A wasiyyar da farfesar da ta lashe kambin 'Nobel Peace Laureate' ta yi, ta bayar da umarnin idan ta mutu a kona gawarta a cikin akwakun lantarki. Hoto: Reuters

Daga Dayo Yusuf

A 2011, 'yan kasar Kenya sun shiga jimamin mutuwar daya daga cikin mashahuran mutane a kasar, Farfesa Wangari Mathai.

Amma ba ma su san cewa daga baya labari mafi girgiza zukata zai biyo baya ba.

A wasiyyar da farfesar da ta lashe kambin 'Nobel Peace Laureate' ta yi, ta bayar da umarnin idan ta mutu a kona gawarta a cikin akwakun lantarki.

Wannan mataki da ta dauka ya janyo ce-ce-ku-ce a kasar, wanda hakan ke bayyana yadda al'adu da addinai suka yi kane-kane game da mutuwa a Kenya da ma sauran yankuna da dama na Afirka.

A cikin al'ummar da ake kallon binne mutane a matsayin matukar girmamawa ga mamacin, zabin Maathai ya zama wani bambarakwai ga jama'ar Kenya.

Bishop Mark kariuki na Cocin Deliverance ta Kenya ya taba fada a wata jaridar kasa cewa duk da kona gawa ba abu ne da aka haramta a bible ba, masu akida a addinin Kiristanci na kyamar yin hakan.

Sai dai kuma, Bishop Mark ya ce yadda gangar jiki ke karewa ba shi ne batun ba. "Abin da aka damu da shi shi ne alakarka da Ubangiji," in ji shi.

Mutuwa cikin mutunci

A Kenya da ma wasu sassan Afirka, bikin binne gawa ba wai al'ada ce kawai ba, hakan na zama wani taro na girmamawa kaka da kakanni da dorewar al'ada.

A birane, kamar Nairobi, makabartu sun cika inda ake fuskantar matsala wajen binne mutane  Hoto: Getty Images

Makabartu a mafi yawancin lokuta na da matsayi na musamman, wanda hakan ke bayyana alakar mamata da rayayyu.

Sabanin haka, ana kuma kallon kona gawa a matsayin bakuwar al'ada kuma mummuna, wanda tarihi ya bayyana 'yan Afirka ba su karbe ta ba.

Mutane da dama musamman tsofaffi na kallon kona gawa a matsayin wata al'ada da Yammacin duniya ke son kawowa.

Har yanzu 'yan Afirka da dama na daukar batun rayuwa da mutuwa da muhimmanci sosai, a wasu lokutan ma batu mai tsarki.

Misali, mafi yawan Kiristoci a Afirka na ci gaba da binne mamatansu, maimakon aiki da mummunar dabi'ar kona gawa.

A wajen Musulmai, kona gawa haramun ne babu wata tantama, Ustaz Shaaban Omar, Limami a Nairobi, ya ce Musulunci na kare martabatar mutum, har bayan ya mutu.

"A yayin da wani ya mutu, babu wani da zai iya yi wa kansa. Addininmu ya koya mana cewa wajibi ne a kan mu a matsayin al'ummar da ke kewaye da mamaci mu tabbatar ba a kunyata, cin fuska ko kaskantar da gawar mamacin ba," in ji Ustaz Shaaban a tattaunawarsa da TRT Afrika.

Batu mai zafi

"Dole ne mu yi masa jana'iza mai kyau da girmamawa tare da yin ta cikin sauri da kuma sauki," in ji shi.

"Ba a yarda da ƙona gawa ba ko ma ta wace hanya ce. Saboda mun yi imanin cewa idan mutum ya mutu, yana iya jin me ke wakana a kewayensa. Ku yi tunanin a ce a kona gawa, ai kamar kona ta da ranta ne."

Amma kuma, dalilin Farfesa Maathai ya ba ta wani haske. A matsayin wadda ta shafe rayuwarta tana yaki da kare muhalli, ta fahimci Ƙona gawa a matsayin zabi ga muhalli, wanda ya dace da fafutukar da ta dinga yi ta samar da muhalli mai dorewa.

Kona gawa ba abu ba ne da aka cika gani kasafai a addinai daban-daban ba. Hoto: Reuters

"Me ya sa zan shiga cikin kasar da na karar da rayuwata ina kare ta?" kamar yadda aka ruwaitota tana faɗi

Matakin da ta dauka ya sanya 'yan kasar Kenya da dama kalubalantar abin da yake a zahiri na birnanci da sauyawar salon rayuwa da ke kokawa da tsarin jana'iza na gargajiya.

A birane, kamar Nairobi, makabartu sun cika wanda ake fuskantar matsala wajen binne mutane, makabartun sun yi tsada sosai kuma ba su da yawa.

Riko da abin da aka yi imani da shi

Tsadar yin jana'iza - kudin akwatin gawa, daukar ta, da gudanar da bikin - na janyo kashe kudi sosai ga dangin mamaci, wanda ke sanya wasu tunanin mafita ta daban.

"A Musulunci ba ruwan mu, ko mutum ya bar wasiyyar cewa a kona shi, to ba za a yi hakan ba." in ji Ustaz Shaaban.

Ya kara da cewa "Jama'a ba za su zartar da wasu umarni ba saboda ba su yi daidai da koyarwar addininmu da Annabi Muhammad (SAW) ba."

A Kenya, akwai 'yan wurare kaɗan da ake kona gawa, ina ake da sananne guda daya a makabartar Lang’ata da ke Nairobi.

Ba kowa ke yin hakan ba, mafi yawanci baki ne 'yan kasashen waje, Hindu ko daidaikun mutane da suke kwaikwayon matakin Maathai.

A fadin Afirka, Musulmai, Kirstoci da mabiya addinan gargajiya ba kasafai suke yin hakan ba, inda suke amfani da hanyar da aka sani ta binne mamata a kasa.

TRT Afrika