Awa Keita Ndiaye ta taso tana kallon danginta suna fama da matsalar ƙarancin ruwa, ko don kiwon shanu ko ban ruwa.

Daga Firmain Eric Mbadinga

Awa Keita Ndiaye ta taso tana kallon danginta suna fama da matsalar ƙarancin ruwa, ko don kiwon shanu ko ban ruwa.

A lokacin da take da shekara 26, tana amfani da digirinta a fannin kasuwancin noma don taimaka wa al'ummarta a ƙauyen Mbollo Aly Sidi na Senegal don shawo kan wannan matsala ta hanyar samar da hanyoyin ruwa ba tare da katsewa ba a duk lokutan yanayi.

Tuni dai shirin Awa ya kawo sauyi. Tun daga shekara ta 2022, wannan ƙauyen da ke tsakanin yankunan Podor da Matam na arewacin Senegal ya ci gaba da samun ci gaba a kai a kai ga burin haɓaka yawan amfanin gona da taimakon makiyaya da fiye da rabi.

Aikin na Mbollo Aly Sidi ya fara ne da Ada inda aka mayar da hankali wajen ƙara samar da ruwan sha domin noman gonakin kakanni wadanda suka hada da 'ya'yan itace da masara da dawa da gero da shinkafa, da rake.

Masu amfani da hasken rana na taimakawa wajen samar da makamashi da ruwa a yankin

"Azabar da dangina ke ciki ta shafe ni sosai. Tun ina ƙarama na yanke shawarar na yi wani abu a kai," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.

Rarraba hannun jari

A bisa tsarin bayar da tallafin kudi da ya shafi jama'ar gari da abokan zaman kansu, aikin da wannan matashiyar ta kaddamar ya samar da tafkunan ruwa guda bakwai a yankin don samar da dukkan bukatun al'umma.

Masu amfani da hasken rana na taimakawa wajen samar da makamashi da ruwa a yankin da ake ruwan sama na watanni uku kacal a shekara.

Tsananin zafi da ake yi a kai a kai inda yakan kai digiri 40 a ma'aunin salshiyas, ya taimaka wajen tsanantar yanayin har sai da wannan aiki nata ya kafu ya fara samo wa al'ummar sauƙi.

“Al’umma sun ba da gudunmawar kusan kashi 30% na CFA miliyan daya da rabi da ake bukata don aikin.

CorpsAfrica, wani kamfani abokin hulɗarmu mai zaman kansa, ya ba da ragowar adadin, tare da gamsuwa da mahimmanci da kuma dacewa da wannan aikin.

An dauki watanni bakwai ana aiwatarwa,” in ji Awa.

Tun daga kan zane har zuwa aiwatar da shi, wani bangare na tafiyar aikin da ya yi fice a wajen Awa shi ne shigar mata cikin lamarin.

"Na ga zaƙuwa da farin ciki da gamsuwa da alfahari a tsakanin mata da maza na al'ummata yayin da aikin ke gudana," in ji ta.

Matan kauyen Mbollo Aly Sidi sun yanke shawarar gina tafkunan a kewayen kasuwanni da wuraren aikin lambu. /Hoto: Awa Keita Ndiaye:

Mata a kan gaba

Dangane da cikakken tsarin aikin, mata 250 da suka kafa kungiyar masu fafutukar tattalin arzikin ƙauyen sun bayyana yankin da za a gina tafkunan bakwai.

Wani abu da ba a yi mamakinsa ba shi ne yadda suka zaɓi kasuwa da wuraren aikin lambu. “Tsarin farko ya hada da sanya na’urar ban ruwa ta drip.

Ko yaya, bayan nazarin haɗarukan da ke tattare da hakan, mun zaɓi manufar ɗorewa. Don haka, mun ƙara gaba daga aikin ban ruwa zuwa samar da madatsun ruwa.

Da abin da ya rage, mun sayi gwangwanayen ruwa da na’urorin amfani da hasken rana,” Awa ta shaida wa TRT Afrika.

Babban yanki na waɗannan maɓuɓɓugan ruwa yana ba da damar tattara ruwa mafi kyau.

Kamar kowace maɓuɓɓugar ruwa da ke aiki a rufaffiyar da'ira, ruwan da ke cikin kwandon yana ci gaba da zagayawa kuma ana sake sabunta shi.

Awa Keita Ndiaye, mai shekaru 26, ta yi digirin farko a fannin kasuwanci na aikin gona. / Hoto: Awa Keita Ndiaye:

Tun lokacin da aka kafa ta, mazauna Mbollo Ali Sidy 1,680 sun sami damar haɓaka amfanin gonakinsu. Hanyoyin hasken rana suna ba da ƙarin fa'ida.

“A tsawon lokaci, duk waɗannan sabbin abubuwan da aka samar za su ba mazauna ƙauyen damar rage ƙwazo da adana lokaci da kuzari, da haɓaka amfanin gona. A wani babban buri, aikin yana da nufin taimaka wa inganta samar da abinci," in ji Awa.

Makasudin samarwa

Aikin na da nufin bai wa manoma damar ƙara yawan noma da kashi 80 cikin 100 a cikin wata shekara da kuma samar da dimbin masu cin gajiyar wadannan ayyuka kai tsaye.

Shugaban ƙauyen Kaw Moussa Mb Ali ya ce "Wannan aikin ya kawo mana sauki sosai, musamman fafutukar da muke yi ta samun ruwan sha domin noma da sauran buƙatu a duk shekara.

Awa mai fafutuka ta yi nisa. Sabuwar manufarta ita ce wayar da kan matasa da iyayensu game da ilimi a Mbollo Aly Sidi ta hanyar kamfen na daƙile yawan barin makarantu.

TRT Afrika