A lokacin da aka gano cewa kwararriyar 'yar kwallon Tennis Billie Jean King na dauke da ciwon sukari na type two shekaru 16 da suka gabata, ta yi gwagwarmaya kamar yadda take yi a filin wasa.
Da take sauya salon abincin da take ci da motsa jikinta, tsohuwar zakarar Duniya kuma wadda ta kuma lashe gasar Grand Slam 38, King ta fara wata sabuwar tafiya don daidaita rayuwarta.
Billie Jean na da wasu kalmomi da kalamai na karfafa gwiwa ga masu fama da cutar sukari su miliyan 550 a duniya. Tana cewa "Kawai ku san cewa za ku iya rayuwa mai kyau, yalwa, akasin haka da kuzari."
Tauraron fina-finan Hausa a Nijeriya Muhammadu Sani Idris Kauru bai iya yadda sosai ba. Jarumin da aka fi sani da Moda a Nijeriya, na amfani da kafar katako bayan rasa kafarsa sakamakon cutar sukari. Amma kuma bai kassara gaba daya ba.
Ya shawarci mutane da cewa su dinga cin abinci mai gina jiki, suna ziyartar likitoci a kai a kai, da kuma aiki da magungunan da aka ba su.
Ba zato ba tsammani
A lokacin da wannan abu na rashin jin dadi ya afku, Moda na tsaka da more rayuwarsa yana jin dadin fito wa a fina-finai.
Jarumin ya shaida wa TRT Afirka cewa "Ina kan hanya ta zuwa Legas don wani shirin amincewa ne na gano wani dan karamin maruru a daya daga cikin yatsun kafata. Sai na sayi reza, na yanke shi tare a matse shi. Kamar dai yadda muke yi wa kowanne irin ƙurji."
Amma kuma sai ciwon ya ci gaba da yaduwa a kwanakin da suka biyo baya.
Amma asalin ibtila'in na nan tafe, kuma ya same shi kamar wata gobarar daji. Ashe ya kusa gano cewa kafarsa da ta samu cuta ta munana sosai.
"A duk lokacin da na ajje kafata a kasa, sai wani ruwa ya dinga zuba," in ji shi. "Akwai mafita guda daya kawai. Shi ne na a yanke kafar gaba daya."
Cuta gama-gari a duniya
Moda ba shi kadai ne ke fama da wannan cuta da me take janyo wa ba, musamman ma idan aka dauki tsawon lokaci ba a gano cutar ba.
Tun 1980 adadin masu dauke da ciwon sukari ya ninka, ya tashi daga kaso 4.7 zuwa 8.5 a tsakanin manyan mutane, kamar yadda alkaluman Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.
Dr Salihu Ibrahim Kwaifa, kwararren likita a Nijeriya ya fada wa TRT Afirka cewa "An yi hasashen nan da 2030, kusan mutane miliyan 600 ne a duniya ne za a samu dauke da ciwon sukai, wanda zai karu zuwa miliyan 800 nan da 2045."
A Afirka, akwai kusan mutane miliyn 24 da ke dauke da ciwon sukari. A shekaru 22 masu zuwa, adadin zai karu zuwa miliyan 55.
Yawaitar cutar cikin sauri na afkuwa a kasashe matalauta da masu matsakaicin arziki, ba kamar a manyan kasashe ba, kamar yadda Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya ta bayyana.
Ciwon sukari na janyo makanta, ciwon koda, bugun zuciya, shanyewar barin jiki da mutuwar labba.
A cikin shekaru 19 tun 2000, an samu karin kaso uku na mutuwar masu dauke da ciwon sukari. A 2019, ciwon sukari ya janyo mutuwar mutum miliyan 1.5 inda kaso 48 na mutuwar ya shafi 'yan kasa da shekaru 70.
Fahimtar cutar
"Ciwon sukari babbar rashin lafiya ce da ke shafar yadda jiki yake sarrafa sukari da kitse da abinci," in ji Dr. Kwalfa.
"Rashin lafiyar na afkuwa a yayin da insulin, sinadarin da ke taimakawa wajen tura sukari zuwa cikin fatar dan adam, ya kasance babu shi ko ba ya aiki baki daya.
Wannan sai ya janyo sukarin da ke jikin dan adam ba ya iya samar da glucose din da jiki ke bukata. A takaice dai, muna ne kallon yunwa a lokacin da ake da wadata."
Masanan kimiyyar lafiya sun kasa ciwon sukari zuwa gid auku; na fako shi ne wanda yara kanana ba su da isasshen Insulin (type 1), sai wanda Insulin din ba ya aiki yadda ya kamata (type 2) da kuma ciwon sukari na giman jarirai a mahaifa da mata masu juna biyu suke fuskanta.
Bangarorin da ke da hatari game da ciwon sukari sun hada da rashin motsa jiki, cin abinci mara inganci, yin kiba ba tare da motsa jiki ba, da kuma rashin daidaito tsakanin samu da fitar da kuzari.
Duk wani abinci da jikinmu ba ya bukata, yana ajje shi a matsayin kitse. Wannan, kamr yadda kwararru ke fada na janyo kiba, daga nan kuma sai ciwon sukari.
Wadanda suke gadar ciwon sukari daga iyayensu ne suka fi hatsarin kamuwa da cutar, kamar dai masu yawan zama waje daya a rayuwarsu.
Yaki da cutar
Duk da wannan barazana, mutum na iya karya ciwon sukari kafin ya girmama ko kuma ya samu nasarar yakarsa bayan ya kama shi sosai.
Matakin farko na samun kariya daga cutar shi ne ilmantar da mutane kan wajabcin motsa jiki, ko suna da kiba ko ba su da ita.
Dr Kwaifa. Dr Khalifa ya bayar da shawarar cewa "Mataki na biyu da ake dauka shi ne na a guji rayuwa a zaune. Ko ma me kake yi, ka samu lokacin tattakawa.
"Ku ci abinci mai gina jiki da amfani sosai - abincin da ke hade da kayan marmari, ganyayyaki da sinadaran gina jiki."
Ziyartar likita sau daya ko sau biyu a shekara don bincikar lafiyarka, abu ne mai kyau sosai.
"Yawanci an fi gano dukkan nau'ikan ciwon sukari da wuri tun kafin ya ta'azara," in ji Dr Kwalfa.
"Idan mutum na aiki da shawarwarin likita a wannan lokaci, to za a iya magance cutar. Babu wani abun damuwa."
Kamar yadda jarumin Hollywood da ya lashe gasar Oscar, Tom Hanks ya fada bayan kamuwa da ciwon sukari na 'type two', "Ban kyale cutar ta illata rayuwata ba."
Wasu jaruman ma irin su Halle Berry da Salma Hayek duk sun yadda da hakan. Dukkan su sun yaki ciwon sukari ta hanyar hana kai abubuwa da yawa, motsa jiki da shan magunguna.