Daga Abdulwasi'u Hassan
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya kafa wani kwamiti da zai yi duba game da yiwuwar kafa rundunar ƴan sanda mallakar jihohi a kasar ta Yammacin Afirka a wani yunkuri na magance matsalolin tsaro masu tasowa.
"Matsayata a bayyane take. Dole mu yi da karfinmu domin mu binciki batutuwa dake akwai ciki har da yiwuwar kafa rundunar ƴan-sanda mallakar jihohi," kamar yadda shugaban ya bayyana wa ƴan Nijeriya, yana mai bayyana dalilin matakin.
Sanarwar ta zo ne kwanaki bayan gwamnoni daga jam'iyyar adawa ta PDO suka yi kira ga gwamnatin tarayya ta bai wa jihohi ƴanci wajen dabbaka domin dakile matsalolin tsaro na yanki a kasar.
Wannan ba shi ne karon farko da ake tafka muhawara kan samar da ƴan-sanda mallakar jiha ba a Nijeriya. Amma ana ganin goyon bayan da Shugaba Tinubu ya bai wa tsarin a matsayin wani mataki na ci-gaba ganin yadda ayyukan rundunar ƴan-sanda na tarayya yake gudana.
Wannan ya zo ne yayin da sassan Nijeriya ke fama da satan mutane domin neman kudin fansa da barayi ke yi da fashi da rikici da kuma ayyukan ta'addanci tsageru ke yi kuma an tura jami'an tsaro yankunan da lamarin ya faru.
Yayin da suke kokarin dakile matsalolin, wadanda suka ta'azzara cikin shekarunnan, hukumomi na kokarin bin matakai daban-daban.
Rundunar ƴan-sandan Nijeriya tana karkashin jagorancin gwamnatin tarayya ne kai-tsaye inda jami'ai da dama ke aiki a jihohin da ba asalinsu ba ne. Wasu masana sun yi imanin cewa za a iya inganta tsaro ne idan aka tura wadannan jami'an a jihohin da suka fito.
A karkashin tsarin da ake bi yanzu, kwamishinan ƴan-sandan ko wace jiha na karkashin jagorancin Sufeto-Janar na ƴan-sanda ne, wanda shi kuma yana bin umarnin shugaban kasar ne.
Duk da cewa gwamnon ko wane daga cikin jihohi 36 na Nijeriya, su ne shugabannin jami'an tsaro a jihohinsu, ba su da iko kan 'yan sanda ko kuma sojoji a jihohin nasu.
Wannan bambancin da kuma kasancewar ƴan-sanda ba dole ne su aiki a inda suka fito ba na daga cikin dalilan da ya sa ake neman a samar da ƴan-sanda mallakar jihohi.
Dakile laifuka
Adetunji Adeleye, Shugaban rundunar tsaro ta Amotekun a kudu masa yammacin Nieriya, daya ne daga cikin masu wannan ra'ayin.
Amotekun, wanda ke nufin damisa a harshen Yarbanci, shi ne sunan da aka rada wa rundunar tsaro ta yammacin Nijeriya da gwamatocin jihohi na yankin suka kafa.
“Mun dade muna goyon bayan rundunar tsaro ta karkara domin yanzu da alamar cewa ita ce kawai hanya daya tilo ta magance wannan msatakar tsaro da ta ki ta ci ta ki cinyewa a sassan kasar," kamar yarda Adeleye shaida wa TRT Afrika.
Ya kafa hujja da abin da ya kira nasarar tsarin Amotekun a jihar Ondo.
"Idan ka yi la'akari da jihar Ondo, mun samu mun yi dakile aikata laifuka, lamarin da ya bayyana gagarumar ragi da aka samu a yawan laifukan da ake aikatawa. Mutanenmu ne suka samu suka cimma wannan," in ji Adeleye.
"Da zaran mun ga na waje haka ko kuma wani da yake aikata wani abu na zargi, za mu dauki mataki nan take. Idan ka gudu, mun fi ka sanin wuraren."
Ra'ayoyi masu karo da juna
Akwai fargabar cewa ƴan-sanda mallakar jihohi za su iya sha gaban matakan tsaron gwannatin tarayya, lamarin da zai iya kara rabe-raben kawuna a kasar. Amma Adeleye ya ce babu dalilin irin wannan fargabar.
‘’Idan dai mun mutunta dokar aiki, ban ga dalilin da zai sa rundunar ƴan-sanda mallakar jiha ba za ta iya nasara ba."
Gwamnonin wasu jihohin kudu maso gabashin da arewa maso yammacin kasar ma sun kafa rundunonin tsaro na kansu domin tunkarar matsalolinsu.
A halin yanzu dai rundunonin tsaron da jihohi suka kafa suna da karancin ikon daukar makami idan aka kwatanta da ƴan-sanda kuma mabobinsu yawanci ƴan sa kai ne.
Idan ana son a sauya wani abu a tsarin ƴan sandan Nijeriya sai an sauya kudin tsarin mulkin Nijeroya.
Kazalika, kamar kasashe da yawa, sauya kundin tsarin mulki na da wuya a Nijeriya. Dole kashi biyu cikin uku na majalisun dokokin jihohi 36 sun amince da sauya kundin tsarin mulkin tare da zaman jin ra'ayin jama'a.
Wadanda suke adawa da rundunar ƴan-sanda mallakar jihohi suna ganin zai iya jnayo koma-baya.
‘’Rundunar ƴan sanda mallakar jihohi ba abin da kasar ke bukata ba ne a halin yanzu. Ba zai inganta yanayin tsaro ba ," a cewar Patrick Agbambu, shugaban kamfanin tsaro na Africa Security Watch Initiative, a hirarsa da TRT Afrika. "Kuma kundin tsarin mulki bai yarda da shi a halin yanzu."
Patrick ya yi imanin cewa ya kamata gwamnoni da kuma shugabannin kananan hukumomi su mayar da hankali kan dakile tushen rashin tsaro a wurarensu ta hanyar ayyuka masu kyau tare da tinkarar matsalolin matsalolin tattalin arziki tare da gwamnatin tarayya.
"Suna da ikon. Kundin tsarin mulkin ya ba su wannan ikon, kuma ya kamata su tallafa wajen tattara bayanai na sirri da kuma hana aukuwar laifi maimakon mayar da martani bayan an aikata laifi," in ji shi.
A cewar Patrick, amfanin da aka yi a da da ƴan-sandan jiha a baya bai kai ga ci ba. Ana fargabar cewa wasu gwamnonin jihohi za su iya amfani da ƴan sandan dake karkashin ikonsu domin cimma wata bukata ta siyasa.
Wadanda suke adawa da tsarin rundunar ƴan-sanda mallakar jiha, kamar Patrick, sun ce ya kamata a karfafa ƴan sandan gwamnatin tarayya da kayayyakin aiki da kuma karin jami'ai tare da horarwa.
"Ina ganin bisa la'akari da yanayinmu da yake daban, rundunar ƴan sanda mallakar jiha ba zai yi taimaka ba," a cewarsa.
Ko ma mene ne dalilin kyawu da rashin kyawun samar da rundunar ƴan sanda mallakar jihohi, ƴan Nijeriya da suke fuskantar rashin tsaro za su yi fatan cewa lamarin zai sauya nan ba da jimawa ba.