yawancin mutane ana gano suna da cutar ne bayan riga ta watsu / Hoto: AA

Daga Mazhun Idris

An ware kowace ranar 8 ga watan Mayu a matsayin ranar wayar da kai kan kansar kwayayen haihuwar mata a duniya.

Kansar kwayayen haihuwar mata da ake kira "Ovarian Cancer" ta bambanta da kansar bakin mahaifa wato "Cervical Cancer".

Ga dai wasu abubuwa da suka kamata ku sani kan wannan cuta.

Mece ce kansar bakin mahaifa?

‘Kansar kwayayen haihuwar mata’ ba cuta daya ce tilo da za a ce an gano a jikin mutum ba. Wani gamammen suna ne na tarin nau’ukan kansa da ke shafar bakin mahaifa da bututun mahaifa da kuma bakin gefen mahaifa.

An kiyasta cewa akwai sama da nau’i 30 na kansar kwayayen haihuwar mata, kuma akwai bambanci mai fadi tsakanin faruwa da bayyanar su.

Kansar kwayayen haihuwar mata ita ce kansar da ta fi kashe mata, wadda kuma babu wani gwaji mai tabbaci da ake yi don gano ta. Kuma kowace mace tana cikin hadarin kamuwa da cutar.

Ta dalilin jinkirin iya ganin cutar, sakamakon rashin dubawa, kuma saboda ana yawan kuskure alamomin cutar da sauran cutuka marasa hadari sosai, yawancin mutane ana gano suna da cutar ne bayan ta riga ta watsu.

Wannan yana janyo karin wahalar magance cutar. Duk da cewa duka mata suna cikin hadarin kamuwa da cutar, ba a faye mayar da hankali kan cutar ba, kuma ba a saka kudi sosai wajen yakar ta.

Ranar yaki da Kansar kwayayen haihuwar mata ta duniya

A cewar shafin kungiyar Gamayyar kwayayen haihuwar mata ta Duniya, wato World Ovarian Cancer Coalition, wasu jagororin kungiyoyin fadakarwa kan kansar bakin mahaifa daga fadin duniya, su ne suka kafa ranar a shekarar 2013.

Sun ware ranar 8 ga watan Mayu. A wannan rana ne a duniya ake daga murya don nuna goyon baya kan yaki da kansar kwayayen haihuwar mata.

Duk da cewa ana ayyuka a wurare da lokuta da yawa kan wannan rana, Ranar Kansar kwayayen haihuwar mata ta Duniya ita ce babbar ranar da ake kamfe kan wayar da kai game da cutar. A yanzu, wannan rana tana samun goyon bayan kungiyoyi 200 daga fadin duniya.

Abubuwa biyar game da kansar kwayayen haihuwar mata

Ga abubuwa biyar da kowa ya kamata ya sani game da cutar daji ta kwayayen haihuwar mata:

Na daya: Gwajin tsome (gwajin lakuce bakin mahaifa) ba ya gano kansar kwayayen haihuwar mata.

Na biyu: An fi gano kansar kwayayen haihuwar mata sanda take matakin karshe na cutar.

Na uku: Gano kansar kwayayen haihuwar mata kafin ta watsu yana saukaka magance ta.

Na hudu: wayar da kai kan alamominta zai iya sa wa a gano ta da hanzari.

Na biyar: alamomin cutar kansar kwayayen haihuwar mata sun hada da:

  • Kumburin mara: girman mara zai karu yana hauhawa kuma ba ya
  • tafiya
  • Matsaloli cin abinci: wahalar cin abinci ko saurin jin koshi
  • Jin ciwon mara: mara ko kasan cibi yana ciwo
  • Alamun fitsari: jin matsin fitsari ko yawan yi.

TRT Afrika