman daidaito ga mata ba."
Alkaluma masu tayar da hankali
Wani rahoto da 'UN Women' suka fitar ya bayyana cewa a cikin duk mata goma akwai guda daya daga cikin matsanancin talauci.
Idan wannan mummunan yanayi ya ci gaba, nan da 2030, kusan kaso 8 na matan duniya - mata miliyan 342.4 da yara mata - za su dinga rayuwa a kasa da dala $2.15 a kowacce rana.
Masu gangami na yin kira ga gwamnatoci, kungiyoyi da daidaikun mutane kan su karfafa wayar da kai game da wadannan alkalumma a tsawon shekara, maimakon gudanar da taro a rana daya kawai.
Kamar yadda Terryanne ta bayyana "hanya mafi sauki wajen bayyana ko ra'ayi da nuna damuwa na gaske ne ko kawai yaudara ce shi ne a kalli abun a ranar tuna wa da shi kawai."
Ta shaida wa TRT Afirka cewa "Wadannan batutuwa za su zama ababan bayyana wa da kara haske idan akwai tarukan kasa da kasa na tunawa da su. Amma kamata ya yi su zama wadanda ake tattaunawa a kan su a kowacce rana a shekara."